< Karin Magana 22 >
1 An fi son suna mai kyau fiye da wadata mai yawa; tagomashi kuma ya fi azurfa ko zinariya.
2 Mawadaci da matalauci suna da abu guda. Ubangiji ne Mahaliccinsu duka.
3 Mai basira kan ga damuwa tana zuwa yă nemi mafaka, amma marar azanci kan yi ta tafiya yă kuma sha wahala.
4 Sauƙinkai da tsoron Ubangiji sukan kawo wadata da girmamawa da kuma rai.
5 A hanyoyin mugu akwai kaya da tarko, amma duk wanda ya kiyaye ransa kan kauce musu.
6 Ka hori yaro a hanyar da ya kamata yă bi, kuma sa’ad da ya tsufa ba zai bar ta ba.
7 Mawadaci yakan yi mulki a kan matalauci, mai cin bashi kuwa bawan mai ba da bashi ne.
8 Duk wanda ya shuka mugunta yakan girbe wahala, za a kuma hallaka sandar fushinsa.
9 Mai bayarwa hannu sake shi kansa zai sami albarka, gama yakan raba abincinsa da matalauta.
10 Ka hori mai ba’a, hatsaniya kuwa za tă yi waje; fitina da zargi kuma za su ƙare.
11 Duk mai son tsabtar zuciya wanda kuma jawabinsa mai alheri ne zai zama aminin sarki.
12 Idanun Ubangiji na lura da sani, amma yakan ƙi kalmomin marar aminci.
13 Rago kan ce, “Akwai zaki a waje!” Ko kuma “Za a kashe ni a tituna!”
14 Bakin mazinaciya rami ne mai zurfi; duk wanda yake a ƙarƙashin fushin Ubangiji zai fāɗa a ciki.
15 Wauta tana da yawa a zuciyar yara, amma sandar horo zai kore ta nesa da su.
16 Duk wanda yake danne matalauta don yă azurta kuma duk wanda yake kyauta ga mawadata, dukansu kan talauta.
17 Ka kasa kunne ka kuma saurara ga maganganu masu hikima; ka yi amfani da abin da nake koyarwa,
18 gama yana da daɗi sa’ad da ka kiyaye su a zuciyarka ka kuma kasance da su a shirye a leɓunanka.
19 Domin dogarawarka ta kasance ga Ubangiji, ina koya maka yau, har kai ma.
20 Ban rubuta maka maganganu talatin ba, maganganun shawara da sani,
21 ina koya maka gaskiya da kalmomin da za ka dogara a kai, saboda ka iya ba da amsa daidai ga duk wanda ya aike ka?
22 Kada ka zalunci matalauta a kan suna matalauta kada kuma ka ƙwari wanda ba shi da mai taimako a gaban shari’a,
23 gama Ubangiji zai yi magana dominsu zai kuwa washe waɗanda suka washe su.
24 Kada ka yi abokantaka da mai zafin rai, kada ka haɗa kai da wanda ba shi da wuya ya yi fushi,
25 in ba haka ba za ka koyi hanyoyinsa ka kuma sa kanka a tarko.
26 Kada ka zama mai ɗaukar lamuni ko ka ba da jingina saboda bashi;
27 gama in ka kāsa biya za a ƙwace gadon da kake kwanciya a kai ma.
28 Kada ka matsar da shaidar kan iyakar da kakanninka suka kafa.
29 Kana ganin mutumin da yake da gwaninta a cikin aikinsa? Zai yi wa sarakuna hidima; ba zai yi hidima wa mutanen da ba su iya ba.