< Zabura 118 >

1 Ku gode wa Ubangiji, gama nagari ne shi; ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.
הוֹדוּ לַיהֹוָה כִּי־טוֹב כִּי לְעוֹלָם חַסְדּֽוֹ׃
2 Bari Isra’ila yă ce, “Ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.”
יֹאמַר־נָא יִשְׂרָאֵל כִּי לְעוֹלָם חַסְדּֽוֹ׃
3 Bari gidan Haruna yă ce, “Ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.”
יֹאמְרוּ־נָא בֵֽית־אַהֲרֹן כִּי לְעוֹלָם חַסְדּֽוֹ׃
4 Bari waɗanda suke tsoron Ubangiji su ce, “Ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.”
יֹאמְרוּ־נָא יִרְאֵי יְהֹוָה כִּי לְעוֹלָם חַסְדּֽוֹ׃
5 Cikin azabata na yi kuka ga Ubangiji, ya kuwa amsa ta wurin’yantar da ni.
מִֽן־הַמֵּצַר קָרָאתִי יָּהּ עָנָנִי בַמֶּרְחָב יָֽהּ׃
6 Ubangiji yana tare da ni; ba zan ji tsoro ba. Me mutum zai yi mini?
יְהֹוָה לִי לֹא אִירָא מַה־יַּעֲשֶׂה לִי אָדָֽם׃
7 Ubangiji yana tare da ni; shi ne mai taimakona. Zan yi nasara a kan abokan gābana.
יְהֹוָה לִי בְּעֹזְרָי וַאֲנִי אֶרְאֶה בְשֹׂנְאָֽי׃
8 Ya fi kyau in nemi mafaka a wurin Ubangiji da in dogara ga mutum.
טוֹב לַחֲסוֹת בַּיהֹוָה מִבְּטֹחַ בָּאָדָֽם׃
9 Ya fi kyau in nemi mafaka a wurin Ubangiji da in dogara ga sarakuna.
טוֹב לַחֲסוֹת בַּיהֹוָה מִבְּטֹחַ בִּנְדִיבִֽים׃
10 Dukan al’ummai sun kewaye ni, amma a cikin sunan Ubangiji na hallaka su.
כׇּל־גּוֹיִם סְבָבוּנִי בְּשֵׁם יְהֹוָה כִּי אֲמִילַֽם׃
11 Sun kewaye ni a kowane gefe, amma a cikin sunan Ubangiji na hallaka su.
סַבּוּנִי גַם־סְבָבוּנִי בְּשֵׁם יְהֹוָה כִּי אֲמִילַֽם׃
12 Sun rufe ni kamar ƙudan zuma, amma suka mutu nan da nan kamar ƙayayyuwa masu cin wuta; a cikin sunan Ubangiji na hallaka su.
סַבּוּנִי כִדְבוֹרִים דֹּעֲכוּ כְּאֵשׁ קוֹצִים בְּשֵׁם יְהֹוָה כִּי אֲמִילַֽם׃
13 An ture ni baya na kusa fāɗuwa, amma Ubangiji ya taimake ni.
דַּחֹה דְחִיתַנִי לִנְפֹּל וַיהֹוָה עֲזָרָֽנִי׃
14 Ubangiji ne ƙarfina da waƙata; ya zama mai cetona.
עׇזִּי וְזִמְרָת יָהּ וַֽיְהִי־לִי לִישׁוּעָֽה׃
15 Sowa ta farin ciki da nasara sun fito a cikin tentunan adalai, “Hannun dama na Ubangiji ya aikata manyan abubuwa!
קוֹל ׀ רִנָּה וִישׁוּעָה בְּאׇהֳלֵי צַדִּיקִים יְמִין יְהֹוָה עֹשָׂה חָֽיִל׃
16 An ɗaga hannun dama na Ubangiji sama; hannun dama na Ubangiji ya aikata manyan abubuwa!”
יְמִין יְהֹוָה רוֹמֵמָה יְמִין יְהֹוָה עֹשָׂה חָֽיִל׃
17 Ba zan mutu ba amma zan rayu, zan kuwa yi shelar abin da Ubangiji ya yi.
לֹא־אָמוּת כִּֽי־אֶחְיֶה וַאֲסַפֵּר מַעֲשֵׂי יָֽהּ׃
18 Ubangiji ya hore ni sosai, amma bai ba da ni ga mutuwa ba.
יַסֹּר יִסְּרַנִּי יָּהּ וְלַמָּוֶת לֹא נְתָנָֽנִי׃
19 Buɗe mini ƙofofin adalci; zan shiga in kuma yi godiya ga Ubangiji.
פִּתְחוּ־לִי שַׁעֲרֵי־צֶדֶק אָבֹא־בָם אוֹדֶה יָֽהּ׃
20 Wannan ne ƙofar Ubangiji inda adalai za su shiga.
זֶה־הַשַּׁעַר לַיהֹוָה צַדִּיקִים יָבֹאוּ בֽוֹ׃
21 Zan yi maka godiya, domin ka amsa mini; ka zama mai cetona.
אוֹדְךָ כִּי עֲנִיתָנִי וַתְּהִי־לִי לִישׁוּעָֽה׃
22 Zabura Dutsen da magina suka ƙi ya zama mai amfani;
אֶבֶן מָאֲסוּ הַבּוֹנִים הָיְתָה לְרֹאשׁ פִּנָּֽה׃
23 Ubangiji ne ya yi haka, kuma abu mai daraja ne a idanunmu.
מֵאֵת יְהֹוָה הָיְתָה זֹּאת הִיא נִפְלָאת בְּעֵינֵֽינוּ׃
24 Wannan ita ce ranar da Ubangiji ya yi; bari mu yi farin ciki mu kuma yi murna a cikinta.
זֶה־הַיּוֹם עָשָׂה יְהֹוָה נָגִילָה וְנִשְׂמְחָה בֽוֹ׃
25 Ya Ubangiji, ka cece mu; Ya Ubangiji, ka ba mu nasara.
אָנָּא יְהֹוָה הוֹשִׁיעָה נָּא אָנָּא יְהֹוָה הַצְלִיחָה נָּֽא׃
26 Mai albarka ne shi mai zuwa cikin sunan Ubangiji. Daga gidan Ubangiji muna sa muku albarka.
בָּרוּךְ הַבָּא בְּשֵׁם יְהֹוָה בֵּרַכְנוּכֶם מִבֵּית יְהֹוָֽה׃
27 Ubangiji shi ne Allah ya kuma sa haskensa ya haskaka a kanmu. Da kwanoni a hannunmu, muka shiga jerin gwanon biki ku kai su ƙahoni na bagade.
אֵל ׀ יְהֹוָה וַיָּאֶר לָנוּ אִסְרוּ־חַג בַּעֲבֹתִים עַד־קַרְנוֹת הַמִּזְבֵּֽחַ׃
28 Kai ne Allahna, zan kuwa yi maka godiya; kai ne Allahna, zan kuwa ɗaukaka ka.
אֵלִי אַתָּה וְאוֹדֶךָּ אֱלֹהַי אֲרוֹמְמֶֽךָּ׃
29 Ku gode wa Ubangiji, gama nagari ne shi; ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.
הוֹדוּ לַיהֹוָה כִּי־טוֹב כִּי לְעוֹלָם חַסְדּֽוֹ׃

< Zabura 118 >