< Zabura 116 >
1 Ina ƙaunar Ubangiji, gama ya ji muryata; ya ji kukata ta neman jinƙai.
2 Domin ya juye kunnensa gare ni, zan kira gare shi muddin ina da rai.
3 Igiyoyin mutuwa sun shaƙe ni, wahalar kabari sun zo a kaina; na cika da wahala da ɓacin rai. (Sheol )
4 Sai na kira ga sunan Ubangiji na ce, “Ya Ubangiji, ka cece ni!”
5 Ubangiji mai alheri ne da kuma mai adalci; Allahnmu yana cike da tausayi.
6 Ubangiji yana tsare masu tawali’u; sa’ad da nake cikin tsananin bukata, ya cece ni.
7 Ka kwantar da hankali, ya raina, gama Ubangiji mai alheri ne a gare ka.
8 Gama kai, ya Ubangiji, ka ceci raina daga mutuwa, idanuna daga hawaye, ƙafafuna daga tuntuɓe,
9 don in iya tafiya a gaban Ubangiji a ƙasar masu rai.
10 Na gaskata, saboda haka na ce, “An azabtar da ni ƙwarai.”
11 Kuma cikin rikicewana na ce, “Dukan mutane maƙaryata ne.”
12 Yaya zan sāka wa Ubangiji saboda dukan alherinsa gare ni?
13 Zan daga kwaf na ceto in kuma kira ga sunan Ubangiji.
14 Zan cika alkawurana ga Ubangiji a gaban dukan mutanensa.
15 Abu mai daraja a gaban Ubangiji shi ne mutuwar tsarkakansa.
16 Ya Ubangiji, da gaske ni bawanka ne; ni bawanka ne, ɗan baiwarka; ka’yantar da ni daga sarƙoƙi.
17 Zan yi hadayar godiya gare ka in kuma kira bisa sunan Ubangiji.
18 Zan cika alkawurana ga Ubangiji a gaban dukan mutanensa,
19 a filayen gidan Ubangiji, a tsakiyarki, ya Urushalima. Yabi Ubangiji.