< Zabura 115 >
1 Ba gare mu ba, ya Ubangiji, ba gare mu ba amma ga sunanka yă sami ɗaukaka, saboda ƙaunarka da amincinka.
2 Me ya sa al’ummai suke cewa, “Ina Allahnsu?”
3 Allahnmu yana a sama; yana yin duk abin da ya ga dama.
4 Amma gumakansu azurfa da zinariya ne, da hannuwan mutane suka yi.
5 Suna da bakuna, amma ba sa magana, idanu, amma ba sa gani;
6 suna da kunnuwa, amma ba sa ji, hanci, amma ba sa jin ƙanshi
7 suna da hannuwa, amma ba sa iya taɓa kome, ƙafafu, amma ba sa iya tafiya; ba sa iya ce wani abu da maƙogwaronsu.
8 Masu yinsu za su zama kamar su, haka kuma zai kasance da duk wanda ya dogara da su.
9 Ya gidan Isra’ila, ku dogara ga Ubangiji, shi ne mai taimakonsu da garkuwarsu.
10 Ya gidan Haruna, ku dogara ga Ubangiji, shi ne mai taimakonsu da garkuwarsu.
11 Ku da kuke tsoronsa, ku dogara ga Ubangiji, shi ne mai taimakonsu da garkuwarsu.
12 Ubangiji yakan tuna da mu zai kuma albarkace mu. Zai albarkace gidan Isra’ila, zai albarkace gidan Haruna,
13 zai albarkace waɗanda suke tsoron Ubangiji, manya da ƙanana duka.
14 Bari Ubangiji yă sa ku ƙaru, da ku da’ya’yanku.
15 Bari Ubangiji yă albarkace ku, shi Mahalicci sama da ƙasa.
16 Saman sammai na Ubangiji ne, amma ya ba da duniya ga mutum.
17 Ba matattu ba ne masu yabon Ubangiji, waɗanda suke gangara zuwa wurin da ake shiru;
18 mu ne masu ɗaukaka Ubangiji, yanzu da har abada kuma. Yabi Ubangiji.