< Karin Magana 23 >
1 Sa’ad da ka zauna domin cin abinci da mai mulki, ka lura sosai da abin da yake gabanka,
When you sit down to dine with a ruler, consider carefully what is set before you,
2 ka kuma sa wuƙa a maƙogwaronka in kai mai ci da yawa ne.
and put a knife to your throat if you possess a great appetite.
3 Kada ka yi marmarin abincinsa mai daɗi gama wannan abinci ruɗu ne.
Do not crave his delicacies, for that food is deceptive.
4 Kada ka gajiyar da kanka don ka yi arziki; ka kasance da hikimar dainawa.
Do not wear yourself out to get rich; be wise enough to restrain yourself.
5 Da ƙyiftawar ido a kan wadata ta ɓace, gama tabbatacce sukan yi fikafikai sukan tashi sama kamar gaggafa.
When you glance at wealth, it disappears, for it makes wings for itself and flies like an eagle to the sky.
6 Kada ka ci abincin mai rowa, kada ka yi marmarin abincinsa mai daɗi;
Do not eat the bread of a stingy man, and do not crave his delicacies;
7 gama shi wani irin mutum ne wanda kullum yana tunani game da tsadar abincin. Zai ce maka, “Ci ka sha,” amma zuciyarsa ba ta tare da kai.
for he is keeping track, inwardly counting the cost. “Eat and drink,” he says to you, but his heart is not with you.
8 Za ka yi amai ɗan abin da ka ci dukan daɗin bakinka kuwa zai tafi a banza.
You will vomit up what little you have eaten and waste your pleasant words.
9 Kada ka yi magana da wawa, gama zai yi wa maganar hikimarka ba’a.
Do not speak to a fool, for he will despise the wisdom of your words.
10 Kada ka kawar da shaidar iyaka ta dā ko ka ɗiba gonar marayu,
Do not move an ancient boundary stone or encroach on the fields of the fatherless,
11 gama mai Kāriyarsu yana da ƙarfi; zai kuwa yi magana dominsu.
for their Redeemer is strong; He will take up their case against you.
12 Ka mai da hankali ga umarni ka kuma kasa kunne ga kalmomin sani.
Apply your heart to instruction and your ears to words of knowledge.
13 Kada ka bar yaro ba horo; in ka yi masa horo da sanda, ba zai mutu ba.
Do not withhold discipline from a child; although you strike him with a rod, he will not die.
14 Ka hukunta shi da sanda ka ceci ransa daga mutuwa. (Sheol )
Strike him with a rod, and you will deliver his soul from Sheol. (Sheol )
15 Ɗana, in zuciyarka mai hikima ce, to, zuciyata za tă yi murna;
My son, if your heart is wise, my own heart will indeed rejoice.
16 cikin cikina zai yi farin ciki in leɓunanka suna maganar abin da yake daidai.
My inmost being will rejoice when your lips speak what is right.
17 Kada ka bar zuciyarka tă yi ƙyashin masu zunubi, amma kullum tsoron Ubangiji za ka yi kishi.
Do not let your heart envy sinners, but always continue in the fear of the LORD.
18 Tabbatacce akwai sa zuciya ta nan gaba dominka, kuma sa zuciyarka ba za tă zama a banza ba.
For surely there is a future, and your hope will not be cut off.
19 Ka saurara, ɗana, ka zama mai hikima, ka kafa zuciyarka a hanyar da take daidai.
Listen, my son, and be wise, and guide your heart on the right course.
20 Kada ka haɗa kai da waɗanda suke shan ruwan inabi da yawa ko masu haɗama kansu da abinci,
Do not join those who drink too much wine or gorge themselves on meat.
21 gama bugaggu da ruwan inabi da masu yawan ci sukan zama matalauta, gama jiri yakan yi musu sutura da tsummoki.
For the drunkard and the glutton will come to poverty, and drowsiness will clothe them in rags.
22 Ka kasa kunne ga mahaifinka, wanda ya ba ka rai, kada kuwa ka rena mahaifiyarka sa’ad da ta tsufa.
Listen to your father who gave you life, and do not despise your mother when she is old.
23 Ka saye gaskiya kada kuwa ka sayar da ita; ka nemi hikima, horo da fahimi.
Invest in truth and never sell it— in wisdom and instruction and understanding.
24 Mahaifin adali yana da farin ciki sosai; duk wanda yake da ɗa mai hikima yakan ji daɗinsa.
The father of a righteous man will greatly rejoice, and he who fathers a wise son will delight in him.
25 Bari mahaifinka da mahaifiyarka su yi murna; bari wadda ta haife ka tă yi farin ciki!
May your father and mother be glad, and may she who gave you birth rejoice!
26 Ɗana, ka ba ni zuciyarka bari kuma idanunka su kiyaye hanyoyina,
My son, give me your heart, and let your eyes delight in my ways.
27 gama karuwa rami ne mai zurfi mace marar aminci matsattsiyar rijiya ce.
For a prostitute is a deep pit, and an adulteress is a narrow well.
28 Kamar’yan fashi, takan kwanta tana jira tana kuma ninka rashin aminci a cikin maza.
Like a robber she lies in wait and multiplies the faithless among men.
29 Wa yake wayyo? Wa yake baƙin ciki? Wa yake neman fada? Wa yake gunaguni? Wa yake da raunuka ba dalili? Wa yake da jan idanu?
Who has woe? Who has sorrow? Who has contentions? Who has complaints? Who has needless wounds? Who has bloodshot eyes?
30 Waɗanda suke daɗe suna shan ruwan inabi, waɗanda suke neman ƙoƙon damammen ruwan inabi.
Those who linger over wine, who go to taste mixed drinks.
31 Kada ka ƙyifce ido a ruwan inabi sa’ad da ya yi ja, sa’ad da yana da kyan gani a cikin ƙwarya, sa’ad da yana gangarawa sumul a maƙogwaro!
Do not gaze at wine while it is red, when it sparkles in the cup and goes down smoothly.
32 A ƙarshe yana sara kamar maciji da kuma dafi kamar gamsheƙa.
In the end it bites like a snake and stings like a viper.
33 Idanunka za su riƙa gane-gane, zuciyarka kuma za su riƙa tunani abubuwa masu rikitarwa.
Your eyes will see strange things, and your mind will utter perversities.
34 Za ka zama kamar wanda yake barci a tsakiyar tekuna, kwance a sama itacen jirgin ruwa.
You will be like one sleeping on the high seas or lying on the top of a mast:
35 Za ka ce “Sun buge ni, amma ban ji ciwo ba! Sun daddoke ni, amma ba na jin zafinsa! Yaushe zan farka don in ƙara shan wani?”
“They struck me, but I feel no pain! They beat me, but I did not know it! When can I wake up to search for another drink?”