< Karin Magana 24 >

1 Kada ka yi ƙyashin mugaye, kada ka yi sha’awar ƙungiyarsu;
אל תקנא באנשי רעה ואל תתאו להיות אתם׃
2 gama leɓunansu suna maganar tā-da-na-zaune-tsaye ne.
כי שד יהגה לבם ועמל שפתיהם תדברנה׃
3 Ta wurin hikima ce ake gina gida, kuma ta wurin fahimi ake kafa ta;
בחכמה יבנה בית ובתבונה יתכונן׃
4 ta wurin sani ɗakunanta sukan cika da kyawawan kayayyaki masu daraja.
ובדעת חדרים ימלאו כל הון יקר ונעים׃
5 Mutum mai hikima yana da iko sosai, kuma mutum mai sani yakan ƙaru da ƙarfi;
גבר חכם בעוז ואיש דעת מאמץ כח׃
6 don yin yaƙi kana bukatar bishewa, kuma don ka yi nasara kana bukatar mashawarta masu yawa.
כי בתחבלות תעשה לך מלחמה ותשועה ברב יועץ׃
7 Hikima ta yi wa wawa nisa ƙwarai a cikin taro a ƙofar gari ba shi da ta cewa.
ראמות לאויל חכמות בשער לא יפתח פיהו׃
8 Duk mai ƙulla mugunta za a ɗauka shi mai kuta hargitsi ne.
מחשב להרע לו בעל מזמות יקראו׃
9 Makircin wawa zunubi ne, mutane kuma sukan yi ƙyamar mai ba’a.
זמת אולת חטאת ותועבת לאדם לץ׃
10 In ba ka da ƙarfi a lokacin wahala, ka tabbatar kai marar ƙarfi ne sosai!
התרפית ביום צרה צר כחכה׃
11 Ka kuɓutar da waɗanda ake ja zuwa inda za a kashe su; ka riƙe waɗanda suke tangaɗi zuwa wajen yanka.
הצל לקחים למות ומטים להרג אם תחשוך׃
12 In kuka ce, “Ai, ba mu san wani abu a kai wannan ba,” shi da yake awon ba shi da zuciyar ganewa ne? Shi da yake tsare ranka bai sani ba ne? Ba zai sāka wa kowane mutum bisa ga abin da ya aikata ba?
כי תאמר הן לא ידענו זה הלא תכן לבות הוא יבין ונצר נפשך הוא ידע והשיב לאדם כפעלו׃
13 Ka sha zuma, ɗana, ka sha zuma gama tana da kyau; zuma daga kaki yana da zaƙi a harshenka.
אכל בני דבש כי טוב ונפת מתוק על חכך׃
14 Ka kuma san cewa hikima tana da zaƙi ga rai; in ka same ta, akwai sa zuciya ta nan gaba dominka, kuma sa zuciyarka ba za tă zama a banza ba.
כן דעה חכמה לנפשך אם מצאת ויש אחרית ותקותך לא תכרת׃
15 Kada ka kwanta kana fako kamar ɗan iska don ƙwace gidan adali, kada ka ƙwace masa wurin zama;
אל תארב רשע לנוה צדיק אל תשדד רבצו׃
16 gama ko da adali ya fāɗi sau bakwai, yakan tashi kuma, amma bala’i kan kwantar da mugaye.
כי שבע יפול צדיק וקם ורשעים יכשלו ברעה׃
17 Kada ka yi dariya sa’ad da abokin gāba ya fāɗi; sa’ad da ya yi tuntuɓe, kada ka yi farin ciki,
בנפל אויביך אל תשמח ובכשלו אל יגל לבך׃
18 in ba haka ba in Ubangiji ya gani ba zai amince ba ya kuma juye fushinsa daga gare shi.
פן יראה יהוה ורע בעיניו והשיב מעליו אפו׃
19 Kada ka ji tsoro saboda masu mugunta ko ka yi ƙyashin mugaye,
אל תתחר במרעים אל תקנא ברשעים׃
20 gama mugu ba shi da zuciya ta nan gaba, kuma fitilar mugaye za tă mutu.
כי לא תהיה אחרית לרע נר רשעים ידעך׃
21 Ka ji tsoron Ubangiji da kuma sarki, ɗana, kuma kada ka haɗa kai da masu tayarwa,
ירא את יהוה בני ומלך עם שונים אל תתערב׃
22 gama za a tura waɗannan biyu zuwa hallaka nan da nan, kuma wa ya sani irin bala’in da za su iya kawowa?
כי פתאם יקום אידם ופיד שניהם מי יודע׃
23 Waɗannan ma maganganun masu hikima ne, Nunan sonkai a shari’a ba shi da kyau.
גם אלה לחכמים הכר פנים במשפט בל טוב׃
24 Duk wanda ya ce wa mai laifi, “Ba ka da laifi”, mutane za su la’ance shi al’umma kuma za tă ce ba a san shi ba.
אמר לרשע צדיק אתה יקבהו עמים יזעמוהו לאמים׃
25 Amma zai zama da lafiya ga duk waɗanda suka hukunta masu laifi, kuma babban albarka zai zo a kansu.
ולמוכיחים ינעם ועליהם תבוא ברכת טוב׃
26 Amsa da take ta gaskiya tana kamar sumba a leɓuna.
שפתים ישק משיב דברים נכחים׃
27 Ka gama aikinka ka kuma shirya gonakinka; bayan haka, ka gina gidanka.
הכן בחוץ מלאכתך ועתדה בשדה לך אחר ובנית ביתך׃
28 Kada ka ba da shaida a kan maƙwabcinka ba tare da isashen dalili ba, ko ka yi amfani da leɓunanka ka yi ruɗu.
אל תהי עד חנם ברעך והפתית בשפתיך׃
29 Kada ka ce, “Zan yi masa kamar yadda ya yi mini; zan rama abin da wannan mutum ya yi mini.”
אל תאמר כאשר עשה לי כן אעשה לו אשיב לאיש כפעלו׃
30 Na wuce cikin gonar rago, na wuce cikin gonar inabin mutumin da ba shi da azanci;
על שדה איש עצל עברתי ועל כרם אדם חסר לב׃
31 ƙayayyuwa sun yi girma ko’ina, ciyayi sun rufe ƙasar, katangar duwatsu duk ta rushe.
והנה עלה כלו קמשנים כסו פניו חרלים וגדר אבניו נהרסה׃
32 Na yi tunani a zuciyata na kuwa koyi darasi daga abin da na gani.
ואחזה אנכי אשית לבי ראיתי לקחתי מוסר׃
33 Ɗan barci, ɗan gyangyaɗi, ɗan naɗin hannuwa don a huta,
מעט שנות מעט תנומות מעט חבק ידים לשכב׃
34 sai talauci ya shigo maka kamar’yan fashi rashi kuma ya zo maka kamar mai hari.
ובא מתהלך רישך ומחסריך כאיש מגן׃

< Karin Magana 24 >