< Zabura 100 >

1 Zabura ce. Don yin godiya. Ku yi sowa don farin ciki ga Ubangiji, dukan duniya.
感謝の供え物のための歌 全地よ、主にむかって喜ばしき声をあげよ。
2 Yi wa Ubangiji sujada da murna; ku zo gabansa da waƙoƙin farin ciki.
喜びをもって主に仕えよ。歌いつつ、そのみ前にきたれ。
3 Ku san cewa Ubangiji shi ne Allah. Shi ne ya yi mu, mu kuwa nasa ne; mu mutanensa ne, tumakin makiyayarsa.
主こそ神であることを知れ。われらを造られたものは主であって、われらは主のものである。われらはその民、その牧の羊である。
4 Ku shiga ƙofofinsa da godiya filayen gidansa kuma da yabo; ku gode masa ku kuma yabi sunansa.
感謝しつつ、その門に入り、ほめたたえつつ、その大庭に入れ。主に感謝し、そのみ名をほめまつれ。
5 Gama Ubangiji yana da kyau kuma ƙaunarsa madawwamiya ce har abada; amincinsa na cin gaba a dukan zamanai.
主は恵みふかく、そのいつくしみはかぎりなく、そのまことはよろず代に及ぶからである。

< Zabura 100 >