< Karin Magana 9 >
1 Hikima ta gina gidanta; ta yi ginshiƙansa bakwai.
2 Ta shirya abincinta gauraye da ruwan inabinta; ta kuma shirya teburinta.
3 Ta aiki bayinta mata, tana kuma kira daga wurare masu tsayi na birnin.
4 “Bari dukan waɗanda suke marasa azanci su zo nan ciki!” Tana faɗa wa marasa hankali.
5 “Ku zo, ku ci abincina da ruwan inabin da na gauraye.
6 Ku bar hanyoyinku marasa hankali za ku kuwa rayu; yi tafiya a hanyar fahimi.
7 “Duk wanda ya yi wa mai ba’a gyara yana gayyatar zagi duk wanda ya tsawata wa mugu yakan gamu da cin mutunci.
8 Kada ka tsawata wa masu ba’a gama za su ƙi ka; ka tsawata wa mai hikima zai kuwa ƙaunace ka.
9 Ka koya wa mai hikima zai kuwa ƙara hikima; ka koya wa mai adalci zai kuwa ƙara koyonsa.
10 “Tsoron Ubangiji shi ne mafarin hikima, sanin Mai Tsarki kuwa fahimi ne.
11 Gama ta wurina kwanakinka za su yi yawa, za a kuwa ƙara wa ranka shekaru.
12 In kana da hikima, hikimarka za tă ba ka lada; in kai mai ba’a ne, kai kaɗai za ka sha wahala.”
13 Wawancin mace a bayyane yake; ba ta da ɗa’a kuma ba ta da sani.
14 Takan zauna a ƙofar gidanta, a wurin zama a wurin mafi tsayi na birni,
15 tana kira ga masu wucewa, waɗanda suke tafiya kai tsaye a hanyarsu.
16 “Bari dukan waɗanda suke marasa azanci su zo cikin nan!” Tana ce wa marasa hankali.
17 “Ruwan da aka sata ya fi daɗi; abincin da aka ci a ɓoye ya fi daɗi!”
18 Amma ba su san cewa matattu suna a can ba, cewa baƙinta suna a can cikin zurfin kabari ba. (Sheol )