< Zabura 114 >

1 Sa’ad da Isra’ila ya fito daga Masar, gidan Yaƙub daga mutane masu baƙon harshe,
בצאת ישראל ממצרים בית יעקב מעם לעז
2 Yahuda ya zama wuri mai tsarki na Allah, Isra’ila mallakarsa.
היתה יהודה לקדשו ישראל ממשלותיו
3 Teku ya kalla ya kuma gudu, Urdun ya juye da baya;
הים ראה וינס הירדן יסב לאחור
4 duwatsu suka yi tsalle kamar raguna, tuddai kamar tumaki.
ההרים רקדו כאילים גבעות כבני-צאן
5 Me ya sa, ya teku, kika gudu, Ya Urdun, ka juya baya,
מה-לך הים כי תנוס הירדן תסב לאחור
6 ku duwatsu, kuka yi tsalle kamar raguna, ku tuddai, kamar tumaki?
ההרים תרקדו כאילים גבעות כבני-צאן
7 Ki yi rawar jiki, ya duniya, a gaban Ubangiji, a gaban Allah na Yaƙub,
מלפני אדון חולי ארץ מלפני אלוה יעקב
8 wanda ya juye dutse ya zama tafki, dutse mai ƙarfi zuwa maɓulɓulan ruwa.
ההפכי הצור אגם-מים חלמיש למעינו-מים

< Zabura 114 >