< Karin Magana 20 >
1 Ruwan inabi mai yin ba’a ne, barasa kuma mai rikici ne; duk wanda suka sa ya kauce marar hikima ne.
Wine is a mocker, strong drink is a brawler, and whoever is led astray by them is not wise.
2 Fushin sarki yana kama da rurin zaki; duk wanda ya sa shi fushi zai rasa ransa.
The terror of a king is like the roar of a lion; whoever provokes him forfeits his own life.
3 Bangirma ne ga mutum ya guji faɗa, amma kowane wawa yana saurin yin faɗa.
It is honorable for a man to resolve a dispute, but any fool will quarrel.
4 Rago ba ya noma a lokacin noma; saboda haka a lokacin girbi ba ya bukata samun kome.
The slacker does not plow in season; at harvest time he looks, but nothing is there.
5 Manufofin zuciyar mutum zurfafan ruwaye ne, amma mutum mai basira yakan jawo su.
The intentions of a man’s heart are deep waters, but a man of understanding draws them out.
6 Kowane mutum gani yake shi mai ƙauna marar ƙarewa ne, amma ina? Da ƙyar ka sami amintacce mutum guda.
Many a man proclaims his loving devotion, but who can find a trustworthy man?
7 Mai adalci kan yi rayuwa marar abin zargi; masu albarka ne’ya’yan da za su biyo bayansa.
The righteous man walks with integrity; blessed are his children after him.
8 Sa’ad da sarki ya zauna kan kujerarsa don yă yi shari’a, yakan ga dukan mugunta da idanunsa.
A king who sits on a throne to judge sifts out all evil with his eyes.
9 Wa zai iya cewa, “Na kiyaye zuciyata da tsarki; ni mai tsabta ne marar zunubi kuma”?
Who can say, “I have kept my heart pure; I am cleansed from my sin”?
10 Ma’auni marar gaskiya da magwajin da ba daidai ba, Ubangiji ya ƙi su duka.
Differing weights and unequal measures — both are detestable to the LORD.
11 Akan san ƙananan yara ta ayyukansu, ana iya sani ko rayuwarsu amintattu ne, mai nagarta.
Even a young man is known by his actions— whether his conduct is pure and upright.
12 Kunnuwan da suke ji da kuma idanun da suke gani, Ubangiji ne ya yi su duka.
Ears that hear and eyes that see— the LORD has made them both.
13 Kada ka so barci in ba haka ba za ka talauce; ka zauna a faɗake za ka kuwa kasance da sauran abinci.
Do not love sleep, or you will grow poor; open your eyes, and you will have plenty of food.
14 “Kai, ya yi tsada, ya yi tsada!” In ji mai saya; sa’ad da ya tafi yana taƙama a kan ya iya ciniki.
“Worthless, worthless!” says the buyer, but on the way out, he gloats.
15 Zinariya akwai ta, lu’ulu’u kuma ga shi a yalwace, amma leɓunan da suke magana da sani suna da wuyan samu kamar duwatsu masu daraja.
There is an abundance of gold and rubies, but lips of knowledge are a rare treasure.
16 A karɓi rigunan wanda ya ɗauki lamunin baƙo; a riƙe shi jingina in ya yi shi don mace marar aminci.
Take the garment of the one who posts security for a stranger; get collateral if it is for a foreigner.
17 Abincin da aka samu ta hanyar zamba yakan zama da daɗi, amma mutum zai ƙarasa da baki cike da yashi.
Food gained by fraud is sweet to a man, but later his mouth is full of gravel.
18 Ka yi shirye-shirye ta wurin neman shawara; in kana yaƙi, ka sami bishewa.
Set plans by consultation, and wage war under sound guidance.
19 Mai gulma yakan lalace yarda; saboda haka ka guji mutum mai yawan surutu.
He who reveals secrets is a constant gossip; avoid the one who babbles with his lips.
20 In mutum ya zargi mahaifinsa ko mahaifiyarsa, fitilarsa za tă mutu a tsakiyar duhu.
Whoever curses his father or mother, his lamp will be extinguished in deepest darkness.
21 Gādon da aka samu da sauri a farkon farawa ba zai zama mai albarka a ƙarshe ba.
An inheritance gained quickly will not be blessed in the end.
22 Kada ka ce, “Zan rama wannan abin da aka yi mini!” Ka dogara ga Ubangiji, zai kuwa fisshe ka.
Do not say, “I will avenge this evil!” Wait on the LORD, and He will save you.
23 Ubangiji ya ƙi ma’aunin da ba daidai ba, da kuma magwajin da ba su gamshe shi ba.
Unequal weights are detestable to the LORD, and dishonest scales are no good.
24 Ubangiji ne yake bi da matakan mutum, Ta yaya wani zai fahimci hanyarsa?
A man’s steps are from the LORD, so how can anyone understand his own way?
25 Tarko ne ga mutum ya keɓe wani abu da ba tunani daga baya kuma ya yi la’akari da alkawarinsa.
It is a trap for a man to dedicate something rashly, only later to reconsider his vows.
26 Sarki mai hikima yakan gane mugunta; ya hukunta su ba tausayi.
A wise king separates out the wicked and drives the threshing wheel over them.
27 Fitilar Ubangiji kan bincika zuciyar mutum takan bincika lamirinsa.
The spirit of a man is the lamp of the LORD, searching out his inmost being.
28 Ƙauna da aminci kan kiyaye sarki lafiya; ta wurin ƙauna sarautarsa za tă zauna a kafe.
Loving devotion and faithfulness preserve a king; by these he maintains his throne.
29 Ɗaukakar matasa maza ita ce ƙarfinsu, furfura ita ce darajar tsofaffi.
The glory of young men is their strength, and gray hair is the splendor of the old.
30 Naushi da rauni kan share mugunta, dūka kuma kan tsabtacce lamiri.
Lashes and wounds scour evil, and beatings cleanse the inmost parts.