< Zabura 103 >
1 Ta Dawuda. Yabi Ubangiji, ya raina; dukan abin da yake cikin cikina, yabi sunansa mai tsarki.
2 Yabi Ubangiji, ya raina, kada kuma ka manta dukan alheransa,
3 wanda yake gafarta dukan zunubai yake kuma warkar da dukan cututtuka,
4 wanda ya fanshi ranka daga rami ya naɗa maka rawani da ƙauna da kuma tausayi,
5 Wanda ya ƙosar da kai da abubuwa masu kyau domin a sabunta ƙuruciyarka kamar na gaggafa.
6 Ubangiji yana aikata adalci da kuma gaskiya ga duk waɗanda aka danne.
7 Ya sanar da hanyoyinsa wa Musa, ayyukansa ga mutanen Isra’ila.
8 Ubangiji mai tausayi ne da kuma alheri, mai jinkirin fushi, cike da ƙauna.
9 Ba zai yi ta zargi ba ba kuwa zai yi ta jin fushi har abada ba;
10 ba ya yin da mu gwargwadon zunubanmu ko yă sāka mana bisa ga laifofinmu.
11 Gama kamar yadda sammai suke can bisa duniya, haka girmar ƙaunarsa yake wa masu tsoronsa;
12 kamar yadda gabas yake daga yamma, haka ya cire laifofinmu daga gare mu.
13 Kamar yadda mahaifi yake jin tausayin’ya’yansa, haka Ubangiji yake jin tausayin waɗanda suke tsoronsa;
14 gama ya san yadda aka yi mu, ya tuna cewa mu ƙura ne.
15 Game da mutum dai, kwanakinsa suna kamar ciyawa da suke haɓaka kamar fure a gona;
16 iska kan hura a kansa sai ya ɓace ba a kuwa sāke tuna da inda dā yake.
17 Amma daga madawwami zuwa madawwami ƙaunar Ubangiji tana tare da waɗanda suke tsoronsa, adalcinsa kuma tare da’ya’yansu,
18 tare da waɗanda suke kiyaye alkawarinsa suna kuma tuna su yi biyayya da farillansa.
19 Ubangiji ya kafa kursiyinsa a sama, masarautarsa kuwa na mulki a bisa duka.
20 Yabi Ubangiji, ku mala’ikunsa, ku jarumawa masu yi masa aiki, waɗanda suke yin biyayya da maganarsa.
21 Yabi Ubangiji, dukanku rundunarsa ta sama, ku bayinsa waɗanda kuke aikata nufinsa.
22 Yabi Ubangiji, dukanku ayyukansa ko’ina a mulkinsa. Yabi Ubangiji, ya raina.