< Karin Magana 3 >
1 Ɗana, kada ka manta da koyarwata, amma ka kiyaye umarnaina a cikin zuciyarka,
2 gama za su ƙara maka tsawon rai da shekaru masu yawa su kuma kawo maka wadata.
3 Kada ka bar ƙauna da aminci su rabu da kai; ka ɗaura su kewaye da wuyanka, ka rubuta su a allon zuciyarka.
4 Sa’an nan za ka sami tagomashi da kuma suna mai kyau a gaban Allah da kuma a gaban mutane.
5 Ka dogara ga Ubangiji da dukan zuciyarka kada kuma ka dangana ga ganewarka;
6 cikin dukan hanyoyinka ka amince da shi, zai kuwa sa hanyoyinka su miƙe.
7 Kada ka zama mai hikima a ganinka; ka ji tsoron Ubangiji ka kuma guji mugunta.
8 Wannan zai ba wa jikinka lafiya yă kuma adana ƙasusuwanka.
9 Ka girmama Ubangiji da dukan dukiyarka, ta wurin miƙa masa nunan fari na dukan amfanin gonarka;
10 ta haka rumbunanka za su cika har su zuba, randunanka kuma su cika har baki da sabon ruwan inabi.
11 Ɗana, kada ka rena horon Ubangiji kada kuma ka ƙi tsawatawarsa,
12 domin Ubangiji yakan hori waɗanda yake ƙauna, kamar yadda mahaifi yake yin wa ɗa da yake fariya da shi.
13 Mai albarka ne mutumin da ya sami hikima, mutumin da ya sami fahimi,
14 gama ta fi azurfa riba tana kuma da amfani fiye da zinariya.
15 Ta fi lu’ulu’u daraja; ba a kwatanta abin da ka fi sha’awa da ita.
16 Tsawon rai yana a cikin hannunta na dama; a hannunta na hagu kuwa akwai arziki da bangirma.
17 Hanyoyinta hanyoyi ne masu daɗi, dukan hanyoyinta kuma salama ne.
18 Ita itacen rai ne ga waɗanda suka rungume ta; waɗanda suke riƙe da ta za su zama masu albarka.
19 Ta wurin hikima Ubangiji ya kafa harsashin duniya, ta wurin fahimi ya shirya sammai inda suke;
20 ta wurin sani aka rarraba zurfafa, gizagizai kuma suka zubo raɓa.
21 Ɗana, ka riƙe sahihiyar shari’a da kuma basira, kada ka bar su su rabu da kai;
22 za su zama rai a gare ka, abin adon da zai gyara wuyanka.
23 Sa’an nan za ka bi hanyarka lafiya, ƙafarka kuwa ba zai yi tuntuɓe ba;
24 sa’ad da ka kwanta, ba za ka ji tsoro ba; sa’ad da ka kwanta, barci zai yi maka daɗi.
25 Kada ka ji tsoron masifar da za tă faru farat ɗaya ko lalacin da yakan auka wa mugaye,
26 gama Ubangiji zai zama ƙarfin halinka zai kuwa kiyaye ƙafarka daga fāɗawa a tarko.
27 Kada ka ƙi yin alheri ga duk wanda ya dace, sa’ad da kana iya yin haka.
28 Kada ka ce wa maƙwabcinka “Ka yă dakata sai gobe,” idan kana iya taimakonsa yanzu.
29 Kada ka shirya kome da zai cuci maƙwabcinka, wanda yake zama da aminci kusa da kai.
30 Kada ka zargi mutum ba dalili, sa’ad da bai yi laifi ba.
31 Kada ka ji kishin mai tā-da-na-zaune-tsaye ko ka yi sha’awar aikata ayyukansu.
32 Gama Ubangiji yana ƙyama mai aikata mugunta amma yakan rungumi adalin da ya amince da shi.
33 La’anar Ubangiji tana a gidan mugaye, amma yakan albarkaci gidan adali.
34 Yakan yi wa masu girman kai ba’a amma yakan yi wa mai sauƙinkai alheri.
35 Masu hikima sukan sami kyakkyawan suna, amma wawaye sukan ƙara wa kansu shan kunya.