< Zabura 110 >

1 Ta Dawuda. Zabura ce. Ubangiji ya ce wa Ubangijina, “Zauna a hannun damana, sai na sa abokan gābanka su zama matashin sawunka.”
לדוד מזמור נאם יהוה לאדני--שב לימיני עד-אשית איביך הדם לרגליך
2 Ubangiji zai fadada ikon sandan mulkinka daga Sihiyona za ka yi mulki a tsakiyar abokan gābanka.
מטה-עזך--ישלח יהוה מציון רדה בקרב איביך
3 Rundunarka za su so yin yaƙi a ranarka ta yaƙi. Saye cikin ɗaukaka mai tsarki, daga cikin ciki na safiya za ka karɓi raɓar ƙuruciyarka.
עמך נדבת ביום חילך בהדרי-קדש מרחם משחר לך טל ילדתיך
4 Ubangiji ya rantse ba zai kuma canja zuciyarsa ba, “Kai firist ne har abada, bisa ga tsarin Melkizedek.”
נשבע יהוה ולא ינחם-- אתה-כהן לעולם על-דברתי מלכי-צדק
5 Ubangiji yana a hannun damanka; zai murƙushe sarakuna a ranar fushinsa.
אדני על-ימינך מחץ ביום-אפו מלכים
6 Zai hukunta al’ummai, yana tarawa gawawwaki yana kuma murƙushe masu mulkin dukan duniya.
ידין בגוים מלא גויות מחץ ראש על-ארץ רבה
7 Zai sha daga rafin da yake kusa da hanya; saboda haka zai ɗaga kansa sama.
מנחל בדרך ישתה על-כן ירים ראש

< Zabura 110 >