< Zabura 111 >
1 Yabi Ubangiji. Zan ɗaukaka Ubangiji da dukan zuciyata a cikin majalisar masu aikata gaskiya da kuma a cikin taro.
2 Ayyukan Ubangiji da girma suke; dukan waɗanda suke farin ciki da su suna tunaninsu.
3 Ayyukansa masu ɗaukaka da kuma daraja ne, adalcinsa kuma zai dawwama har abada.
4 Ya sa a tuna da abubuwa masu banmamaki nasa; Ubangiji mai alheri ne mai tausayi kuma.
5 Yana ba da abinci ga waɗanda suke tsoronsa; yakan tuna da alkawarinsa har abada.
6 Ya nuna wa mutanensa ikon ayyukansa, yana ba su ƙasashen waɗansu al’ummai.
7 Ayyukan hannuwansa masu aminci ne da kuma gaskiya; dukan farillansa abin dogara ne.
8 Tsayayyu ne har abada abadin, ana yinsu cikin aminci da kuma gaskiya.
9 Yana ba da ceto ga mutanensa; ya kafa alkawarinsa har abada, tsarki da banrazana ne sunansa.
10 Tsoron Ubangiji ne mafarin hikima; dukan waɗanda suke bin farillansa suna da ganewa mai kyau. Gare shi ne madawwamin yabo.