< Zabura 12 >

1 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da kayan kiɗi. Bisa ga sheminit. Zabura ta Dawuda. Ka taimaka, Ubangiji, gama masu tsoron Allah ba sa nan kuma; masu aminci sun ɓace daga cikin mutane.
למנצח על השמינית מזמור לדוד הושיעה יהוה כי גמר חסיד כי פסו אמונים מבני אדם׃
2 Kowa yana yi wa maƙwabcinsa ƙarya; zaƙin bakinsu maganar ƙarya ce suna cike da ruɗu a zukatansu.
שוא ידברו איש את רעהו שפת חלקות בלב ולב ידברו׃
3 Bari Ubangiji yă yanke dukan zaƙin bakinsu da kuma kowane harshe mai fariya,
יכרת יהוה כל שפתי חלקות לשון מדברת גדלות׃
4 masu cewa, “Da harsunanmu za mu yi nasara; leɓunanmu za su kāre mu, wane ne maigidanmu?”
אשר אמרו ללשננו נגביר שפתינו אתנו מי אדון לנו׃
5 “Saboda danniyar marasa ƙarfi da kuma nishin masu bukata, zan tashi yanzu,” in ji Ubangiji. “Zan kāre su daga masu yin musu sharri.”
משד עניים מאנקת אביונים עתה אקום יאמר יהוה אשית בישע יפיח לו׃
6 Kalmomin Ubangiji kuwa ba su da kuskure, kamar azurfan da aka tace cikin matoyan yumɓu, aka tsabtacce sau bakwai.
אמרות יהוה אמרות טהרות כסף צרוף בעליל לארץ מזקק שבעתים׃
7 Ya Ubangiji, za ka kiyaye mu lafiya ka tsare mu daga irin mutanen nan har abada.
אתה יהוה תשמרם תצרנו מן הדור זו לעולם׃
8 Mugaye suna yawo a sake sa’ad da ake girmama abin da ba shi da kyau a cikin mutane.
סביב רשעים יתהלכון כרם זלות לבני אדם׃

< Zabura 12 >