< Zabura 124 >

1 Waƙar haurawa. Ta Dawuda. Da ba don Ubangiji ya kasance a gefenmu ba, bari Isra’ila yă ce,
שיר המעלות לדוד לולי יהוה שהיה לנו-- יאמר-נא ישראל
2 da ba don Ubangiji ya kasance a gefenmu ba sa’ad da aka auka mana,
לולי יהוה שהיה לנו-- בקום עלינו אדם
3 sa’ad da fushinsu ya ƙuna a kanmu, ai, da sun haɗiye mu da rai;
אזי חיים בלעונו-- בחרות אפם בנו
4 da rigyawa ta kwashe mu, da ambaliya ta rufe mu.
אזי המים שטפונו-- נחלה עבר על-נפשנו
5 Da ruwa mai hauka ya share mu ƙaf.
אזי עבר על-נפשנו-- המים הזידונים
6 Yabo ya tabbata ga Ubangiji, wanda bai bari aka yayyage mu da haƙoransu ba.
ברוך יהוה-- שלא נתננו טרף לשניהם
7 Mun tsira kamar tsuntsu daga tarkon mai farauta; an tsinke tarko, muka kuwa tsira.
נפשנו-- כצפור נמלטה מפח יוקשים הפח נשבר ואנחנו נמלטנו
8 Taimakonmu yana a sunan Ubangiji, Wanda ya yi sama da ƙasa.
עזרנו בשם יהוה-- עשה שמים וארץ

< Zabura 124 >