< Karin Magana 28 >
1 Mugu yakan gudu ko babu wanda yake korarsa, amma adalai suna da ƙarfin hali kamar zaki.
2 Sa’ad da ƙasa ta yi tayarwa, takan kasance da masu mulki da yawa, amma mai fahimi da sani kan mai da zaman lafiya.
3 Mai mulkin da ya danne talakawa yana kama da ruwan saman da ya lalatar da hatsi.
4 Duk waɗanda ba sa bin doka yabon mugaye suke yi, amma waɗanda suke yin biyayya da doka suna gāba da mugaye ke nan.
5 Mugaye ba su san gaskiya ba, amma waɗanda suke neman Ubangiji sun santa sosai.
6 Gara matalauci wanda yake tafiya babu abin zargi da mai arziki wanda hanyoyinsa mugaye ne.
7 Duk wanda ya kiyaye doka ɗa ne mai la’akari, amma wanda yake abokantaka da masu zari yakan jawo wa mahaifinsa kunya.
8 Duk wanda ya tara dukiyarsa ta wurin ba da bashi da ruwan da ya wuce misali yana tara wa wani ne wanda zai yi wa talakawa alheri.
9 In wani ya yi kunnuwa ƙashi ga doka ko addu’arsa ma abar ƙyama ce.
10 Duk wanda ya jagorance masu aikata gaskiya a hanyar mugunta zai fāɗa cikin tarkonsa amma marasa abin zargi za su sami gādo mai kyau.
11 Mai arziki zai yi zato shi mai hikima ne a ganinsa, amma matalauci mai basira ya fi shi sanin abin da yake daidai.
12 Sa’ad da adalai suka yi nasara, kowa yakan yi biki; amma sa’ad da mugu ya samu shugabanci, mutane sukan yi ta ɓuya.
13 Duk wanda ya ɓoye zunubansa ba ya taɓa cin nasara, amma duk wanda ya furta ya kuma ƙi su yakan sami jinƙai.
14 Mai albarka ne mutumin da kullum yake jin tsoron Allah, amma duk wanda ya taurare zuciyarsa yakan shiga wahala.
15 Kamar rurin zaki ko sanɗar beyar haka mugun mutum mai mulki a kan mutane marasa ƙarfi yake.
16 Mugu mai mulki ba shi da azanci, amma duk wanda yake ƙin ƙazamar riba yakan yi tsawon rai.
17 Mutumin da laifin kisa ya yi ta damunsa zai zama mai gudu don tsoro har mutuwa; kada wani ya taimake shi.
18 Duk wanda ya yi tafiya marar abin zargi zai zauna lafiya, amma duk wanda hanyoyinsa mugaye ne zai fāɗi nan da nan.
19 Duk wanda ya nome gonarsa zai sami amfani a yalwace, amma duk wanda yake zaman banza zai zama matalauci a koyaushe.
20 Mutum mai aminci zai cika da albarka, amma duk mai son yin arziki dare ɗaya zai sha hukunci.
21 Nuna sonkai ba shi da kyau, duk da haka mutum zai aikata abin da ba daidai ba saboda’yar ƙaramar rashawa.
22 Mai rowa yana alla-alla ya yi arziki bai san cewa talauci ne ke jiransa ba.
23 Duk wanda ya tsawata wa wani mutum zai sami yabo a ƙarshe fiye da wanda yake mai daɗin baki.
24 Duk wanda ya yi wa mahaifin ko mahaifiyarsa sata ya kuma ce, “Ai, ba laifi ba ne” abokin mai hallakarwa ne shi.
25 Mai haɗama yakan jawo tā-da-na-zaune-tsaye, amma duk wanda ya dogara ga Ubangiji zai yi nasara.
26 Duk mai dogara ga kansa wawa ne, amma duk wanda yake tafiya da hikima zai zauna lafiya.
27 Duk wanda yake bayarwa ga matalauta ba zai rasa kome ba, amma duk wanda bai kula da su ba yana samu la’ana masu yawa.
28 Sa’ad da mugu ya samu shugabanci, mutane sukan yi ta ɓuya; amma sa’ad da mugu ya hallaka, adali kan ci gaba cikin arziki da lafiya.