< Zabura 101 >

1 Ta Dawuda. Zabura ce. Zan rera wa ƙauna da adalcinka; gare ka, ya Ubangiji, zan rera yabo. 2 Zan yi hankali ga yin rayuwa marar zargi, yaushe za ka zo gare ni? Zan bi da sha’anin gidana da zuciya marar abin zargi 3 Ba zan kafa a gaban idanuna 1 wani abu marar kyau ba. Na ƙi jinin ayyukan mutane marasa aminci; ba za su manne mini ba. 4 Mutane masu mugun zuciya za su nesa da ni; ba abin da zai haɗa ni da mugunta. 5 Duk wanda ya yi ɓatanci wa maƙwabcinsa a ɓoye shi za a kashe; duk mai renin wayo da mai girman kai, ba zan jure masa ba. 6 Idanuna za su kasance a kan amintattu a cikin ƙasar, don su zauna tare da ni; tafiyarsa ba ta da zargi zai yi mini hidima. 7 Babu mai ruɗun da zai zauna a gidana; babu mai ƙaryan da zai tsaya a gabana. 8 Kowace safiya zan rufe bakunan dukan mugaye a ƙasar; zan yanke kowane mai aikata mugunta daga birnin Ubangiji.

< Zabura 101 >