< Karin Magana 17 >
1 Gara ka ci busasshen burodi da kwanciyar rai kuma shiru da ka je cin abinci a gidan da ke cike da biki amma da ɓacin rai.
Better is a dry morsel, and quietness therewith, than a house full of feasting [with] strife.
2 Bawa mai hikima zai yi mulki a kan da mai rashin kunya, kuma zai raba gādo kamar ɗaya daga cikin’yan’uwansa.
A wise servant shall rule over a son that causeth shame, and shall have part in the inheritance among the brethren.
3 Ana gwajin azurfa da kuma zinariya da wuta, amma Ubangiji ne mai gwajin zuciya.
The fining-pot is for silver, and the furnace for gold; but Jehovah trieth the hearts.
4 Mugun mutum kan mai da hankali ga mugayen leɓuna; maƙaryaci yakan kasa kunne ga harshen ƙarairayi.
The evil-doer giveth heed to iniquitous lips; the liar giveth ear to a mischievous tongue.
5 Duk wanda yake wa matalauta ba’a yana zagin Mahaliccinsu ne; duk wanda ya yi murna akan masifar da ta sami wani za a hukunta shi.
Whoso mocketh a poor [man] reproacheth his Maker; he that is glad at calamity shall not be held innocent.
6 Jikoki rawanin tsofaffi ne, kuma iyaye su ne abin taƙamar’ya’yansu.
Children's children are the crown of old men; and the glory of children are their fathers.
7 Leɓunan basira ba su dace da wawa ba, ya ma fi muni a ce mai mulki yana da leɓunan ƙarya!
Excellent speech becometh not a vile [man]; how much less do lying lips a noble!
8 Cin hanci kamar sihiri yake ga wanda yake ba da shi; ko’ina ya juye, yakan yi nasara.
A gift is a precious stone in the eyes of the possessor: whithersoever it turneth it prospereth.
9 Duk wanda ya rufe laifi yana inganta ƙauna ne, amma duk wanda ya yi ta maimaita batu yakan raba abokai na kusa.
He that covereth transgression seeketh love; but he that bringeth a matter up again separateth very friends.
10 Tsawata kan sa mutum ya koyi basira fiye da abin da wawa zai koya ko da an dūke shi sau ɗari.
A reproof entereth more deeply into him that hath understanding than a hundred stripes into a fool.
11 Mugayen mutane sukan kuta tawaye da Allah; za a aika manzo mutuwa a kansu.
An evil [man] seeketh only rebellion; but a cruel messenger shall be sent against him.
12 Gara a haɗu da beyar da aka ƙwace wa’ya’ya fiye da a sadu da wawa cikin wautarsa.
Let a bear robbed of her whelps meet a man rather than a fool in his folly.
13 In mutum ya sāka alheri da mugunta, mugunta ba za tă taɓa barin gidansa ba.
Whoso rewardeth evil for good, evil shall not depart from his house.
14 Farawar faɗa tana kamar ɓarkewa madatsar ruwa ne, saboda haka ka bar batun kafin faɗa ta ɓarke.
The beginning of contention is [as] when one letteth out water; therefore leave off strife before it become vehement.
15 Baratar da mai laifi a kuma hukunta mai adalci, Ubangiji ya ƙi su biyu.
He that justifieth the wicked, and he that condemneth the righteous, even they both are abomination to Jehovah.
16 Mene ne amfanin kuɗi a hannun wawa, da yake ba shi da sha’awar samun hikima?
To what purpose is there a price in the hand of a fool to get wisdom, seeing [he] hath no sense?
17 Aboki yakan yi ƙauna a koyaushe, ɗan’uwa kuma, ai, don ɗaukar nawayar juna ne aka haife shi.
The friend loveth at all times, and a brother is born for adversity.
18 Mutumin da ba shi da azanci yakan ɗauki lamunin wani ya kuma ɗauki nauyin biyan basusuwan maƙwabci.
A senseless man striketh hands, becoming surety for his neighbour.
19 Duk mai son faɗa yana son zunubi, duk wanda ya gina ƙofar shiga mai tsawo yana gayyatar hallaka.
He loveth transgression that loveth a quarrel; he that maketh high his gate seeketh destruction.
20 Mutum mai muguwar zuciya ba ya cin gaba; duk wanda yake da harshen ruɗu kan shiga wahala.
He that hath a perverse heart findeth no good; and he that shifteth about with his tongue falleth into evil.
21 Kasance da wawa kamar ɗa yakan kawo baƙin ciki babu farin ciki ga mahaifin wawa.
He that begetteth a fool [doeth it] to his sorrow, and the father of a vile [man] hath no joy.
22 Zuciya mai farin ciki magani ne mai kyau, amma bakin rai kan busar da ƙasusuwa.
A joyful heart promoteth healing; but a broken spirit drieth up the bones.
23 Mugun mutum yakan karɓa cin hanci a asirce don yă lalace yin adalci.
A wicked [man] taketh a gift out of the bosom, to pervert the paths of judgment.
24 Mutum mai basira kan kafa idonsa a kan hikima, amma idanun wawa suna a kan ƙarshen duniya.
Wisdom is before him that hath understanding; but the eyes of a fool are in the ends of the earth.
25 Da yake wawa yakan kawo baƙin ciki ga mahaifinsa da ɓacin rai ga wanda ya haife shi.
A foolish son is a grief to his father, and bitterness to her that bore him.
26 Ba shi da kyau a hukunta marar laifi, ko a bulale shugaba saboda mutuncinsu.
To punish a righteous [man] is not good, nor to strike nobles because of [their] uprightness.
27 Mutum mai sani yakan yi la’akari da amfani da kalmomi, mutum mai basira kuma natsattse ne.
He that hath knowledge spareth his words; and a man of understanding is of a cool spirit.
28 Ko wawa in bai buɗe bakinsa ba, za a zaci shi mai hikima ne, da kuma mai basira inda ya ƙame bakinsa.
Even a fool when he holdeth his peace is reckoned wise, [and] he that shutteth his lips, intelligent.