< Karin Magana 16 >

1 Ga mutum ne shirye-shiryen zuciya suke, amma daga Ubangiji ne amshin harshe kan zo.
לאדם מערכי-לב ומיהוה מענה לשון
2 Dukan hanyoyin mutum sukan yi kamar marar laifi ne gare shi, amma Ubangiji yakan auna manufofi.
כל-דרכי-איש זך בעיניו ותכן רוחות יהוה
3 Ka miƙa wa Ubangiji dukan abin da kake yi, shirye-shiryenka kuwa za su yi nasara.
גל אל-יהוה מעשיך ויכנו מחשבתיך
4 Ubangiji yana yin kome domin amfaninsa, har ma da mugaye domin ranar masifa.
כל פעל יהוה למענהו וגם-רשע ליום רעה
5 Ubangiji yana ƙyamar dukan zuciya mai girman kai. Ka tabbata da wannan. Ba za su kuɓuta daga hukunci ba.
תועבת יהוה כל-גבה-לב יד ליד לא ינקה
6 Ta wurin ƙauna da aminci akan yi kafarar zunubi; ta wurin tsoron Ubangiji mutum kan guji mugunta.
בחסד ואמת יכפר עון וביראת יהוה סור מרע
7 Sa’ad da hanyoyin mutum sun gamshi Ubangiji, yakan sa abokan gāban mutumin ma su zauna lafiya da shi.
ברצות יהוה דרכי-איש גם-אויביו ישלם אתו
8 Gara ka sami kaɗan ta hanyar adalci da sami riba mai yawa ta hanyar rashin gaskiya.
טוב-מעט בצדקה-- מרב תבואות בלא משפט
9 ’Yan Adam sukan yi shirye-shiryensu a zukatansu, amma Ubangiji ne yake da ikon cika matakansa.
לב אדם יחשב דרכו ויהוה יכין צעדו
10 Leɓunan sarki kan yi magana kamar ta wurin ikon Allah, kuma bai kamata bakinsa ya yi kuskure a yanke shari’a ba.
קסם על-שפתי-מלך במשפט לא ימעל-פיו
11 Ma’aunai da magwajin gaskiya daga Ubangiji ne; dukan ma’aunai da suke cikin jaka yinsa ne.
פלס ומאזני משפט--ליהוה מעשהו כל-אבני-כיס
12 Sarakuna suna ƙyamar abin da ba shi da kyau, gama an kafa kujerar sarauta ta wurin adalci ne.
תועבת מלכים עשות רשע כי בצדקה יכון כסא
13 Sarakuna sukan ji daɗi leɓuna masu yin gaskiya; sukan darjanta mutumin da yake faɗin gaskiya.
רצון מלכים שפתי-צדק ודבר ישרים יאהב
14 Fushin sarki ɗan saƙon mutuwa ne, amma mai hikima yakan faranta masa rai.
חמת-מלך מלאכי-מות ואיש חכם יכפרנה
15 Sa’ad da fuskar sarki ta haska, yana nufin rai ke nan; tagomashinsa yana kamar girgijen ruwa a bazara.
באור-פני-מלך חיים ורצונו כעב מלקוש
16 Ya ma fi kyau ka sami hikima fiye da zinariya, ka zaɓi fahimi a maimakon azurfa!
קנה-חכמה--מה-טוב מחרוץ וקנות בינה נבחר מכסף
17 Buɗaɗɗiyar hanyar masu aikata gaskiya kan guje wa mugunta; duk wanda yake lura da hanyarsa yakan lura da ransa.
מסלת ישרים סור מרע שמר נפשו נצר דרכו
18 Girmankai yakan zo kafin hallaka, girman kai yakan zo kafin fāɗuwa.
לפני-שבר גאון ולפני כשלון גבה רוח
19 Gara ka zama ɗaya daga cikin matalauta masu sauƙinkai, da ka raba ganima da masu girman kai.
טוב שפל-רוח את-עניים (ענוים) מחלק שלל את-גאים
20 Duk wanda ya mai da hankali ga umarni yakan yi nasara, kuma mai albarka ne wanda yake dogara ga Ubangiji.
משכיל על-דבר ימצא-טוב ובוטח ביהוה אשריו
21 Akan ce da masu hikima a zuciya hazikai, kuma kalmomi masu daɗi kan inganta umarni.
לחכם-לב יקרא נבון ומתק שפתים יסיף לקח
22 Fahimi shi ne maɓulɓular rai ga waɗanda suke da shi, amma wauta kan kawo hukunci ga wawaye.
מקור חיים שכל בעליו ומוסר אולים אולת
23 Zuciyar mai hikima kan bi da bakinsa, kuma leɓunansa kan inganta umarni.
לב חכם ישכיל פיהו ועל-שפתיו יסיף לקח
24 Kalmomi masu daɗi suna kama da kakin zuma, mai zaƙi ga rai da kuma warkarwa ga ƙasusuwa.
צוף-דבש אמרי-נעם מתוק לנפש ומרפא לעצם
25 Akwai hanyar da ta yi kamar daidai ga mutum, amma a ƙarshe takan kai ga mutuwa.
יש דרך ישר לפני-איש ואחריתה דרכי-מות
26 Marmarin cin abinci yakan yi wa ɗan ƙodago aiki; yunwarsa kan sa ya ci gaba.
נפש עמל עמלה לו כי-אכף עליו פיהו
27 Mutumin banza yakan ƙulla mugunta, kuma jawabinsa yana kama da wuta mai ƙuna.
איש בליעל כרה רעה ועל-שפתיו (שפתו) כאש צרבת
28 Fitinannen mutum yakan zuga tashin hankali, mai gulma kuma yakan raba abokai na kusa.
איש תהפכות ישלח מדון ונרגן מפריד אלוף
29 Mutum mai tā-da-na-zaune-tsaye yakan ruɗi maƙwabcinsa ya kai shi a hanyar da ba ta da kyau.
איש חמס יפתה רעהו והוליכו בדרך לא-טוב
30 Duk wanda ya ƙyifce da idonsa yana ƙulla maƙarƙashiya ce; duk wanda ya murguɗa leɓunansa yana niyya aikata mugunta ke nan.
עצה עיניו לחשב תהפכות קרץ שפתיו כלה רעה
31 Furfura rawani ne mai daraja; akan same ta ta wurin yin rayuwa ta adalci.
עטרת תפארת שיבה בדרך צדקה תמצא
32 Gara ka zama mai haƙuri da ka zama jarumi, ya fi kyau ka iya mallakar kanka fiye da mallakar birane.
טוב ארך אפים מגבור ומשל ברוחו מלכד עיר
33 Akan jefa ƙuri’a a kan cinya, amma kowace shawara mai kyau daga Ubangiji ne.
בחיק יוטל את-הגורל ומיהוה כל-משפטו

< Karin Magana 16 >