< Karin Magana 4 >
1 Ku saurara’ya’yana ga koyarwar mahaifinku; ku mai da hankali, ku sami fahimi.
2 Ina ba ku sahihiyar koyarwa, saboda haka kada ku ƙyale koyarwata.
3 Sa’ad da nake yaro a gidan mahaifina, yaro kaɗai kuma na mahaifiyata,
4 ya koya mini ya ce, “Ka riƙe kalmomina da dukan zuciyarka; ka kiyaye umarnaina za ka kuwa rayu.
5 Ka nemi hikima, ka nemi fahimi; kada ka manta da kalmomina ko ka kauce daga gare su.
6 Kada ka ƙyale hikima, za tă kuwa tsare ka; ka ƙaunace ta, za tă kuwa lura da kai.
7 Hikima ce mafi girma duka; saboda haka ka nemi hikima. Ko da za tă ci duk abin da kake da shi, ka dai nemi fahimi.
8 Ka ƙaunace ta, za tă ɗaukaka ka; ka rungume ta, za tă kuwa girmama ka.
9 Za tă zama kayan ado da za su inganta kanka tă kuma zamar maka rawanin ɗaukaka.”
10 Ka saurara, ɗana, ka yarda da abin da na faɗa, shekarun rayuwarka kuwa za su zama masu yawa.
11 Na bishe ka a hanyar hikima na kuma jagorance ka a miƙaƙƙun hanyoyi.
12 Sa’ad da kake tafiya, ba abin da zai sa ka tuntuɓe; sa’ad da kake gudu, ba za ka fāɗi ba.
13 Ka riƙe umarni, kada ka bari yă kuɓuce; ka tsare shi sosai, gama ranka ne.
14 Kada ka sa ƙafa a kan hanyar mugaye kada ka bi gurbin mugaye.
15 Ka guji mugunta, kada ka yi tafiya a kanta; juya daga gare ta ka yi tafiyarka.
16 Mugaye ba sa iya barci, sai sun aikata mugunta; ba su barci sai sun cuci wani.
17 Mugunta da ta’adi kamar ci da sha suke a gare su.
18 Hanyar adali kamar fitowar rana ce, sai ƙara haske take yi, har ta kai tsaka.
19 Amma hanyar mugaye kamar zurfin duhu ne; ba sa sanin abin da ya sa suke tuntuɓe.
20 Ɗana, ka kula da abin da nake faɗa, ka saurara sosai ga kalmomina.
21 Kada ka bari su rabu da kai, ka kiyaye su a cikin zuciyarka;
22 gama rai ne ga waɗanda suke nemansu da kuma lafiya ga dukan jikin mutum.
23 Fiye da kome duka, ka tsare zuciyarka, gama maɓulɓulan ruwan rijiyar rai ne.
24 Ka kau da muguwar magana daga bakinka; ka yi nesa da magana marar kyau daga leɓunanka.
25 Bari idanunka su dubi gaba sosai, ka kafa idanunka kai tsaye a gabanka.
26 Ka san inda ƙafafunka suke takawa ka bi hanyoyin da suke daram kawai.
27 Kada ka kauce dama ko hagu; ka kiyaye ƙafarka daga mugunta.