< Zabura 123 >

1 Waƙar haurawa. Na tā da idanuna gare ka, gare ka da kursiyinka yake cikin sama.
(Sang til Festrejserne.) Jeg løfter mine Øjne til dig, som troner i Himlen!
2 Kamar yadda idanun bayi suna duban hannun maigidansu, kamar yadda idanun baiwa suna duban hannun uwargijiyarta, haka idanunmu suna duban Ubangiji Allahnmu, sai ya nuna mana jinƙansa.
Som trælles øjne følger deres Herres Hånd, som en Trælkvindes Øjne følger hendes Frues Hånd, så følger vore Øjne HERREN vor Gud, til han er os nådig.
3 Ka yi mana jinƙai, ya Ubangiji, ka yi mana jinƙai, gama mun jimre da reni mai yawa.
Forbarm dig over os, HERRE, forbarm dig! Thi overmætte er vi af Spot,
4 Mun jimre da wulaƙanci daga masu girman kai, reni mai yawa daga masu fariya.
overmæt er vor Sjæl af de sorgløses Hån, de stoltes Spot!

< Zabura 123 >