< Zabura 102 >

1 Addu’ar mutum mai shan wahala. Sa’ad da ya rasa ƙarfi ya kuma yi makoki a gaban Ubangiji. Ka ji addu’ata, ya Ubangiji; bari kukata ta neman taimako ta zo gare ka.
תפלה לעני כי-יעטף-- ולפני יהוה ישפך שיחו ב יהוה שמעה תפלתי ושועתי אליך תבוא
2 Kada ka ɓoye fuskarka daga gare ni sa’ad da nake cikin damuwa. Ka juye kunnenka gare ni; sa’ad da na yi kira, ka amsa mini da sauri.
אל-תסתר פניך ממני-- ביום צר-לי הטה-אלי אזנך ביום אקרא מהר ענני
3 Gama kwanakina sun ɓace kamar hayaƙi; ƙasusuwana suna ƙuna kamar jan wuta.
כי-כלו בעשן ימי ועצמותי כמוקד נחרו
4 Zuciyata ta kamu da ciwo ta kuma bushe kamar ciyawa; na manta in ci abinci.
הוכה-כעשב ויבש לבי כי-שכחתי מאכל לחמי
5 Saboda nishina mai ƙarfi na rame na bar ƙasusuwa kawai.
מקול אנחתי-- דבקה עצמי לבשרי
6 Ni kamar mujiyar jeji ne, kamar mujiya a kufai.
דמיתי לקאת מדבר הייתי ככוס חרבות
7 Na kwanta a faɗake; na zama kamar tsuntsun da yake shi kaɗai a kan rufin ɗaki.
שקדתי ואהיה-- כצפור בודד על-גג
8 Dukan yini abokan gābana suna tsokanata; waɗanda suke mini ba’a suna amfani da sunana yă zama abin la’ana.
כל-היום חרפוני אויבי מהוללי בי נשבעו
9 Gama ina cin toka a matsayin abincina ina kuma gauraye abin sha nawa da hawaye
כי-אפר כלחם אכלתי ושקוי בבכי מסכתי
10 saboda fushinka mai girma, gama ka ɗaga ni sama ka yar a gefe.
מפני-זעמך וקצפך-- כי נשאתני ותשליכני
11 Kwanakina suna kamar inuwar yamma; na bushe kamar ciyawa.
ימי כצל נטוי ואני כעשב איבש
12 Amma kai, ya Ubangiji, kana zaune a kursiyinka har abada; sunan da ka yi zai dawwama a dukan zamanai.
ואתה יהוה לעולם תשב וזכרך לדר ודר
13 Za ka tashi ka kuma ji tausayin Sihiyona, gama lokaci ne na nuna alheri gare ta; ƙayyadadden lokacin ya zo.
אתה תקום תרחם ציון כי-עת לחננה כי-בא מועד
14 Gama duwatsunta suna da daraja ga bayinka; ƙurarta kawai kan sa su ji tausayi.
כי-רצו עבדיך את-אבניה ואת-עפרה יחננו
15 Al’ummai za su ji tsoron sunan Ubangiji, dukan sarakunan duniya za su girmama ɗaukakarka.
וייראו גוים את-שם יהוה וכל-מלכי הארץ את-כבודך
16 Gama Ubangiji zai sāke gina Sihiyona ya kuma bayyana a ɗaukakarsa.
כי-בנה יהוה ציון-- נראה בכבודו
17 Zai amsa addu’ar marasa ƙarfi; ba zai ƙyale roƙonsu ba.
פנה אל-תפלת הערער ולא-בזה את-תפלתם
18 Bari a rubuta wannan don tsara mai zuwa, cewa mutanen da ba a riga an halitta ba za su yabi Ubangiji,
תכתב זאת לדור אחרון ועם נברא יהלל-יה
19 “Ubangiji ya duba ƙasa daga wurinsa mai tsarki a bisa, daga sama ya hangi duniya,
כי-השקיף ממרום קדשו יהוה משמים אל-ארץ הביט
20 don yă ji nishe-nishen’yan kurkuku yă kuma saki waɗanda aka yanke musu hukuncin mutuwa.”
לשמע אנקת אסיר לפתח בני תמותה
21 Saboda haka za a furta sunan Ubangiji a Sihiyona yabonsa kuma a Urushalima
לספר בציון שם יהוה ותהלתו בירושלם
22 sa’ad da mutane da mulkoki suka tattaru don su yi wa Ubangiji sujada.
בהקבץ עמים יחדו וממלכות לעבד את-יהוה
23 Cikin rayuwata, ya karye ƙarfina; ya gajartar da kwanakina.
ענה בדרך כחו (כחי) קצר ימי
24 Sai na ce, “Kada ka ɗauke ni a tsakiyar kwanakina, ya Allah; shekarunka suna bi cikin dukan zamanai.
אמר--אלי אל תעלני בחצי ימי בדור דורים שנותיך
25 A farkon fari ka kafa tushen duniya, sammai kuma aikin hannuwanka ne.
לפנים הארץ יסדת ומעשה ידיך שמים
26 Za su hallaka, amma za ka ci gaba; duk za su tsufe kamar riga. Kamar riga za ka canja su za a kuwa zubar da su.
המה יאבדו-- ואתה תעמד וכלם כבגד יבלו כלבוש תחליפם ויחלפו
27 Amma kana nan yadda kake, kuma shekarunka ba za su taɓa ƙarewa ba.
ואתה-הוא ושנותיך לא יתמו
28 ’Ya’yan bayinka za su zauna a gabanka; zuriyarsu za su kahu a gabanka.”
בני-עבדיך ישכונו וזרעם לפניך יכון

< Zabura 102 >