< Zabura 121 >
1 Waƙar haurawa. Na tā da idanuna zuwa wajen tuddai, ta ina ne taimakona zai zo?
2 Taimakona zai zo daga wurin Ubangiji, wanda ya kafa sama da ƙasa.
3 Ba zai bari ƙafarka tă yi santsi ba, shi da yake tsaronka ba zai yi gyangyaɗi ba;
4 tabbatacce, shi da yake tsaron Isra’ila ba ya gyangyaɗi ko barci.
5 Ubangiji yana tsaronka, Ubangiji ne inuwa a hannun damanka;
6 rana ba za tă buge ka cikin yini ba balle wata da dare.
7 Ubangiji zai kiyaye ka daga dukan masifa, zai tsare ranka;
8 Ubangiji zai kiyaye shigarka da fitarka yanzu da har abada kuma.