< Zabura 106 >

1 Yabi Ubangiji. Yi godiya ga Ubangiji, gama nagari ne shi; ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.
הללו-יה הודו ליהוה כי-טוב-- כי לעולם חסדו
2 Wane ne zai furta manyan ayyukan Ubangiji ko yă furta cikakken yabonsa?
מי--ימלל גבורות יהוה ישמיע כל-תהלתו
3 Masu albarka ne waɗanda suke yin adalci, waɗanda kullum suke yin abin da yake daidai.
אשרי שמרי משפט עשה צדקה בכל-עת
4 Ka tuna da ni, ya Ubangiji, sa’ad da ka nuna alheri ga mutanenka, ka zo ka taimake ni sa’ad da ka cece su,
זכרני יהוה ברצון עמך פקדני בישועתך
5 don in ji daɗin nasarar zaɓaɓɓunka, don in sami rabo cikin farin cikin al’ummarka in kuma shiga gādonka cikin yin yabo.
לראות בטובת בחיריך-- לשמח בשמחת גויך להתהלל עם-נחלתך
6 Mun yi zunubi, kamar yadda kakanninmu suka yi; mun yi ba daidai ba muka kuma aikata mugunta.
חטאנו עם-אבותינו העוינו הרשענו
7 Sa’ad da kakanninmu suke a Masar, ba su damu da mu’ujizanka ba; ba su tuna yawan alheranka ba, suka kuma yi tayarwa a teku, Jan Teku.
אבותינו במצרים לא-השכילו נפלאותיך-- לא זכרו את-רב חסדיך וימרו על-ים בים-סוף
8 Duk da haka ya cece su saboda sunansa, don yă sanar da ikonsa mai girma.
ויושיעם למען שמו-- להודיע את-גבורתו
9 Ya tsawata wa Jan Teku, ya kuwa bushe; ya bi da su ta cikin zurfafa sai ka ce a hamada.
ויגער בים-סוף ויחרב ויוליכם בתהמות כמדבר
10 Ya cece su daga hannun maƙiyi; daga hannun abokin gāba ya fanshe su.
ויושיעם מיד שונא ויגאלם מיד אויב
11 Ruwaye suka rufe abokan gābansu; babu ko ɗaya da ya tsira.
ויכסו-מים צריהם אחד מהם לא נותר
12 Sa’an nan suka gaskata alkawarinsa suka kuma rera yabonsa.
ויאמינו בדבריו ישירו תהלתו
13 Amma nan da nan suka manta abin da ya yi ba su kuwa jira shawararsa ba.
מהרו שכחו מעשיו לא-חכו לעצתו
14 A cikin hamada suka bar sha’awarsu ta mamaye su a ƙasar da babu kome suka gwada Allah.
ויתאוו תאוה במדבר וינסו-אל בישימון
15 Sai ya ba su abin da suka roƙa, amma ya aika musu da muguwar cuta.
ויתן להם שאלתם וישלח רזון בנפשם
16 A sansani suka ji kishin Musa da kuma Haruna, wanda Ubangiji ya keɓe.
ויקנאו למשה במחנה לאהרן קדוש יהוה
17 Ƙasa ta buɗe ta haɗiye Datan ta binne iyalin Abiram.
תפתח-ארץ ותבלע דתן ותכס על-עדת אבירם
18 Wuta ta ƙuno a cikin mabiyansu; harshen wuta ya cinye mugaye.
ותבער-אש בעדתם להבה תלהט רשעים
19 A Horeb suka yi ɗan maraƙi suka yi wa gunkin zubi daga ƙarfe sujada.
יעשו-עגל בחרב וישתחוו למסכה
20 Suka sauke Ɗaukakarsu saboda siffar bijimi, wanda yake cin ciyawa.
וימירו את-כבודם בתבנית שור אכל עשב
21 Suka manta da Allahn da ya cece su, wanda ya aikata manyan abubuwa a Masar,
שכחו אל מושיעם-- עשה גדלות במצרים
22 mu’ujizai a ƙasar Ham ayyukan banrazana a Jan Teku.
נפלאות בארץ חם נוראות על-ים-סוף
23 Don haka ya ce zai hallaka su, amma Musa, zaɓaɓɓensa, ya yi godo a gabansa don yă kau da hasalarsa daga hallaka su.
ויאמר להשמידם לולי משה בחירו-- עמד בפרץ לפניו להשיב חמתו מהשחית
24 Sai suka rena ƙasa mai ni’ima; ba su gaskata alkawarinsa ba.
וימאסו בארץ חמדה לא-האמינו לדברו
25 Suka yi gunaguni a tentunansu ba su kuwa yi biyayya da Ubangiji ba.
וירגנו באהליהם לא שמעו בקול יהוה
26 Saboda haka ya rantse musu ya kuma ɗaga hannu cewa zai sa su mutu a cikin hamada,
וישא ידו להם-- להפיל אותם במדבר
27 ya sa zuriyarsu su mutu a cikin al’ummai ya kuma watsar da su cikin dukan ƙasashe.
ולהפיל זרעם בגוים ולזרותם בארצות
28 Suka haɗa kai da Ba’al-Feyor suka kuma ci hadayun da aka miƙa wa allolin da ba su da rai;
ויצמדו לבעל פעור ויאכלו זבחי מתים
29 suka tsokane Ubangiji ya yi fushi ta wurin mugayen ayyukansu, sai annoba ta ɓarke a cikinsu.
ויכעיסו במעלליהם ותפרץ-בם מגפה
30 Amma Finehas ya miƙe tsaye ya ɗauki mataki, sai annobar ta daina.
ויעמד פינחס ויפלל ותעצר המגפה
31 An ayana masa wannan a matsayin adalci har zamanai marar matuƙa masu zuwa.
ותחשב לו לצדקה לדר ודר עד-עולם
32 A ruwan Meriba suka ba Ubangiji fushi, sai wahala ta zo wa Musa saboda su;
ויקציפו על-מי מריבה וירע למשה בעבורם
33 saboda sun yi tayarwa a kan Ruhun Allah, har mugayen kalmomi suka fito daga leɓunan Musa.
כי-המרו את-רוחו ויבטא בשפתיו
34 Ba su hallakar da mutanen yadda Ubangiji ya umarce su ba,
לא-השמידו את-העמים-- אשר אמר יהוה להם
35 amma suka yi cuɗanya da al’ummai suka ɗauki al’adunsu.
ויתערבו בגוים וילמדו מעשיהם
36 Suka yi wa gumakansu sujada, waɗanda suka zama tarko gare su.
ויעבדו את-עצביהם ויהיו להם למוקש
37 Suka miƙa’ya’yansu maza hadaya’yan matansu kuma ga aljanu.
ויזבחו את-בניהם ואת-בנותיהם-- לשדים
38 Suka zub da jini marar laifi, jinin’ya’yansu maza da mata, waɗanda suka miƙa hadaya ga gumakan Kan’ana, ƙasar kuwa ta ƙazantu ta wurin jininsu.
וישפכו דם נקי דם-בניהם ובנותיהם-- אשר זבחו לעצבי כנען ותחנף הארץ בדמים
39 Suka ƙazantar da kansu ta wurin abin da suka yi; ta wurin ayyukansu suka yi karuwanci.
ויטמאו במעשיהם ויזנו במעלליהם
40 Saboda haka Ubangiji ya yi fushi da mutanensa ya ji ƙyamar gādonsa.
ויחר-אף יהוה בעמו ויתעב את-נחלתו
41 Ya miƙa su ga al’ummai, maƙiyansu kuma suka yi mulki a kansu.
ויתנם ביד-גוים וימשלו בהם שנאיהם
42 Abokan gābansu suka danne su suka sa su a ƙarƙashin ikonsu.
וילחצום אויביהם ויכנעו תחת ידם
43 Sau da yawa ya cece su, amma sun nace su yi tawaye suka kuma lalace cikin zunubinsu.
פעמים רבות יצילם והמה ימרו בעצתם וימכו בעונם
44 Amma ya lura da wahalarsu sa’ad da ya ji kukansu;
וירא בצר להם-- בשמעו את-רנתם
45 saboda su ya tuna da alkawarinsa kuma daga yawan ƙaunarsa ya ji tausayi.
ויזכר להם בריתו וינחם כרב חסדו
46 Ya sa aka ji tausayinsu a wurin dukan waɗanda suka kame su.
ויתן אותם לרחמים-- לפני כל-שוביהם
47 Ka cece mu, Ubangiji Allahnmu, ka kuma tattara mu daga al’ummai, don mu yi wa sunanka mai tsarki godiya mu kuma ɗaukaka cikin yabonka.
הושיענו יהוה אלהינו וקבצנו מן-הגוים להדות לשם קדשך להשתבח בתהלתך
48 Yabo ga Ubangiji, Allah na Isra’ila, daga madawwami zuwa madawwami. Bari dukan mutane su ce, “Amin!” Yabo ga Ubangiji.
ברוך יהוה אלהי ישראל מן-העולם ועד העולם-- ואמר כל-העם אמן הללו-יה

< Zabura 106 >