< Karin Magana 18 >

1 Mutumin da ba ya abokantaka yakan nema ya cika burinsa ne kaɗai; yakan ƙi yarda da kowace maganar da take daidai.
לתאוה יבקש נפרד בכל-תושיה יתגלע
2 Wawa ba ya sha’awa ya sami fahimta amma abin da yake so ya yi kaɗai, shi ne ya ba da ra’ayinsa.
לא-יחפץ כסיל בתבונה כי אם-בהתגלות לבו
3 Sa’ad da mugunci ya zo, reni ma kan zo, haka kuma sa’ad da kunya ta zo, shan kunya kan biyo.
בבוא-רשע בא גם-בוז ועם-קלון חרפה
4 Kalmomin bakin mutum suna da zurfi kamar ruwaye, amma maɓulɓulan hikima rafi ne mai gudu.
מים עמקים דברי פי-איש נחל נבע מקור חכמה
5 Ba shi da kyau ka yi wa mugu alheri ko ka hana wa marar laifi adalci.
שאת פני-רשע לא-טוב-- להטות צדיק במשפט
6 Leɓunan wawa kan jawo masa faɗa, bakinsa kuma kan gayyaci dūka.
שפתי כסיל יבאו בריב ופיו למהלמות יקרא
7 Bakin wawa lalatar da kansa yake yi leɓunansa kuma tarko ne ga ransa.
פי-כסיל מחתה-לו ושפתיו מוקש נפשו
8 Kalmomin mai gulma kamar abinci mai daɗi suke; sukan gangara zuwa can cikin gaɓoɓin mutum.
דברי נרגן כמתלהמים והם ירדו חדרי-בטן
9 Wanda yake ragwanci a aikinsa ɗan’uwa ne ga wanda yakan lalatar da abubuwa.
גם מתרפה במלאכתו-- אח הוא לבעל משחית
10 Sunan Ubangiji hasumiya ce mai ƙarfi; masu adalci kan gudu zuwa wurinta don su zauna lafiya.
מגדל-עז שם יהוה בו-ירוץ צדיק ונשגב
11 Dukiyar masu arziki ita ce birninsu mai katanga; suna gani cewa ba za a iya huda katangar ba.
הון עשיר קרית עזו וכחומה נשגבה במשכתו
12 Kafin fāɗuwarsa zuciyar mutum takan yi girman kai, amma sauƙinkai kan zo kafin girmamawa.
לפני-שבר יגבה לב-איש ולפני כבוד ענוה
13 Duk wanda yakan ba da amsa kafin ya saurara, wannan wauta ce da kuma abin kunya.
משיב דבר בטרם ישמע-- אולת היא-לו וכלמה
14 Sa rai da mutum ke yi kan taimake shi sa’ad da yake ciwo, amma in ya karai, to, tasa ta ƙare.
רוח-איש יכלכל מחלהו ורוח נכאה מי ישאנה
15 Zuciya mai la’akari kan nemi sani; kunnuwan mai hikima kan bincika don yă koya.
לב נבון יקנה-דעת ואזן חכמים תבקש-דעת
16 Kyauta kan buɗe hanya wa mai bayarwa yakan kuma kai shi a gaban babban mutum.
מתן אדם ירחיב לו ולפני גדלים ינחנו
17 Wanda ya fara mai da jawabi yakan zama kamar shi ne mai gaskiya, sai wani ya fito ya yi masa tambaya tukuna.
צדיק הראשון בריבו יבא- (ובא-) רעהו וחקרו
18 Jefa ƙuri’a kan daidaita tsakanin masu faɗa ta kuma ajiye masu faɗan a rabe.
מדינים ישבית הגורל ובין עצומים יפריד
19 Ɗan’uwan da aka yi wa laifi ya fi birni mai katanga wuyan shiryawa, kuma faɗace-faɗace suna kama da ƙofofin ƙarfe na fada.
אח--נפשע מקרית-עז ומדונים (ומדינים) כבריח ארמון
20 Daga abin da baki ya furta ne cikin mutum kan cika; girbi daga leɓunansa kuma yakan ƙoshi.
מפרי פי-איש תשבע בטנו תבואת שפתיו ישבע
21 Harshe yana da ikon rai da mutuwa, kuma waɗanda suke ƙaunarsa za su ci amfaninsa.
מות וחיים ביד-לשון ואהביה יאכל פריה
22 Duk wanda ya sami mace ya sami abu mai kyau ya kuma sami tagomashi daga Ubangiji.
מצא אשה מצא טוב ויפק רצון מיהוה
23 Matalauci kan yi roƙo da taushi, amma mawadaci kan amsa da kakkausar murya.
תחנונים ידבר-רש ועשיר יענה עזות
24 Mutum mai abokai masu yawa kan lalace, amma akwai abokin da yakan manne kurkusa fiye da ɗan’uwa.
איש רעים להתרעע ויש אהב דבק מאח

< Karin Magana 18 >