< Karin Magana 26 >

1 Kamar ƙanƙara a rani ko ruwan sama a lokacin girbi, haka girmamawa bai dace da wawa ba.
כשלג בקיץ--וכמטר בקציר כן לא-נאוה לכסיל כבוד
2 Kamar gwara mai yawo ko alallaka mai firiya, haka yake da la’anar da ba tă dace tă kama ka ba take.
כצפור לנוד כדרור לעוף-- כן קללת חנם לא (לו) תבא
3 Bulala don doki, linzami don jaki, sanda kuma don bayan wawaye!
שוט לסוס מתג לחמור ושבט לגו כסילים
4 Kada ka amsa wa wawa bisa ga wautarsa, in ba haka ba kai kanka za ka zama kamar sa.
אל-תען כסיל כאולתו פן-תשוה-לו גם-אתה
5 Ka amsa wa wawa bisa ga wautarsa, in ba haka ba zai ga kansa mai hikima ne.
ענה כסיל כאולתו פן-יהיה חכם בעיניו
6 Kamar datsewar ƙafafun wani ko shan dafi haka yake da a aika da saƙo ta hannun wawa.
מקצה רגלים חמס שתה-- שלח דברים ביד-כסיל
7 Kamar ƙafafun gurgun da suka yi laƙwas haka karin magana yake a bakin wawa.
דליו שקים מפסח ומשל בפי כסילים
8 Kamar ɗaura dutse a majajjawa haka yake da girmama wawa.
כצרור אבן במרגמה-- כן-נותן לכסיל כבוד
9 Kamar suƙar ƙaya a hannun wanda ya bugu haka karin magana yake a bakin wawa.
חוח עלה ביד-שכור ומשל בפי כסילים
10 Kamar maharbi wanda yake jin wa kowa rauni haka yake da duk wanda ya yi hayan wawa ko wani mai wucewa.
רב מחולל-כל ושכר כסיל ושכר עברים
11 Kamar yadda kare kan koma ga amansa, haka wawa kan maimaita wautarsa.
ככלב שב על-קאו-- כסיל שונה באולתו
12 Gwamma riƙaƙƙen wawa da mutum mai ganin kansa mai hikima ne.
ראית--איש חכם בעיניו תקוה לכסיל ממנו
13 Rago yakan ce, “Akwai zaki a kan hanya, zaki mai faɗa yana yawo a tituna!”
אמר עצל שחל בדרך ארי בין הרחבות
14 Kamar yadda ƙofa kan juya a ƙyaurensa, haka rago yake jujjuya a gadonsa.
הדלת תסוב על-צירה ועצל על-מטתו
15 Rago kan sa hannunsa a kwano ba ya ma iya ɗaga shi ya kai bakinsa.
טמן עצל ידו בצלחת נלאה להשיבה אל-פיו
16 Rago yana gani yana da hikima fiye da mutane bakwai da suke ba da amsa da dalilai a kan ra’ayinsu.
חכם עצל בעיניו-- משבעה משיבי טעם
17 Kamar wani da ya kama kare a kunnuwa haka yake da mai wucewa da ya tsoma baki a faɗan da ba ruwansa.
מחזיק באזני-כלב-- עבר מתעבר על-ריב לא-לו
18 Kamar yadda mahaukaci yake harbin cukwimai ko kibiyoyi masu dafi
כמתלהלה הירה זקים-- חצים ומות
19 haka yake da mutumin da ya ruɗe maƙwabci sa’an nan ya ce, “Wasa ne kawai nake yi!”
כן-איש רמה את-רעהו ואמר הלא-משחק אני
20 In ba itace wuta takan mutu; haka kuma in ba mai gulma ba za a yi faɗa ba.
באפס עצים תכבה-אש ובאין נרגן ישתק מדון
21 Kamar yadda gawayi yake ga murhu, itace kuma ga wuta, haka mutum mai neman faɗa yake ga faɗa.
פחם לגחלים ועצים לאש ואיש מדונים (מדינים) לחרחר-ריב
22 Kalmomin mai gulma suna kama da burodi mai daɗi; sukan gangara can cikin cikin mutum.
דברי נרגן כמתלהמים והם ירדו חדרי-בטן
23 Kamar kaskon da aka dalaye da azurfar da ba a tace ba haka leɓuna masu mugun zuciya.
כסף סיגים מצפה על-חרש-- שפתים דלקים ולב-רע
24 Mai yin ƙiyayya yakan ɓoye kansa da maganar bakinsa, amma a cikin zuciyarsa yana cike da munafunci
בשפתו ינכר שונא ובקרבו ישית מרמה
25 Ko da jawabinsa ya ɗauki hankali, kada ka gaskata shi, gama abubuwa ƙyama guda bakwai sun cika zuciyarsa.
כי-יחנן קולו אל-תאמן-בו כי שבע תועבות בלבו
26 Wataƙila ya ɓoye ƙiyayyarsa da ƙarya, duk da haka za a tone muguntarsa a cikin taro.
תכסה שנאה במשאון תגלה רעתו בקהל
27 In mutum ya haƙa rami, shi zai fāɗi a ciki; in mutum ya mirgino dutse, dutsen zai mirgine a kansa.
כרה-שחת בה יפול וגולל אבן אליו תשוב
28 Harshe mai faɗin ƙarya yana ƙin waɗanda yake ɓata musu rai, daɗin baki kuma yakan aikata ɓarna.
לשון-שקר ישנא דכיו ופה חלק יעשה מדחה

< Karin Magana 26 >