< Karin Magana 5 >

1 Ɗana, ka mai da hankali ga hikimata ka saurara da kyau ga kalmomin basirata,
בני לחכמתי הקשיבה לתבונתי הט-אזנך
2 don ka ci gaba da yin kome daidai leɓunanka za su adana sani.
לשמר מזמות ודעת שפתיך ינצרו
3 Gama leɓunan mazinaciya na ɗigan zuma, maganarta tana da sulɓi fiye da mai;
כי נפת תטפנה שפתי זרה וחלק משמן חכה
4 amma a ƙarshe tana da ɗaci kamar tafashiya, mai ci kamar takobi mai kaifi biyu.
ואחריתה מרה כלענה חדה כחרב פיות
5 Ƙafafunta na kaiwa ga mutuwa; sawunta na jagora kai tsaye zuwa kabari. (Sheol h7585)
רגליה ירדות מות שאול צעדיה יתמכו (Sheol h7585)
6 Ba ta wani tunanin rayuwa; hanyoyinta karkatacce ne, amma ba tă sani ba.
ארח חיים פן-תפלס נעו מעגלתיה לא תדע
7 Yanzu fa,’ya’yana, ku saurare ni; kada ku juye daga abin da nake faɗa.
ועתה בנים שמעו-לי ואל-תסורו מאמרי-פי
8 Ku yi nesa da hanyarta, kana ku je kusa da ƙofar gidanta,
הרחק מעליה דרכך ואל-תקרב אל-פתח ביתה
9 don kada ku ba da ƙarfi mafi kyau ga waɗansu da kuma shekarunku ga wani marar imani,
פן-תתן לאחרים הודך ושנתיך לאכזרי
10 don kada baƙi su yi biki a kan dukiyarku wahalarku ta azurta gidan wani mutum dabam.
פן-ישבעו זרים כחך ועצביך בבית נכרי
11 A ƙarshen rayuwarku za ku yi ta nishi, sa’ad da namanku da jikinku suka zagwanye.
ונהמת באחריתך בכלות בשרך ושארך
12 Za ku ce, “Me ya sa na ƙi horo! Me ya sa zuciyata ta ƙi gyara!
ואמרת--איך שנאתי מוסר ותוכחת נאץ לבי
13 Ban yi biyayya da malamaina ba ko in saurari masu koyar da ni.
ולא-שמעתי בקול מורי ולמלמדי לא-הטיתי אזני
14 Na zo gab da hallaka gaba ɗaya a tsakiyar dukan taron.”
כמעט הייתי בכל-רע-- בתוך קהל ועדה
15 Ku sha ruwa daga tankinku, ruwa mai gudu daga rijiyarku.
שתה-מים מבורך ונזלים מתוך בארך
16 In maɓulɓulanku suka cika suna malala har waje, rafuffukan ruwanku a dandalin jama’a?
יפוצו מעינתיך חוצה ברחבות פלגי-מים
17 Bari su zama naka kaɗai, don kada ka raba da baƙi.
יהיו-לך לבדך ואין לזרים אתך
18 Bari maɓulɓulanka ya zama mai albarka, bari kuma ka yi farin ciki da matar ƙuruciyarka.
יהי-מקורך ברוך ושמח מאשת נעורך
19 Ƙaunatacciyar mariri, barewa mai kyan gani, bari mamanta su ishe ka kullum, bari ƙaunarta ta ɗauke hankalinka kullum.
אילת אהבים ויעלת-חן דדיה ירוך בכל-עת באהבתה תשגה תמיד
20 Ɗana, me ya sa za ka bari mazinaciya ta ɗauke maka hankali? Don me za ka rungume matar wani?
ולמה תשגה בני בזרה ותחבק חק נכריה
21 Gama hanyar mutum a bayyane take a gaban Ubangiji, yana kuma lura da dukan hanyoyinsa.
כי נכח עיני יהוה--דרכי-איש וכל-מעגלתיו מפלס
22 Ayyukan mugunta na mugun mutum tarko ne gare shi; igiyoyin zunubinsa za su daure shi kankan.
עוונתיו--ילכדנו את-הרשע ובחבלי חטאתו יתמך
23 Zai mutu saboda rashin ɗa’a yawan wawancinsa zai sa yă kauce.
הוא--ימות באין מוסר וברב אולתו ישגה

< Karin Magana 5 >