< Karin Magana 27 >
1 Kada ka yi fariya a kan gobe gama ba san abin da ranar za tă kawo ba.
No te jactes del día de mañana, ya que no sabes qué dará de sí el día (siguiente).
2 Ka bar wani ya yabe ka, ba kai kanka ba; wani dabam, ba leɓunanka ba.
Alábete otro, y no tu boca; un extraño, y no tus labios.
3 Dutse yana da nauyi yashi kuma wahala ce, amma tsokanar wawa ta fi su duka nauyi.
Pesada es la piedra, y una carga la arena, pero más gravosa que ambas cosas es la ira del necio.
4 Fushi mugun abu ne mai hallakarwa, amma wa zai iya tsaya a gaban kishi?
Cruel es la cólera e impetuoso el furor; pero, ¿quién es capaz de suprimir los celos?
5 Gara tsawatawar da ake yi a fili da ƙaunar da ake yi a ɓoye.
Más vale una reprensión abierta que una amistad que no se manifiesta.
6 Za a iya amince da rauni daga aboki, amma abokin gāba ko da ya sumbace ka kada ka sake da shi!
Son sinceras las heridas hechas por quien ama, pero engañosos los besos del que odia.
7 Duk wanda ya ƙoshi da zuma, ba ya marmarinsa kuma amma wanda yake yunwa ko abin da yake da ɗaci ma zai ji shi da zaƙi.
El harto pisotea el panal, para el hambriento todo lo amargo es dulce.
8 Kamar tsuntsun da ya ɓace daga sheƙarsa haka yake da mutumin da ya bar gidansa.
Como ave que se aleja de su nido, así es el hombre que abandona su lugar.
9 Man shafawa mai ƙanshi da kuma turare kan faranta zuciya, gaisuwar amini kuma takan fito daga shawarar kirki.
Como perfumes e incienso deleitan el corazón, así el alma encuentra dulzura en el consejo de un amigo.
10 Kada ka manta da abokinka da kuma abokin mahaifinka, kuma kada ka tafi gidan ɗan’uwanka sa’ad da masifa ta same ka, gara ka je wurin maƙwabci na kusa da ka je wurin ɗan’uwan da yake da nisa.
No abandones a tu amigo, ni al amigo de tu padre, y en el día de tu dolor no vayas a la casa de tu hermano. Más vale vecino cercano que hermano lejano.
11 Ka zama mai hikima, ɗana, ka kuma faranta mini zuciya; zan iya amsa kowace irin suƙar da wani zai yi mini.
Sé sabio, hijo mío, y alegra mi corazón; para que pueda yo responder a quien me afrenta.
12 Mai basira kan hango hatsari ya kuma kauce, marar azanci zai yi ta kutsa kai ciki, daga baya ya yi da na sani.
El hombre cauto divisa el peligro y se esconde; el incauto sigue adelante y sufre el daño.
13 A karɓe rigunan wanda ya ɗauki lamunin baƙo; a riƙe shi jingina in ya yi shi don mace marar aminci.
Quítale el vestido, pues salió de fiador por otro, y tómale prenda para satisfacer a la mujer extraña.
14 In mutum ya albarkaci maƙwabcinsa da murya mai ƙarfi da sassafe, za a ɗauka shi a matsayin la’ana.
Bendecir al amigo a grandes voces y muy de mañana, es reputado como una maldición.
15 Mace mai fitina kamar ɗiɗɗigar ruwa take ba ƙaƙƙautawa;
Gotera continua en tiempo de lluvia, y mujer rencillosa, cosa igual;
16 hana ta yana kamar yin ƙoƙari tsai da iska ne ko yin ƙoƙarin cafke mai a tafin hannunka.
querer guardarla es guardar los vientos, y retener en la mano el aceite.
17 Kamar yadda ƙarfe kan wasa ƙarfe haka mutum kan koyi daga mutum.
Hierro con hierro se aguza; así un hombre aguza a otro.
18 Duk wanda ya lura da itacen ɓaure, zai ci’ya’yansa, kuma duk wanda ya lura da maigidansa za a girmama shi.
Quien cultiva una higuera comerá su fruto; quien cuida a su señor será honrado.
19 Kamar yadda ruwa kan nuna yadda fuska take, haka zuciyar mutum kan nuna irin mutumin.
Como en el agua rostro (corresponde) a rostro, así el corazón del hombre al hombre.
20 Mutuwa da Hallaka ba sa ƙoshi, haka idanun mutum ba sa ƙoshi da gani. (Sheol )
El scheol y el abismo no se sacian nunca; así tampoco los ojos del hombre. (Sheol )
21 Ana gwajin azurfa da kuma zinariya da wuta, amma akan gwada mutum ta wurin yabon da ya samu.
El crisol prueba la plata, la hornaza el oro; así le prueba al hombre la boca que le alaba.
22 Ko da ka daka wawa a turmi, kana daka shi kamar hatsi da taɓarya, ba za ka fid da wauta daga gare shi ba.
Aunque majares al necio en un mortero, como se maja el trigo con el pisón, no por eso se apartará de él su necedad.
23 Ka tabbata ka san lafiyar garken tumakinka, ka mai da hankali ga garken shanunka;
Conoce bien tus ovejas y cuida de tus rebaños,
24 domin dukiya ba ta dawwama har abada, ba a kuma kasance da rawani daga tsara zuwa tsara.
porque no duran siempre las riquezas, ni la corona de generación en generación.
25 Sa’ad da aka yanki ingirci sabon toho kuma ya bayyana aka kuma tattara ciyawa daga tuddai,
Brota el pasto, aparece la hierba y se recoge el heno de los montes;
26 gashin raguna za su tanada maka tufafi, za ka iya sayi gonaki masu kyau da kuɗin awaki.
entonces los corderos te darán el vestido, los cabritos el precio del campo,
27 Za ka kasance da madarar awaki mai yawa don ka ciyar da kanka da kuma iyalinka ka kuma inganta bayinka mata.
y las cabras leche en abundancia para tu alimento, para el sustento de tu casa y la vida de tus criadas.