< Zabura 107 >

1 Ku yi godiya ga Ubangiji, gama nagari ne shi; ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.
הדו ליהוה כי טוב כי לעולם חסדו׃
2 Bari fansassu na Ubangiji su faɗa wannan, su da aka fansa daga hannun maƙiyi,
יאמרו גאולי יהוה אשר גאלם מיד צר׃
3 su da ya tattara daga ƙasashe, daga gabas da yamma, daga arewa da kudu.
ומארצות קבצם ממזרח וממערב מצפון ומים׃
4 Waɗansu sun yi ta yawo a jejin hamada, ba su sami hanya zuwa birnin da za su zauna ba.
תעו במדבר בישימון דרך עיר מושב לא מצאו׃
5 Sun ji yunwa da ƙishirwa, suka kuma fid da zuciya.
רעבים גם צמאים נפשם בהם תתעטף׃
6 Sa’an nan suka yi kuka ga Ubangiji cikin wahalarsu, ya kuma cece su daga damuwarsu.
ויצעקו אל יהוה בצר להם ממצוקותיהם יצילם׃
7 Ya bishe su ta miƙaƙƙiyar hanya zuwa birnin da za su zauna.
וידריכם בדרך ישרה ללכת אל עיר מושב׃
8 Bari su yi godiya ga Ubangiji saboda ƙaunarsa marar ƙarewa da kuma ayyukansa masu banmamaki saboda mutane,
יודו ליהוה חסדו ונפלאותיו לבני אדם׃
9 gama yana shayar da masu ƙishirwa yana kuma ƙosar da mayunwata da abubuwa masu kyau.
כי השביע נפש שקקה ונפש רעבה מלא טוב׃
10 Waɗansu sun zauna a cikin duhu da kuma zurfin ɓacin rai,’yan kurkuku suna wahala cikin sarƙoƙin ƙarfe,
ישבי חשך וצלמות אסירי עני וברזל׃
11 gama sun yi tayarwa a kan maganar Allah suka ƙi shawarar Mafi Ɗaukaka.
כי המרו אמרי אל ועצת עליון נאצו׃
12 Saboda haka ya ba da su ga aiki mai wuya; suka yi tuntuɓe, kuma ba mai taimako.
ויכנע בעמל לבם כשלו ואין עזר׃
13 Sa’an nan suka yi kuka ga Ubangiji cikin wahalarsu, ya kuwa cece su daga damuwarsu.
ויזעקו אל יהוה בצר להם ממצקותיהם יושיעם׃
14 Ya fitar da su daga duhu da zurfin ɓaci rai ya tsintsinke sarƙoƙinsu.
יוציאם מחשך וצלמות ומוסרותיהם ינתק׃
15 Bari su yi godiya ga Ubangiji saboda ƙaunarsa marar ƙarewa da kuma ayyukansa masu banmamaki saboda mutane,
יודו ליהוה חסדו ונפלאותיו לבני אדם׃
16 gama ya farfashe ƙofofin tagulla ya kuma ragargaza ƙyamaren ƙarfe.
כי שבר דלתות נחשת ובריחי ברזל גדע׃
17 Waɗansu suka zama wawaye ta wurin hanyoyinsu na tayarwa suka kuwa sha wahala saboda laifofinsu.
אולים מדרך פשעם ומעונתיהם יתענו׃
18 Ba su so su ga abinci ba suka kuwa kai bakin mutuwa.
כל אכל תתעב נפשם ויגיעו עד שערי מות׃
19 Sa’an nan suka yi kuka ga Ubangiji cikin wahalarsu, ya kuwa cece su daga damuwarsu.
ויזעקו אל יהוה בצר להם ממצקותיהם יושיעם׃
20 Ya ba da umarninsa ya kuma warkar da su ya kuɓutar da su daga kabari.
ישלח דברו וירפאם וימלט משחיתותם׃
21 Bari su yi godiya ga Ubangiji saboda ƙaunarsa marar ƙarewa da kuma ayyukansa masu banmamaki saboda mutane.
יודו ליהוה חסדו ונפלאותיו לבני אדם׃
22 Bari su miƙa hadaya ta godiya su kuma ba da labarin ayyukansa da waƙoƙin farin ciki.
ויזבחו זבחי תודה ויספרו מעשיו ברנה׃
23 Waɗansu suka yi tafiya a teku cikin jiragen ruwa; su’yan kasuwa ne a manyan ruwaye.
יורדי הים באניות עשי מלאכה במים רבים׃
24 Sun ga ayyukan Ubangiji, ayyukansa masu banmamaki a cikin zurfin teku.
המה ראו מעשי יהוה ונפלאותיו במצולה׃
25 Gama ya yi magana ya kuma sa iska mai ƙarfi ta tashi ya ɗaga raƙuman ruwa sama.
ויאמר ויעמד רוח סערה ותרומם גליו׃
26 Suka hau zuwa sammai suka kuma tsinduma cikin zurfafa; a cikin azabarsu sai ƙarfin halinsu ya karai.
יעלו שמים ירדו תהומות נפשם ברעה תתמוגג׃
27 Suka yi tangaɗi suna tuntuɓe kamar bugaggu; suka kuma kai ga ƙarshen dabararsu.
יחוגו וינועו כשכור וכל חכמתם תתבלע׃
28 Sai suka yi kuka ga Ubangiji cikin wahalarsu, ya kuwa fitar da su daga damuwarsu.
ויצעקו אל יהוה בצר להם וממצוקתיהם יוציאם׃
29 Ya kwantar da hadiri suka yi tsit; raƙuman ruwan teku suka yi shiru.
יקם סערה לדממה ויחשו גליהם׃
30 Suka yi murna sa’ad da wuri ya kwanta, ya kuma bishe su zuwa inda suka so su kai.
וישמחו כי ישתקו וינחם אל מחוז חפצם׃
31 Bari su yi godiya ga Ubangiji saboda ƙaunarsa marar ƙarewa da kuma ayyukansa masu banmamaki saboda mutane.
יודו ליהוה חסדו ונפלאותיו לבני אדם׃
32 Bari su ɗaukaka shi cikin taron mutane su kuma yabe shi cikin taron dattawa.
וירממוהו בקהל עם ובמושב זקנים יהללוהו׃
33 Ya mai da koguna suka zama hamada, maɓulɓulai masu gudu suka zama ƙasa mai ƙishirwa,
ישם נהרות למדבר ומצאי מים לצמאון׃
34 ƙasa mai amfani kuma suka zama gishiri marar amfani, saboda muguntar waɗanda suka zauna a can.
ארץ פרי למלחה מרעת ישבי בה׃
35 Ya mai da hamada ya zama tafkunan ruwa busasshiyar ƙasa kuma zuwa maɓulɓulai masu gudu;
ישם מדבר לאגם מים וארץ ציה למצאי מים׃
36 a can ya kai mayunwata su yi zama, ya kuma samo birnin da za su zauna.
ויושב שם רעבים ויכוננו עיר מושב׃
37 Suka yi shuka a gonaki suka dasa inabi suka kuma girbe amfani gona;
ויזרעו שדות ויטעו כרמים ויעשו פרי תבואה׃
38 ya albarkace su, yawansu kuma ya ƙaru, bai kuwa bar garkunansu suka ragu ba.
ויברכם וירבו מאד ובהמתם לא ימעיט׃
39 Sa’an nan yawansu ya ragu, aka kuma ƙasƙantar da su ta wurin danniya, bala’i da kuma baƙin ciki;
וימעטו וישחו מעצר רעה ויגון׃
40 shi da yake kawo reni a kan manyan mutane ya sa suka yi ta yawo a cikin jejin da ba hanya.
שפך בוז על נדיבים ויתעם בתהו לא דרך׃
41 Amma ya fid da mabukata daga wahalarsu ya kuma ƙara iyalansu da tumakinsu.
וישגב אביון מעוני וישם כצאן משפחות׃
42 Masu yin gaskiya suka gani suka yi farin ciki amma dukan mugaye suka rufe bakunansu.
יראו ישרים וישמחו וכל עולה קפצה פיה׃
43 Duk mai hikima, bari yă ji waɗannan abubuwa yă kuma lura da ƙauna mai girma ta Ubangiji.
מי חכם וישמר אלה ויתבוננו חסדי יהוה׃

< Zabura 107 >