< Karin Magana 6 >

1 Ɗana, in ka shirya tsaya wa maƙwabcinka don yă karɓi bashi, in ka sa hannunka don ɗaukar lamunin wani,
בני אם-ערבת לרעך תקעת לזר כפיך
2 in maganarka ta taɓa kama ka, ko kalmomin bakinka sun zama maka tarko,
נוקשת באמרי-פיך נלכדת באמרי-פיך
3 to, sai ka yi haka, ɗana don ka’yantar da kanka; da yake ka shiga hannuwan maƙwabcinka, ka tafi ka ƙasƙantar da kanka; ka roƙi maƙwabcinka!
עשה זאת אפוא בני והנצל-- כי באת בכף-רעך לך התרפס ורהב רעיך
4 Ka hana kanka barci, ko gyangyaɗi a idanunka ma.
אל-תתן שנה לעיניך ותנומה לעפעפיך
5 Ka’yantar da kanka, kamar barewa daga hannun mai farauta, kamar tsuntsu daga tarkon mai kafa tarko.
הנצל כצבי מיד וכצפור מיד יקוש
6 Ku tafi wurin kyashi, ku ragwaye; ku lura da hanyoyinsa ku zama masu hikima!
לך-אל-נמלה עצל ראה דרכיה וחכם
7 Ba shi da jagora ba shugaba ko mai mulki,
אשר אין-לה קצין-- שטר ומשל
8 duk da haka yakan yi tanade-tanadensa da rani ya kuma tattara abincinsa a lokacin girbi.
תכין בקיץ לחמה אגרה בקציר מאכלה
9 Har yaushe za ku kwanta a can, ku ragwaye? Yaushe za ku farka daga barcinku?
עד-מתי עצל תשכב מתי תקום משנתך
10 Ɗan barci, ɗan gyangyaɗi, ɗan naɗin hannuwa don a huta,
מעט שנות מעט תנומות מעט חבק ידים לשכב
11 talauci kuwa zai zo kamar’yan hari rashi kuma kamar ɗan fashi.
ובא-כמהלך ראשך ומחסרך כאיש מגן
12 Sakare da mutumin banza wanda yana yawo da magana banza a baki,
אדם בליעל איש און הולך עקשות פה
13 wanda yake ƙyifce da ido, yana yi alama da ƙafafunsa yana kuma nuni da yatsotsinsa,
קרץ בעינו מלל ברגלו מרה באצבעתיו
14 wanda yake ƙulla mugunta da ruɗu a cikin zuciyarsa, kullum yana tā-da-na-zaune-tsaye
תהפכות בלבו--חרש רע בכל-עת מדנים (מדינים) ישלח
15 Saboda haka masifa za tă fāɗa farat ɗaya; za a hallaka shi nan da nan, ba makawa.
על-כן--פתאם יבוא אידו פתע ישבר ואין מרפא
16 Akwai abubuwa shida da Ubangiji ya ƙi, abubuwa bakwai da suke abin ƙyama gare shi,
שש-הנה שנא יהוה ושבע תועבות (תועבת) נפשו
17 duban reni, harshe mai ƙarya, hannuwa masu zub da jinin marar laifi,
עינים רמות לשון שקר וידים שפכות דם-נקי
18 zuciyar da take ƙulla mugayen dabaru, ƙafafun da suke sauri zuwa aikata mugunta,
לב--חרש מחשבות און רגלים ממהרות לרוץ לרעה
19 mai shaidar ƙarya wanda yake zuba ƙarairayi, da kuma mutumin da yake tā-da-na-zaune-tsaye a cikin’yan’uwa.
יפיח כזבים עד שקר ומשלח מדנים בין אחים
20 Ɗana, ka kiyaye umarnan mahaifinka kada kuma ka ƙyale koyarwar mahaifiyarka.
נצר בני מצות אביך ואל-תטש תורת אמך
21 Ka ɗaura su a zuciyarka har abada; ka ɗaura su kewaye da wuyanka.
קשרם על-לבך תמיד ענדם על-גרגרתך
22 Sa’ad da kake tafiya, za su bishe ka; sa’ad da kake barci, za su lura da kai; sa’ad da ka farka, za su yi maka magana.
בהתהלכך תנחה אתך-- בשכבך תשמר עליך והקיצות היא תשיחך
23 Gama waɗannan umarnai fitila ne, wannan koyarwa haske ne, kuma gyare-gyaren horo hanyar rayuwa ce,
כי נר מצוה ותורה אור ודרך חיים תוכחות מוסר
24 suna kiyaye ka daga mace marar ɗa’a daga sulɓin harshen mace marar aminci.
לשמרך מאשת רע מחלקת לשון נכריה
25 Kada ka yi sha’awarta a cikin zuciyarka kada ka bar ta tă ɗauki hankalinka da idanunta.
אל-תחמד יפיה בלבבך ואל-תקחך בעפעפיה
26 Gama karuwa takan mai da kai kamar burodin kyauta, mazinaciya kuma takan farauci ranka.
כי בעד-אשה זונה עד-ככר-לחם ואשת איש-- נפש יקרה תצוד
27 Mutum zai iya ɗiba wuta ya zuba a cinyarsa ba tare da rigunansa sun ƙone ba?
היחתה איש אש בחיקו ובגדיו לא תשרפנה
28 Mutum zai iya yin tafi a garwashi wuta mai zafi ba tare da ƙafafunsa sun ƙone ba?
אם-יהלך איש על-הגחלים ורגליו לא תכוינה
29 Haka yake da wanda ya kwana da matar wani; babu wanda ya taɓa ta da zai tafi babu hukunci.
כן--הבא אל-אשת רעהו לא-ינקה כל-הנגע בה
30 Mutane ba sa ƙyale ɓarawo in ya yi sata don yă ƙosar da yunwarsa sa’ad da yake jin yunwa.
לא-יבוזו לגנב כי יגנוב-- למלא נפשו כי ירעב
31 Duk da haka in aka kama shi, dole yă biya sau bakwai ko da yake abin zai ci dukan arzikin gidansa.
ונמצא ישלם שבעתים את-כל-הון ביתו יתן
32 Amma mutumin da ya yi zina ba shi da hankali; duk wanda ya yi haka yana hallaka kansa ne.
נאף אשה חסר-לב משחית נפשו הוא יעשנה
33 Dūka da kunya ne za su zama rabonsa, kuma kunyarsa za tă dawwama.
נגע-וקלון ימצא וחרפתו לא תמחה
34 Gama kishi kan tā da hasalar miji, kuma ba zai ji tausayi ba sa’ad da yake ramawa.
כי-קנאה חמת-גבר ולא-יחמול ביום נקם
35 Ba zai karɓi duk wata biya ba; zai ƙi cin hanci, kome yawansu.
לא-ישא פני כל-כפר ולא-יאבה כי תרבה-שחד

< Karin Magana 6 >