< Zabura 109 >
1 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta Dawuda. Zabura ce. Ya Allah, wanda nake yabo, kada ka yi shiru,
2 gama mugaye da masu ruɗu sun buɗe bakunansu a kaina; sun yi magana a kaina da harsunan ƙarya.
3 Da kalmomin ƙiyayya sun kewaye ni; sun tasar mini ba dalili.
4 A maimakon ƙauna sun sāka mini da zargi, amma ni mutum ne mai addu’a.
5 Sun sāka mini alheri da mugunta, ƙauna kuma da ƙiyayya.
6 Ka naɗa mugun mutum yă yi hamayya da shi; bari mai zargi yă tsaya a hannun damansa.
7 Sa’ad da aka yi masa shari’a, bari a same shi da laifi, bari kuma addu’o’insa su hukunta shi.
8 Bari kwanakinsa su zama kaɗan; bari wani yă ɗauki wurinsa na shugabanci.
9 Bari’ya’yansa su zama marayu matarsa kuma gwauruwa.
10 Bari’ya’yansa su zama masu yawo suna bara; bari a yi ta koransu daga gidajensu da suke kufai.
11 Bari mai binsa bashi yă ƙwace dukan abin da yake da shi; bari baƙi su washe amfanin aikinsa.
12 Bari kada kowa yă yi masa alheri ko yă ji tausayin marayunsa.
13 Bari duk zuriyarsa su mutu, a shafe sunayensu daga tsara mai zuwa.
14 Bari a tuna da laifin kakanninsa a gaban Ubangiji; bari kada a taɓa shafe zunubin mahaifiyarsa.
15 Bari zunubansu su kasance a gaban Ubangiji kullum, don yă sa a manta da su daga duniya.
16 Gama bai taɓa yin tunanin yin alheri ba, amma ya tsananta wa matalauta da mabukata da kuma masu fid da zuciya har suka mutu.
17 Yana jin daɗin la’antarwa, bari yă dawo a kansa; ba ya son sa albarka, bari kada kowa yă sa masa albarka.
18 Ya sa la’antarwa kamar rigarsa; ta shiga cikin jikinsa kamar ruwa, cikin ƙasusuwansa kamar mai.
19 Bari tă zama kamar mayafin da aka ɗaura kewaye da shi, kamar ɗamara da aka ɗaura kewaye da shi har abada.
20 Bari wannan yă zama sakayyar Ubangiji ga masu zargina, ga waɗanda suke mugayen maganganu a kaina.
21 Amma kai, ya Ubangiji Mai Iko Duka, ka yi da ni da kyau saboda sunanka; ta alherin ƙaunarka, ka cece ni.
22 Gama ni matalauci ne mai bukata kuma, zuciyata kuwa ta yi rauni a cikina.
23 Na ɓace kamar inuwar yamma; ana kakkaɓe ni kamar fāra.
24 Gwiwoyina suna mutuwa saboda azumi; jikina ya rame ba kuma ƙarfi.
25 Na zama abin dariya ga masu zargina; sa’ad da suka gan ni, suka kaɗa kawunansu.
26 Ka taimake ni, ya Ubangiji Allahna; ka cece ni bisa ga ƙaunarka.
27 Bari su san cewa hannunka ne, cewa kai ne, ya Ubangiji, ka yi shi.
28 Za su iya la’anta, amma kai za ka sa albarka; sa’ad da suka tasar za su sha kunya, amma bawanka zai yi farin ciki.
29 Masu zargina za su sha kunya za a rufe su da kunya kamar mayafi.
30 Da bakina zan ɗaukaka Ubangiji sosai; cikin babban taro zan yabe shi.
31 Gama yana tsaya a hannun damar mai bukata, don yă cece ransa daga waɗanda suke hukunta shi.