< Karin Magana 29 >
1 Mutumin da ya ci gaba da taurinkai bayan an kwaɓe shi ba da daɗewa ba zai hallaka ba makawa.
κρείσσων ἀνὴρ ἐλέγχων ἀνδρὸς σκληροτραχήλου ἐξαπίνης γὰρ φλεγομένου αὐτοῦ οὐκ ἔστιν ἴασις
2 Sa’ad da masu adalci suke cin nasara, mutane kan yi farin ciki sa’ad da mugaye suke mulki, mutane kan yi nishi.
ἐγκωμιαζομένων δικαίων εὐφρανθήσονται λαοί ἀρχόντων δὲ ἀσεβῶν στένουσιν ἄνδρες
3 Duk mai ƙaunar hikima kan kawo wa mahaifinsa farin ciki, amma wanda yake ma’amala da karuwai kan lalatar da dukiyarsa.
ἀνδρὸς φιλοῦντος σοφίαν εὐφραίνεται πατὴρ αὐτοῦ ὃς δὲ ποιμαίνει πόρνας ἀπολεῖ πλοῦτον
4 Ta wurin yin adalci sarki kan sa ƙasa tă yi ƙarƙo amma duk mai haɗama don cin hanci kan rushe ƙasar.
βασιλεὺς δίκαιος ἀνίστησιν χώραν ἀνὴρ δὲ παράνομος κατασκάπτει
5 Duk wanda yake wa maƙwabcinsa daɗin baki yana sa wa ƙafafunsa tarko ne.
ὃς παρασκευάζεται ἐπὶ πρόσωπον τοῦ ἑαυτοῦ φίλου δίκτυον περιβάλλει αὐτὸ τοῖς ἑαυτοῦ ποσίν
6 Mugun mutum tarko ne ta wurin zunubinsa, amma mai adalci zai iya rera ya kuma yi murna.
ἁμαρτάνοντι ἀνδρὶ μεγάλη παγίς δίκαιος δὲ ἐν χαρᾷ καὶ ἐν εὐφροσύνῃ ἔσται
7 Masu adalci sun damu game da adalci don talakawa, amma mugaye ba su da wannan damuwa.
ἐπίσταται δίκαιος κρίνειν πενιχροῖς ὁ δὲ ἀσεβὴς οὐ συνήσει γνῶσιν καὶ πτωχῷ οὐχ ὑπάρχει νοῦς ἐπιγνώμων
8 Masu ba’a kan kuta faɗa a birni, amma masu hikima sukan kwantar da fushi.
ἄνδρες λοιμοὶ ἐξέκαυσαν πόλιν σοφοὶ δὲ ἀπέστρεψαν ὀργήν
9 In mai hikima ya je wurin shari’a da wawa, wawa kan yi ta fushi yana ta dariya, ba kuwa za a sami salama ba.
ἀνὴρ σοφὸς κρίνει ἔθνη ἀνὴρ δὲ φαῦλος ὀργιζόμενος καταγελᾶται καὶ οὐ καταπτήσσει
10 Masu kisankai sukan ƙi mutum mai mutunci su kuma nema su kashe mai aikata gaskiya.
ἄνδρες αἱμάτων μέτοχοι μισήσουσιν ὅσιον οἱ δὲ εὐθεῖς ἐκζητήσουσιν ψυχὴν αὐτοῦ
11 Wawa yakan nuna fushinsa a fili, amma mai hikima kan kanne fushinsa.
ὅλον τὸν θυμὸν αὐτοῦ ἐκφέρει ἄφρων σοφὸς δὲ ταμιεύεται κατὰ μέρος
12 In mai mulki yana sauraran ƙarairayi, dukan ma’aikatansa za su zama mugaye.
βασιλέως ὑπακούοντος λόγον ἄδικον πάντες οἱ ὑπ’ αὐτὸν παράνομοι
13 Matalauci da azzalumi suna da wannan abu ɗaya. Ubangiji ne yake ba dukansu gani.
δανιστοῦ καὶ χρεοφειλέτου ἀλλήλοις συνελθόντων ἐπισκοπὴν ποιεῖται ἀμφοτέρων ὁ κύριος
14 In sarki yana hukunta talakawa da adalci kursiyinsa kullum zai kasance lafiya.
βασιλέως ἐν ἀληθείᾳ κρίνοντος πτωχοὺς ὁ θρόνος αὐτοῦ εἰς μαρτύριον κατασταθήσεται
15 Sandar gyara kan ba da hikima, amma yaron da aka bari ba horo kan jawo kunya ga mahaifiyarsa.
πληγαὶ καὶ ἔλεγχοι διδόασιν σοφίαν παῖς δὲ πλανώμενος αἰσχύνει γονεῖς αὐτοῦ
16 Sa’ad da mugaye suke cin nasara, haka zunubi zai yi ta ƙaruwa, amma masu adalci za su ga fāɗuwar waɗannan mutane.
πολλῶν ὄντων ἀσεβῶν πολλαὶ γίνονται ἁμαρτίαι οἱ δὲ δίκαιοι ἐκείνων πιπτόντων κατάφοβοι γίνονται
17 Ka hori ɗanka, zai kuwa ba ka salama; zai ba ka farin cikin da kake so.
παίδευε υἱόν σου καὶ ἀναπαύσει σε καὶ δώσει κόσμον τῇ ψυχῇ σου
18 Inda ba wahayi, mutane kan kangare; amma masu albarka ne waɗanda suke kiyaye doka.
οὐ μὴ ὑπάρξῃ ἐξηγητὴς ἔθνει παρανόμῳ ὁ δὲ φυλάσσων τὸν νόμον μακαριστός
19 Ba a yi wa bawa gyara ta wurin magana kawai; ko da ya fahimta ma, ba zai kula ba.
λόγοις οὐ παιδευθήσεται οἰκέτης σκληρός ἐὰν γὰρ καὶ νοήσῃ ἀλλ’ οὐχ ὑπακούσεται
20 Ka ga mutum mai yin magana da garaje? To, gara a sa zuciya ga wawa da a sa zuciya gare shi.
ἐὰν ἴδῃς ἄνδρα ταχὺν ἐν λόγοις γίνωσκε ὅτι ἐλπίδα ἔχει μᾶλλον ἄφρων αὐτοῦ
21 In mutum ya yi wa bawansa shagwaɓa tun yana yaro, zai jawo baƙin ciki a ƙarshe.
ὃς κατασπαταλᾷ ἐκ παιδός οἰκέτης ἔσται ἔσχατον δὲ ὀδυνηθήσεται ἐφ’ ἑαυτῷ
22 Mutum mai cika fushi yakan tā da faɗa, mai zafin rai kuma kan yi zunubai masu yawa.
ἀνὴρ θυμώδης ὀρύσσει νεῖκος ἀνὴρ δὲ ὀργίλος ἐξώρυξεν ἁμαρτίας
23 Fariyar mutum kan jawo masa ƙasƙanci amma mai sauƙinkai kan sami girmamawa.
ὕβρις ἄνδρα ταπεινοῖ τοὺς δὲ ταπεινόφρονας ἐρείδει δόξῃ κύριος
24 Duk wanda yake abokin ɓarawo abokin gāban kansa ne; yana jin sa yana ta rantsuwa, amma bai isa ya ce kome ba.
ὃς μερίζεται κλέπτῃ μισεῖ τὴν ἑαυτοῦ ψυχήν ἐὰν δὲ ὅρκου προτεθέντος ἀκούσαντες μὴ ἀναγγείλωσιν
25 Jin tsoron mutum tarko ne, amma duk wanda ya dogara ga Ubangiji zai zauna lafiya.
φοβηθέντες καὶ αἰσχυνθέντες ἀνθρώπους ὑπεσκελίσθησαν ὁ δὲ πεποιθὼς ἐπὶ κύριον εὐφρανθήσεται ἀσέβεια ἀνδρὶ δίδωσιν σφάλμα ὃς δὲ πέποιθεν ἐπὶ τῷ δεσπότῃ σωθήσεται
26 Mutane sukan nemi samun farin jini daga wurin sarki, amma daga wurin Ubangiji ne mutum kan sami adalci.
πολλοὶ θεραπεύουσιν πρόσωπα ἡγουμένων παρὰ δὲ κυρίου γίνεται τὸ δίκαιον ἀνδρί
27 Masu adalci suna ƙyamar masu rashin gaskiya; mugaye sukan yi ƙyamar masu aikata gaskiya.
βδέλυγμα δικαίοις ἀνὴρ ἄδικος βδέλυγμα δὲ ἀνόμῳ κατευθύνουσα ὁδός