< Karin Magana 21 >

1 A hannun Ubangiji zuciyar sarki kamar ruwan rafi ne wanda yake bi da shi duk inda ya so.
פלגי מים לב מלך ביד יהוה על כל אשר יחפץ יטנו׃
2 Mutum zai yi tunani hanyoyinsa daidai suke, amma Ubangiji yakan auna zuciya.
כל דרך איש ישר בעיניו ותכן לבות יהוה׃
3 Yin abin da yake daidai da kuma nagari Ubangiji ya fi yarda da shi fiye da hadaya.
עשה צדקה ומשפט נבחר ליהוה מזבח׃
4 Girmankai da fariya, su ne fitilar mugaye, wannan kuwa zunubi ne!
רום עינים ורחב לב נר רשעים חטאת׃
5 Shirye-shiryen mai aiki tuƙuru kan kai ga riba in kuwa ka cika gaggawa zai kai ga talauci.
מחשבות חרוץ אך למותר וכל אץ אך למחסור׃
6 Dukiyar da aka samu ta wurin harshe mai yin ƙarya tarin tururi ne da kuma mugun tarko.
פעל אוצרות בלשון שקר הבל נדף מבקשי מות׃
7 Rikicin mugaye zai yi gāba da su, gama sun ƙi su yi abin da yake daidai.
שד רשעים יגורם כי מאנו לעשות משפט׃
8 Hanyar mai laifi karkatacciya ce, amma halin marar laifi sukan aikata gaskiya.
הפכפך דרך איש וזר וזך ישר פעלו׃
9 Gara a zauna a kusurwar rufin ɗaki da a zauna a gida ɗaya da mace mai fitina.
טוב לשבת על פנת גג מאשת מדונים ובית חבר׃
10 Mugun mutum yakan zaƙu ya aikata mugunta; maƙwabcinsa ba ya samun jinƙai daga gare shi.
נפש רשע אותה רע לא יחן בעיניו רעהו׃
11 Sa’ad da aka hukunta mai ba’a marasa azanci suka yi wayo; sa’ad da aka yi wa mai hikima umarni yakan sami sani.
בענש לץ יחכם פתי ובהשכיל לחכם יקח דעת׃
12 Mai Adalci kan lura da gidan mugu kan kuma zama sanadin lalacin mugu.
משכיל צדיק לבית רשע מסלף רשעים לרע׃
13 In mutum ya toshe kunnuwansa ga kukan matalauci, shi ma zai yi kukan neman taimako ba kuwa zai sami amsa ba.
אטם אזנו מזעקת דל גם הוא יקרא ולא יענה׃
14 Kyautar da aka yi a asirce takan kwantar da fushi, kuma cin hancin da aka rufe a cikin riga kan tā da fushi mai tsanani.
מתן בסתר יכפה אף ושחד בחק חמה עזה׃
15 Sa’ad da aka yi adalci, yakan kawo farin ciki ga mai adalci amma fargaba ga masu aikata mugunta.
שמחה לצדיק עשות משפט ומחתה לפעלי און׃
16 Mutumin da ya kauce daga hanyar fahimi kan zo ga hutu a ƙungiyar matattu.
אדם תועה מדרך השכל בקהל רפאים ינוח׃
17 Duk mai son jin daɗi zai zama matalauci; duk mai son ruwan inabi da mai ba zai taɓa zama mai arziki ba.
איש מחסור אהב שמחה אהב יין ושמן לא יעשיר׃
18 Mugu kan zama abin fansa don adali, marar aminci kuma don mai aikata gaskiya.
כפר לצדיק רשע ותחת ישרים בוגד׃
19 Gara a zauna a hamada da a zauna da mace mai fitina da kuma mugun hali.
טוב שבת בארץ מדבר מאשת מדונים וכעס׃
20 A gidan mai hikima akwai wuraren ajiya na abinci da mai masu kyau, amma wawa kan cinye duk abin da yake da shi.
אוצר נחמד ושמן בנוה חכם וכסיל אדם יבלענו׃
21 Duk wanda ya nemi adalci da ƙauna kan sami rai, wadata da girmamawa.
רדף צדקה וחסד ימצא חיים צדקה וכבוד׃
22 Mutum mai hikima kan fāɗa wa birnin jarumawa ya kuma rushe katangar da suka dogara a kai.
עיר גברים עלה חכם וירד עז מבטחה׃
23 Duk wanda yake lura da bakinsa da kuma harshensa kan kiyaye kansa daga masifa.
שמר פיו ולשונו שמר מצרות נפשו׃
24 Mai girmankai da kuma mai fariya, “Mai ba’a” ne sunansa; yana yin abubuwa da girmankai ainun.
זד יהיר לץ שמו עושה בעברת זדון׃
25 Marmarin rago zai zama mutuwarsa, domin hannuwansa sun ƙi su yi aiki.
תאות עצל תמיתנו כי מאנו ידיו לעשות׃
26 Dukan yini yana marmari ya sami ƙari, amma mai adalci yakan bayar hannu sake.
כל היום התאוה תאוה וצדיק יתן ולא יחשך׃
27 Hadayar mugaye abin ƙyama ne, balle ma in aka kawo da mugun nufi!
זבח רשעים תועבה אף כי בזמה יביאנו׃
28 Mai ba da shaidar ƙarya zai hallaka, kuma duk wanda ya saurare shi zai hallaka har abada.
עד כזבים יאבד ואיש שומע לנצח ידבר׃
29 Mugun mutum kan yi tsayin daka, amma mai aikata gaskiya kan yi tunani a kan abin da yake yi.
העז איש רשע בפניו וישר הוא יכין דרכיו׃
30 Babu hikima, babu tunani, babu shirin da zai yi nasara a kan Ubangiji.
אין חכמה ואין תבונה ואין עצה לנגד יהוה׃
31 Akan shirya doki domin ranar yaƙi, amma nasara tana ga Ubangiji ne.
סוס מוכן ליום מלחמה וליהוה התשועה׃

< Karin Magana 21 >