< Karin Magana 8 >

1 Hikima ba ta yin kira ne? Fahimi ba ya tā da muryarsa ne?
הלא-חכמה תקרא ותבונה תתן קולה
2 A ƙwanƙoli a kan hanya, inda hanyoyi suka haɗu, ta ɗauki matsayinta;
בראש-מרמים עלי-דרך בית נתיבות נצבה
3 kusa da ƙofofin shiga cikin birni, a mashigai, ta tā da murya,
ליד-שערים לפי-קרת מבוא פתחים תרנה
4 “Gare ku, ya mutane, nake kira; na tā da muryata ga dukan’yan adam.
אליכם אישים אקרא וקולי אל-בני אדם
5 Ku da kuke marasa azanci, ku yi hankali; ku da kuke wawaye, ku nemi fahimi.
הבינו פתאים ערמה וכסילים הבינו לב
6 Ku saurara, gama ina da abubuwa masu darajan da zan faɗa; na buɗe leɓunana don in faɗa abin da yake daidai.
שמעו כי-נגידים אדבר ומפתח שפתי מישרים
7 Bakina yana magana abin da yake gaskiya, gama leɓunana sun ƙi mugunta.
כי-אמת יהגה חכי ותועבת שפתי רשע
8 Dukan kalmomin bakina suna da adalci; babu waninsu da ya karkace ko kuwa ƙarya ne.
בצדק כל-אמרי-פי אין בהם נפתל ועקש
9 Ga mai tunani dukansu daidai ne; ba su da laifi ga waɗanda suke da sani.
כלם נכחים למבין וישרים למצאי דעת
10 Ku zaɓi umarnina a maimakon azurfa, sani a maimakon zinariya zalla,
קחו-מוסרי ואל-כסף ודעת מחרוץ נבחר
11 gama hikima ta fi lu’ulu’ai daraja, kuma ba abin da kake sha’awa da za a kwatanta da ita.
כי-טובה חכמה מפנינים וכל-חפצים לא ישוו-בה
12 “Ni, hikima, ina zama tare da hankali; ina da sani da iya rarrabewa.
אני-חכמה שכנתי ערמה ודעת מזמות אמצא
13 Jin tsoron Ubangiji shi ne ƙin mugunta; ina ƙin girman kai da fariya, halin mugunta da kuma muguwar magana.
יראת יהוה שנאת-רע גאה וגאון ודרך רע ופי תהפכות שנאתי
14 Shawara da yin tunani mai kyau nawa ne; ina da fahimi da kuma iko.
לי-עצה ותושיה אני בינה לי גבורה
15 Ta wurina sarakuna suke mulki masu mulki kuma suke yin dokokin da suke da adalci;
בי מלכים ימלכו ורזנים יחקקו צדק
16 ta wurina sarakuna suke mulki, da kuma dukan manyan mutanen da suke mulkin duniya.
בי שרים ישרו ונדיבים כל-שפטי צדק
17 Ina ƙaunar waɗanda suke ƙaunata, kuma waɗanda suke nemana sukan same ni.
אני אהביה (אהבי) אהב ומשחרי ימצאנני
18 Tare da ni akwai wadata da girmamawa, dukiya da wadata masu dawwama.
עשר-וכבוד אתי הון עתק וצדקה
19 ’Ya’yan itacena sun fi zinariya zalla; amfanin gonar da nake bayar ya fi azurfa mafi kyau.
טוב פריי מחרוץ ומפז ותבואתי מכסף נבחר
20 Ina tafiya a hanyar adalci, a kan hanyoyin gaskiya,
בארח-צדקה אהלך בתוך נתיבות משפט
21 ina ba da wadata ga waɗanda suke ƙaunata ina sa wuraren ajiyarsu su cika.
להנחיל אהבי יש ואצרתיהם אמלא
22 “Ubangiji ya kawo ni a matsayi na farko na ayyukansa, kafin ayyukansa na tuntuni;
יהוה--קנני ראשית דרכו קדם מפעליו מאז
23 an naɗa ni tun fil azal, daga farko, kafin duniya ta kasance.
מעולם נסכתי מראש-- מקדמי-ארץ
24 Sa’ad da babu tekuna, aka haife ni, sa’ad da babu maɓulɓulai masu ruwa;
באין-תהמות חוללתי באין מעינות נכבדי-מים
25 kafin a kafa duwatsu a wurarensu, kafin tuddai ma, an haife ni,
בטרם הרים הטבעו לפני גבעות חוללתי
26 kafin ya yi duniya ko gonaki ko wata ƙurar duniya.
עד-לא עשה ארץ וחוצות וראש עפרות תבל
27 Ina nan sa’ad da ya kafa sammai a wurarensu, sa’ad da ya shata sararin sama a kan fuskar zurfafa,
בהכינו שמים שם אני בחקו חוג על-פני תהום
28 sa’ad da ya kafa gizagizai a bisa ya kuma kafa maɓulɓulan zurfafa daram,
באמצו שחקים ממעל בעזוז עינות תהום
29 sa’ad da ya ba wa teku iyakarsa domin kada ruwaye su zarce umarninsa, da kuma sa’ad da ya shata tussan duniya.
בשומו לים חקו ומים לא יעברו-פיו בחוקו מוסדי ארץ
30 A lokacin ni ne mai tsara abubuwa a gefensa. Na cika da murna kowace rana, kullum ina farin ciki a gabansa,
ואהיה אצלו אמון ואהיה שעשועים יום יום משחקת לפניו בכל-עת
31 ina farin ciki da dukan duniyarsa ina murna da’yan adam.
משחקת בתבל ארצו ושעשעי את-בני אדם
32 “Yanzu fa,’ya’yana, ku saurare ni; masu albarka ne waɗanda suke kiyaye hanyoyina.
ועתה בנים שמעו-לי ואשרי דרכי ישמרו
33 Ku saurari umarnina ku kuma zama masu hikima; kada ku ƙyale ta.
שמעו מוסר וחכמו ואל-תפרעו
34 Mai albarka ne wanda ya saurare ni; yana tsaro kullum a ƙofofina, yana jira a ƙofar shigata.
אשרי אדם שמע-לי לשקד על-דלתתי יום יום--לשמר מזוזת פתחי
35 Gama duk wanda ya same ni ya sami rai zai kuma sami tagomashi daga Ubangiji.
כי מצאי מצאי (מצא) חיים ויפק רצון מיהוה
36 Amma duk wanda ya kāsa samuna ya cuci kansa; dukan waɗanda suke ƙina suna ƙaunar mutuwa ke nan.”
וחטאי חמס נפשו כל-משנאי אהבו מות

< Karin Magana 8 >