< Zabura 119 >

1 Albarka ta tabbata ga waɗanda rayuwarsu ba ta da abin zargi, waɗanda suke tafiya bisa ga dokar Ubangiji.
אשרי תמימי דרך ההלכים בתורת יהוה׃
2 Albarka ta tabbata ga waɗanda suke kiyaye ƙa’idodinsa suke kuma nemansa da dukan zuciyarsu.
אשרי נצרי עדתיו בכל לב ידרשוהו׃
3 Ba sa yin wani abin da ba daidai ba; suna tafiya a hanyoyinsa.
אף לא פעלו עולה בדרכיו הלכו׃
4 Ka shimfiɗa farillan da dole a yi biyayya da su.
אתה צויתה פקדיך לשמר מאד׃
5 Kash, da a ce hanyoyina tsayayyu ne a yin biyayya da ƙa’idodinka mana!
אחלי יכנו דרכי לשמר חקיך׃
6 Da ba zan sha kunya ba sa’ad da na lura da dukan umarnanka.
אז לא אבוש בהביטי אל כל מצותיך׃
7 Zan yabe ka da zuciya ta gaskiya yayinda nake koyon dokokinka masu adalci.
אודך בישר לבב בלמדי משפטי צדקך׃
8 Zan yi biyayya da ƙa’idodinka; kada ka yashe ni ɗungum.
את חקיך אשמר אל תעזבני עד מאד׃
9 Yaya matashi zai kiyaye hanyarsa da tsabta? Sai ta yin rayuwa bisa ga maganarka.
במה יזכה נער את ארחו לשמר כדברך׃
10 Na neme ka da dukan zuciyata; kada ka bar ni in kauce daga umarnanka.
בכל לבי דרשתיך אל תשגני ממצותיך׃
11 Na ɓoye maganarka a cikin zuciyata don kada in yi maka zunubi.
בלבי צפנתי אמרתך למען לא אחטא לך׃
12 Yabo ya tabbata gare ka, ya Ubangiji; ka koya mini ƙa’idodinka.
ברוך אתה יהוה למדני חקיך׃
13 Da leɓunana na ba da labarin dukan dokokin da suka fito bakinka.
בשפתי ספרתי כל משפטי פיך׃
14 Na yi farin ciki da bin farillanka yadda mutum yakan yi farin ciki da arziki mai yawa.
בדרך עדותיך ששתי כעל כל הון׃
15 Na yi tunani a kan farillanka na kuma lura da hanyoyinka.
בפקדיך אשיחה ואביטה ארחתיך׃
16 Na yi murna a cikin ƙa’idodinka; ba zan ƙyale maganarka ba.
בחקתיך אשתעשע לא אשכח דברך׃
17 Ka yi alheri ga bawanka, zan kuwa rayu; zan yi biyayya da maganarka.
גמל על עבדך אחיה ואשמרה דברך׃
18 Ka buɗe idanuna don in iya gani abubuwan banmamaki a cikin dokarka.
גל עיני ואביטה נפלאות מתורתך׃
19 Ni baƙo ne a duniya; kada ka ɓoye mini umarnanka.
גר אנכי בארץ אל תסתר ממני מצותיך׃
20 Zuciyata ta ƙosa saboda marmari don dokokinka koyaushe.
גרסה נפשי לתאבה אל משפטיך בכל עת׃
21 Ka tsawata wa masu fariya, waɗanda suke la’anta waɗanda kuma suka kauce daga umarnanka.
גערת זדים ארורים השגים ממצותיך׃
22 Ka cire mini ba’a da reni, gama ina kiyaye farillanka.
גל מעלי חרפה ובוז כי עדתיך נצרתי׃
23 Ko da yake masu mulki sun zauna tare suna ɓata mini suna, bawanka zai yi tunani a kan ƙa’idodinka.
גם ישבו שרים בי נדברו עבדך ישיח בחקיך׃
24 Farillanka ne abin farin cikina; su ne mashawartana.
גם עדתיך שעשעי אנשי עצתי׃
25 An kwantar da ni ƙasa cikin ƙura; ka kiyaye raina bisa ga maganarka.
דבקה לעפר נפשי חיני כדברך׃
26 Na ba da labari hanyoyina ka kuma amsa mini; ka koya mini ƙa’idodinka.
דרכי ספרתי ותענני למדני חקיך׃
27 Bari in gane koyarwar farillanka; sa’an nan zan yi tunani a kan abubuwan banmamakinka.
דרך פקודיך הבינני ואשיחה בנפלאותיך׃
28 Raina ya gaji da baƙin ciki; ka ƙarfafa ni bisa ga maganarka.
דלפה נפשי מתוגה קימני כדברך׃
29 Ka kiyaye ni daga hanyoyin ruɗu; ka yi mini alheri ta wurin dokokinka.
דרך שקר הסר ממני ותורתך חנני׃
30 Na zaɓi hanyar gaskiya; na sa zuciyata a kan dokokinka.
דרך אמונה בחרתי משפטיך שויתי׃
31 Na riƙe farillanka kankan, ya Ubangiji; kada ka sa in sha kunya.
דבקתי בעדותיך יהוה אל תבישני׃
32 Ina gudu a kan hanyar umarnanka, gama ka’yantar da zuciyata.
דרך מצותיך ארוץ כי תרחיב לבי׃
33 Ka koya mini Ya Ubangiji, don in bi ƙa’idodinka; sa’an nan zan kiyaye su har ƙarshe.
הורני יהוה דרך חקיך ואצרנה עקב׃
34 Ka ba ni ganewa, zan kuwa kiyaye dokarka in kuma yi biyayya da ita da dukan zuciyata.
הבינני ואצרה תורתך ואשמרנה בכל לב׃
35 Ka bi da ni a hanyar umarnanka, gama a can zan sami farin ciki.
הדריכני בנתיב מצותיך כי בו חפצתי׃
36 Ka juye zuciyata wajen farillanka ba wajen riba ta sonkai ba.
הט לבי אל עדותיך ואל אל בצע׃
37 Ka juye idanuna daga abubuwa marasa amfani; ka kiyaye raina bisa ga maganarka.
העבר עיני מראות שוא בדרכך חיני׃
38 Ka cika alkawarinka ga bawanka, saboda a ji tsoronka.
הקם לעבדך אמרתך אשר ליראתך׃
39 Ka kawar da shan kunyar da nake tsoro, gama dokokinka nagari ne.
העבר חרפתי אשר יגרתי כי משפטיך טובים׃
40 Ina marmarin farillanka ƙwarai! Ka kiyaye raina cikin adalcinka.
הנה תאבתי לפקדיך בצדקתך חיני׃
41 Bari ƙaunarka marar ƙarewa ta zo gare ni, ya Ubangiji, cetonka bisa ga alkawarinka;
ויבאני חסדך יהוה תשועתך כאמרתך׃
42 sa’an nan zan amsa wa masu cin mutuncina, gama na dogara ga maganarka.
ואענה חרפי דבר כי בטחתי בדברך׃
43 Kada ka ƙwace maganarka daga bakina, gama na sa zuciyata a dokokinka.
ואל תצל מפי דבר אמת עד מאד כי למשפטך יחלתי׃
44 Kullayaumi zan yi biyayya da dokokinka, har abada abadin.
ואשמרה תורתך תמיד לעולם ועד׃
45 Zan yi ta yawo a sake gama na nemi farillanka.
ואתהלכה ברחבה כי פקדיך דרשתי׃
46 Zan yi maganar farillanka a gaban sarakuna ba kuwa za a kunyata ni ba,
ואדברה בעדתיך נגד מלכים ולא אבוש׃
47 gama ina farin ciki da umarnanka saboda ina ƙaunarsu.
ואשתעשע במצותיך אשר אהבתי׃
48 Na ɗaga hannuwana ga umarnanka, waɗanda nake ƙauna, ina kuma tunani a kan ƙa’idodinka.
ואשא כפי אל מצותיך אשר אהבתי ואשיחה בחקיך׃
49 Tuna da maganarka ga bawanka, gama ka ba ni bege.
זכר דבר לעבדך על אשר יחלתני׃
50 Ta’aziyyata cikin wahalata ita ce alkawarinka yana kiyaye raina.
זאת נחמתי בעניי כי אמרתך חיתני׃
51 Masu fariya suna yi mini ba’a ba tare da an hana su ba, amma ban rabu da dokar ba.
זדים הליצני עד מאד מתורתך לא נטיתי׃
52 Na tuna da dokokinka na tun dā, ya Ubangiji, na kuwa sami ta’aziyya a cikinsu.
זכרתי משפטיך מעולם יהוה ואתנחם׃
53 Fushi ya kama ni saboda mugaye, waɗanda suka keta dokokinka.
זלעפה אחזתני מרשעים עזבי תורתך׃
54 Ƙa’idodinka su ne kan waƙata a duk inda na sauka.
זמרות היו לי חקיך בבית מגורי׃
55 Da dare na tuna da sunanka, ya Ubangiji, zan kuwa kiyaye dokarka.
זכרתי בלילה שמך יהוה ואשמרה תורתך׃
56 Wannan shi ne na saba yi, ina yin biyayya da farillanka.
זאת היתה לי כי פקדיך נצרתי׃
57 Kai ne rabona, ya Ubangiji; na yi alkawarin in kiyaye maganarka.
חלקי יהוה אמרתי לשמר דבריך׃
58 Na nemi fuskarka da dukan zuciyata; ka yi mini alheri bisa ga alkawarinka.
חליתי פניך בכל לב חנני כאמרתך׃
59 Na lura da hanyoyina na kuma mayar da matakaina ga farillanka.
חשבתי דרכי ואשיבה רגלי אל עדתיך׃
60 Zan gaggauta ba zan ɓata lokaci ba in yi biyayya da umarnanka.
חשתי ולא התמהמהתי לשמר מצותיך׃
61 Ko da yake mugaye sun ɗaura ni da igiyoyi, ba zan manta da dokokinka ba.
חבלי רשעים עודני תורתך לא שכחתי׃
62 Da tsakar dare nakan tashi in gode maka saboda dokokinka masu adalci.
חצות לילה אקום להודות לך על משפטי צדקך׃
63 Ni aboki ne ga duk mai tsoronka, ga duk wanda yake bin farillanka.
חבר אני לכל אשר יראוך ולשמרי פקודיך׃
64 Duniya ta cika da ƙaunarka, ya Ubangiji; ka koya mini ƙa’idodinka.
חסדך יהוה מלאה הארץ חקיך למדני׃
65 Ka yi wa bawanka alheri bisa ga maganarka, ya Ubangiji.
טוב עשית עם עבדך יהוה כדברך׃
66 Ka koya mini sani da kuma hukunci mai kyau, gama na gaskata a umarnanka.
טוב טעם ודעת למדני כי במצותיך האמנתי׃
67 Kafin in sha wahala na kauce, amma yanzu ina biyayya da maganarka.
טרם אענה אני שגג ועתה אמרתך שמרתי׃
68 Kai nagari ne, kuma abin da kake yi yana da kyau; ka koya mini ƙa’idodinka.
טוב אתה ומטיב למדני חקיך׃
69 Ko da yake masu fariya sun shafe ni da ƙarairayi, na kiyaye farillanka da dukan zuciyata.
טפלו עלי שקר זדים אני בכל לב אצר פקודיך׃
70 Zukatansu sun yi tauri da kuma marasa tausayi amma ina farin ciki a dokarka.
טפש כחלב לבם אני תורתך שעשעתי׃
71 Ya yi kyau da na sha wahala don in koyi ƙa’idodinka.
טוב לי כי עניתי למען אלמד חקיך׃
72 Doka daga bakinka ya fi mini daraja fiye da azurfa da zinariya guda dubu.
טוב לי תורת פיך מאלפי זהב וכסף׃
73 Hannuwanka ne suka yi suka kuma siffanta ni; ka ba ni ganewa don in koyi umarnanka.
ידיך עשוני ויכוננוני הבינני ואלמדה מצותיך׃
74 Bari waɗanda suke tsoronka su yi farin ciki sa’ad da suke gan ni, gama na sa zuciyata a maganarka.
יראיך יראוני וישמחו כי לדברך יחלתי׃
75 Ya Ubangiji na sani, cewa dokokinka masu adalci ne, kuma cikin aminci ka hore ni.
ידעתי יהוה כי צדק משפטיך ואמונה עניתני׃
76 Bari ƙaunarka marar ƙarewa tă yi mini ta’aziyya, bisa ga alkawarinka ga bawanka.
יהי נא חסדך לנחמני כאמרתך לעבדך׃
77 Bari tausayinka yă zo mini don in rayu, gama dokarka ce farin cikina.
יבאוני רחמיך ואחיה כי תורתך שעשעי׃
78 Bari masu girman kai su sha kunya saboda abubuwa marasa kyau da suke yi mini ba dalili; amma zan yi tunani a kan farillanka.
יבשו זדים כי שקר עותוני אני אשיח בפקודיך׃
79 Bari waɗanda suke tsoronka su juya gare ni, waɗanda suka gane da farillanka.
ישובו לי יראיך וידעו עדתיך׃
80 Bari zuciyata ta kasance marar abin zargi wajen ƙa’idodinka, don kada in sha kunya.
יהי לבי תמים בחקיך למען לא אבוש׃
81 Raina ya tafke da marmari don cetonka, amma na sa zuciyata a maganarka.
כלתה לתשועתך נפשי לדברך יחלתי׃
82 Idanuna sun gaji, suna jiran alkawarinka; Na ce, “Yaushe za ka ta’azantar da ni?”
כלו עיני לאמרתך לאמר מתי תנחמני׃
83 Ko da yake ni kamar salkar ruwan inabi ne a cikin hayaƙi, ban manta da ƙa’idodinka ba.
כי הייתי כנאד בקיטור חקיך לא שכחתי׃
84 Har yaushe bawanka zai yi ta jira? Yaushe za ka hukunta masu tsananta mini?
כמה ימי עבדך מתי תעשה ברדפי משפט׃
85 Masu girman kai sun haƙa mini rami, sun ƙetare dokarka.
כרו לי זדים שיחות אשר לא כתורתך׃
86 Dukan umarnanka abin dogara ne; ka taimake ni, gama mutane suna tsananta mini ba dalili.
כל מצותיך אמונה שקר רדפוני עזרני׃
87 Sun kusa gama da ni a duniya, amma ban bar bin farillanka ba.
כמעט כלוני בארץ ואני לא עזבתי פקודיך׃
88 Ka kiyaye raina bisa ga ƙaunarka, zan kuwa yi biyayya da farillan bakinka.
כחסדך חיני ואשמרה עדות פיך׃
89 Maganarka, ya Ubangiji madawwamiya ce; tana nan daram a cikin sammai.
לעולם יהוה דברך נצב בשמים׃
90 Amincinka yana cin gaba cikin dukan zamanai; ka kafa duniya ta kuma dawwama.
לדר ודר אמונתך כוננת ארץ ותעמד׃
91 Dokokinka sun dawwama har yă zuwa yau, gama dukan abubuwa suna maka hidima.
למשפטיך עמדו היום כי הכל עבדיך׃
92 Da ba don dokarka ce farin cikina ba, da na hallaka a cikin azabana.
לולי תורתך שעשעי אז אבדתי בעניי׃
93 Ba zan taɓa manta da farillanka ba, gama ta wurinsu ne ka kiyaye raina.
לעולם לא אשכח פקודיך כי בם חייתני׃
94 Ka cece ni, gama ni naka ne; na yi ƙoƙarin neman farillanka.
לך אני הושיעני כי פקודיך דרשתי׃
95 Mugaye suna jira su hallaka ni, amma zan yi ta tunani a kan farillanka.
לי קוו רשעים לאבדני עדתיך אתבונן׃
96 Ga duk cikakke na ga kāsawa; amma umarnanka ba su da iyaka.
לכל תכלה ראיתי קץ רחבה מצותך מאד׃
97 Kash, ga yadda nake ƙaunar dokarka! Ina tunani a kanta dukan yini.
מה אהבתי תורתך כל היום היא שיחתי׃
98 Umarnanka suna sa in zama mai hikima fiye da abokan gābana, gama kullum suna tare da ni.
מאיבי תחכמני מצותך כי לעולם היא לי׃
99 Ina da ganewa sosai fiye da dukan malamaina, gama ina tunani a kan farillanka.
מכל מלמדי השכלתי כי עדותיך שיחה לי׃
100 Ina da ganewa fiye da dattawa, gama ina biyayya da farillanka.
מזקנים אתבונן כי פקודיך נצרתי׃
101 Na kiyaye ƙafafuna daga kowace muguwar hanya domin in yi biyayya da maganarka.
מכל ארח רע כלאתי רגלי למען אשמר דברך׃
102 Ban rabu da dokokinka ba, gama kai da kanka ne ka koya mini.
ממשפטיך לא סרתי כי אתה הורתני׃
103 Ɗanɗanon maganarka akwai zaki, sun ma fi zuma zaki a bakina!
מה נמלצו לחכי אמרתך מדבש לפי׃
104 Na sami ganewa daga farillanka; saboda haka ina ƙin kowace hanyar da ba daidai ba.
מפקודיך אתבונן על כן שנאתי כל ארח שקר׃
105 Maganarka fitila ce ga ƙafafuna haske kuma a kan hanyata.
נר לרגלי דברך ואור לנתיבתי׃
106 Na yi rantsuwa na kuma tabbatar da shi, cewa zan bi dokokinka masu adalci.
נשבעתי ואקימה לשמר משפטי צדקך׃
107 Na sha wahala sosai; ka kiyaye raina, ya Ubangiji, bisa ga maganarka.
נעניתי עד מאד יהוה חיני כדברך׃
108 Ka karɓi yabon bakina da nake yi da yardar rai, ya Ubangiji, ka kuwa koya mini dokokinka.
נדבות פי רצה נא יהוה ומשפטיך למדני׃
109 Ko da yake kullum ina riƙe da raina a hannuwana, ba zan manta da dokarka ba.
נפשי בכפי תמיד ותורתך לא שכחתי׃
110 Mugaye sun kafa mini tarko, amma ban kauce daga farillanka ba.
נתנו רשעים פח לי ומפקודיך לא תעיתי׃
111 Farillanka su ne gādona har abada; su ne farin cikin zuciyata.
נחלתי עדותיך לעולם כי ששון לבי המה׃
112 Zuciyata ta shirya a kan kiyaye ƙa’idodinka har ƙarshe.
נטיתי לבי לעשות חקיך לעולם עקב׃
113 Na ƙi mutane masu baki biyu, amma ina ƙauna dokarka.
סעפים שנאתי ותורתך אהבתי׃
114 Kai ne mafakata da garkuwata; na sa zuciyata a maganarka.
סתרי ומגני אתה לדברך יחלתי׃
115 Ku rabu da ni, ku masu aikata mugunta, don in kiyaye umarnan Allahna!
סורו ממני מרעים ואצרה מצות אלהי׃
116 Ka raya ni bisa ga alkawarinka, zan kuwa rayu; kada ka bari a gwale sa zuciyata.
סמכני כאמרתך ואחיה ואל תבישני משברי׃
117 Ka riƙe ni za a kuma cece ni; kullayaumi zan ɗauka ƙa’idodinka da muhimmanci.
סעדני ואושעה ואשעה בחקיך תמיד׃
118 Ka ki dukan waɗanda suka kauce daga ƙa’idodinka, gama yaudararsu banza ne.
סלית כל שוגים מחקיך כי שקר תרמיתם׃
119 Dukan mugayen duniya ka zubar kamar datti; saboda haka nake ƙaunar farillanka.
סגים השבת כל רשעי ארץ לכן אהבתי עדתיך׃
120 Naman jikina na rawan jiki don tsoronka; na cika da tsoron dokokinka.
סמר מפחדך בשרי וממשפטיך יראתי׃
121 Na aikata abin da yake mai adalci da kuma daidai; kada ka ni a hannun masu danne ni.
עשיתי משפט וצדק בל תניחני לעשקי׃
122 Ka tabbatar da lafiyar bawanka; kada ka bar masu girman kai su danne ni.
ערב עבדך לטוב אל יעשקני זדים׃
123 Idanuna sun gaji, da jiran cetonka, da jiran alkawarinka mai adalci.
עיני כלו לישועתך ולאמרת צדקך׃
124 Ka yi da bawanka bisa ga ƙaunarka ka kuma koya mini ƙa’idodinka.
עשה עם עבדך כחסדך וחקיך למדני׃
125 Ni bawanka ne, ka ba ni fahimi don in gane farillanka.
עבדך אני הבינני ואדעה עדתיך׃
126 Lokaci ya yi da za ka yi wani abu, ya Ubangiji; ana karya dokarka.
עת לעשות ליהוה הפרו תורתך׃
127 Saboda ina ƙaunar umarnanka fiye da zinariya, kai, fiye da zinariya zalla,
על כן אהבתי מצותיך מזהב ומפז׃
128 saboda kuma ina lura da dukan farillanka da kyau, na ƙi kowace hanyar da ba daidai ba.
על כן כל פקודי כל ישרתי כל ארח שקר שנאתי׃
129 Farillanka masu banmamaki ne; saboda haka nake yin biyayya da su.
פלאות עדותיך על כן נצרתם נפשי׃
130 Fassarar maganganunka sukan ba da haske; sukan ba da ganewa ga marar ilimi.
פתח דבריך יאיר מבין פתיים׃
131 Ina hakkin da bakina a buɗe, ina marmarin umarnanka.
פי פערתי ואשאפה כי למצותיך יאבתי׃
132 Ka juye wurina ka kuma yi mini jinƙai, yadda kullum ka yi wa waɗanda suke ƙaunar sunanka.
פנה אלי וחנני כמשפט לאהבי שמך׃
133 Ka bi da sawuna bisa ga maganarka; kada ka bar zunubi yă mallake ni.
פעמי הכן באמרתך ואל תשלט בי כל און׃
134 Ka fanshe ni daga mutane masu danniya, don in yi biyayya da farillanka.
פדני מעשק אדם ואשמרה פקודיך׃
135 Ka sa fuskarka ta haskaka a kan bawanka ka kuma koya mini ƙa’idodinka.
פניך האר בעבדך ולמדני את חקיך׃
136 Hawaye suna malalowa daga idanuna kamar rafi, gama ba a biyayya da dokarka.
פלגי מים ירדו עיני על לא שמרו תורתך׃
137 Mai adalci ne kai, ya Ubangiji, dokokinka kuma daidai ne.
צדיק אתה יהוה וישר משפטיך׃
138 Farillan da ka shimfiɗa masu adalci ne; su kuma abin dogara ne ƙwarai.
צוית צדק עדתיך ואמונה מאד׃
139 Kishina ya cinye ni ɗungum, gama abokan gābana sun yi biris da maganganunka.
צמתתני קנאתי כי שכחו דבריך צרי׃
140 An gwada alkawuranka sarai, bawanka kuwa yana ƙaunarsu.
צרופה אמרתך מאד ועבדך אהבה׃
141 Ko da yake ni ba kome ba ne an kuwa rena ni, ba na manta da farillanka.
צעיר אנכי ונבזה פקדיך לא שכחתי׃
142 Adalcinka dawwammame ne dokar kuma gaskiya ce.
צדקתך צדק לעולם ותורתך אמת׃
143 Wahala da damuwa suna a kaina, amma umarnanka su ne farin cikina.
צר ומצוק מצאוני מצותיך שעשעי׃
144 Farillanka daidai ne har abada; ka ba ni ganewa don in rayu.
צדק עדותיך לעולם הבינני ואחיה׃
145 Na yi kira da dukan zuciyata; ka amsa mini, ya Ubangiji, zan kuwa yi biyayya da ƙa’idodinka.
קראתי בכל לב ענני יהוה חקיך אצרה׃
146 Na yi kira gare ka; ka cece ni zan kuwa kiyaye farillanka.
קראתיך הושיעני ואשמרה עדתיך׃
147 Na tashi kafin fitowar rana na kuma yi kukan neman taimako; na sa zuciyata a maganarka.
קדמתי בנשף ואשועה לדבריך יחלתי׃
148 Ban rufe idanuna ba dukan dare, don in yi tunani a kan alkawuranka.
קדמו עיני אשמרות לשיח באמרתך׃
149 Ka ji muryata bisa ga ƙaunarka; ka kiyaye raina, ya Ubangiji, bisa ga dokokinka.
קולי שמעה כחסדך יהוה כמשפטך חיני׃
150 Waɗanda suke ƙirƙiro mugayen dabaru suna nan kusa, amma suna nesa da dokarka.
קרבו רדפי זמה מתורתך רחקו׃
151 Duk da haka kana kusa, ya Ubangiji, kuma dukan umarnanka gaskiya ne.
קרוב אתה יהוה וכל מצותיך אמת׃
152 Tun tuni na koyi daga farillanka cewa ka kafa su su kasance har abada.
קדם ידעתי מעדתיך כי לעולם יסדתם׃
153 Ka dubi wahalata ka cece ni, gama ban manta da dokarka ba.
ראה עניי וחלצני כי תורתך לא שכחתי׃
154 Ka kāre manufata ka kuma fanshe ni, ka cece rai na kamar yadda ka alkawarta!
ריבה ריבי וגאלני לאמרתך חיני׃
155 Ceto yana nesa da mugaye, gama ba sa neman ƙa’idodinka.
רחוק מרשעים ישועה כי חקיך לא דרשו׃
156 Tausayinka da girma yake, ya Ubangiji; ka kiyaye raina bisa ga dokokinka.
רחמיך רבים יהוה כמשפטיך חיני׃
157 Maƙiya masu yawa ne suke tsananta mini, amma ban rabu da farillanka ba.
רבים רדפי וצרי מעדותיך לא נטיתי׃
158 Na dubi marasa aminci da ƙyama, gama ba sa yin biyayya da maganarka.
ראיתי בגדים ואתקוטטה אשר אמרתך לא שמרו׃
159 Dubi yadda nake ƙaunar farillanka; ka kiyaye raina, ya Ubangiji, bisa ga ƙaunarka.
ראה כי פקודיך אהבתי יהוה כחסדך חיני׃
160 Dukan maganganunka gaskiya ne; dukan dokokinka masu adalci madawwami ne.
ראש דברך אמת ולעולם כל משפט צדקך׃
161 Masu mulki suna tsananta mini ba dalili, amma zuciyata na rawan jiki game da maganarka.
שרים רדפוני חנם ומדבריך פחד לבי׃
162 Ina farin ciki da alkawarinka kamar yadda wani kan sami ganima mai girma.
שש אנכי על אמרתך כמוצא שלל רב׃
163 Na ƙi ina kuma ƙyamar ƙarya amma ina ƙaunar dokarka.
שקר שנאתי ואתעבה תורתך אהבתי׃
164 Sau bakwai a rana ina yabonka saboda dokokinka masu adalci.
שבע ביום הללתיך על משפטי צדקך׃
165 Waɗanda suke ƙaunar dokarka suna da babban salama, kuma babu abin da zai sa su yi tuntuɓe.
שלום רב לאהבי תורתך ואין למו מכשול׃
166 Ina jiran cetonka, ya Ubangiji, ina kuma bin umarnanka.
שברתי לישועתך יהוה ומצותיך עשיתי׃
167 Ina biyayya da farillanka, gama ina ƙaunarsu ƙwarai.
שמרה נפשי עדתיך ואהבם מאד׃
168 Ina biyayya da farillanka da kuma koyarwarka, gama dukan hanyoyina sanannu ne gare ka.
שמרתי פקודיך ועדתיך כי כל דרכי נגדך׃
169 Bari kukata ta zo gare ka, ya Ubangiji; ka ba ni ganewa bisa ga maganarka.
תקרב רנתי לפניך יהוה כדברך הבינני׃
170 Bari roƙona yă zo gabanka; ka cece ni bisa ga alkawarinka.
תבוא תחנתי לפניך כאמרתך הצילני׃
171 Bari leɓunana su cika da yabonka, gama ka koya mini ƙa’idodinka.
תבענה שפתי תהלה כי תלמדני חקיך׃
172 Bari harshena yă rera game da maganarka, gama dukan umarnanka masu adalci ne.
תען לשוני אמרתך כי כל מצותיך צדק׃
173 Bari hannunka yă kasance a shirye don yă taimake ni, gama na zaɓi farillanka.
תהי ידך לעזרני כי פקודיך בחרתי׃
174 Ina marmarin cetonka, ya Ubangiji, dokarka kuwa ita ce farin cikina.
תאבתי לישועתך יהוה ותורתך שעשעי׃
175 Bari in rayu don in yabe ka, bari kuma dokokinka su raya ni.
תחי נפשי ותהללך ומשפטך יעזרני׃
176 Na kauce kamar ɓatacciyar tunkiya. Ka nemi bawanka, gama ban manta da umarnanka ba.
תעיתי כשה אבד בקש עבדך כי מצותיך לא שכחתי׃

< Zabura 119 >