< Karin Magana 2 >
1 Ɗana, in ka yarda da kalmomina ka kuma ajiye umarnaina a cikinka,
2 kana kasa kunne ga abin da yake na hikima, kana kuma yin ƙoƙari ka fahimce shi,
3 in kuma ka kira ga tsinkaya ka kuma kira da ƙarfi don ganewa,
4 in ka neme shi yadda ake neman azurfa ka kuma neme shi kamar yadda ake neman ɓoyayyiyar dukiya,
5 to, za ka gane tsoron Ubangiji ka kuma sami sanin Allah.
6 Gama Ubangiji yana ba da hikima, daga bakinsa kuma, sani da ganewa sukan fito.
7 Yana riƙe da nasara a ma’aji don masu yin gaskiya, shi ne mafaka ga waɗanda tafiyarsu ba ta da laifi,
8 gama yana tsare abin da masu adalci suke bukata yana kuma tsare hanyar amintattunsa.
9 Sa’an nan za ku fahimci abin da yake daidai da abin da yake na adalci da abin da yake gaskiya, da kowace hanya mai kyau.
10 Gama hikima za tă shiga cikin zuciyarka, sani kuma zai faranta maka rai.
11 Tsinkaya za tă tsare ka, ganewa kuma za tă yi maka jagora.
12 Hikima za tă cece ka daga hanyoyin mugayen mutane, daga kalmomin mutane masu ɓatanci,
13 waɗanda suke barin miƙaƙƙun hanyoyi don su yi tafiya a hanyoyi masu duhu,
14 waɗanda suke jin daɗin yin abin da ba shi da kyau suna kuma farin ciki a mugayen ɓatanci,
15 waɗanda hanyoyinsu karkatattu ne waɗanda kuma suke cuku-cuku a hanyoyinsu.
16 Zai kiyaye ku kuma daga mazinaciya, daga mace mai lalata, mai ƙoƙarin kama ka da daɗin bakinta,
17 wadda ta bar mijin ƙuruciyarta ta kuma ƙyale alkawarin da ta yi a gaban Allah.
18 Gama gidanta yana kai ga mutuwa hanyarta kuma ga ruhohin matattu.
19 Duk wanda ya ziyarce ta ba ya ƙara komowa ba zai ƙara komowa ga hanyar rai.
20 Don haka dole ku yi tafiya a hanyoyin mutanen kirki ku kuma yi ta bi hanyoyin adalai.
21 Gama masu aikata gaskiya za su zauna a cikin ƙasar, marasa laifi kuma za su kasance a cikinta;
22 amma za a fid da mugaye daga ƙasar, za a tumɓuke marasa aminci kuma daga gare ta.