< Karin Magana 15 >

1 Amsa da tattausar harshe kan kwantar da fushi, amma magana da kakkausan harshe kan kuta fushi.
מענה-רך ישיב חמה ודבר-עצב יעלה-אף
2 Harshen mai hikima kan yi zance mai kyau a kan sani, amma bakin wawa kan fitar da wauta.
לשון חכמים תיטיב דעת ופי כסילים יביע אולת
3 Idanun Ubangiji suna a ko’ina, suna lura da masu aikata mugunta da masu aikata alheri.
בכל-מקום עיני יהוה צפות רעים וטובים
4 Harshen da ya kawo warkarwa shi ne itacen rai, amma harshe mai ƙarya kan ragargaza zuciya.
מרפא לשון עץ חיים וסלף בה שבר ברוח
5 Wawa yakan ƙi kulawa da horon da mahaifinsa yake masa, amma duk wanda ya yarda da gyara kan nuna azanci.
אויל--ינאץ מוסר אביו ושמר תוכחת יערים
6 Gidan adali yana da dukiya mai yawa, amma albashin mugaye kan kawo musu wahala.
בית צדיק חסן רב ובתבואת רשע נעכרת
7 Leɓunan masu hikima sukan baza sani; ba haka zukatan wawaye suke ba.
שפתי חכמים יזרו דעת ולב כסילים לא-כן
8 Ubangiji yana ƙyamar hadayar mugaye, amma addu’ar masu aikata gaskiya kan sa ya ji daɗi.
זבח רשעים תועבת יהוה ותפלת ישרים רצונו
9 Ubangiji yana ƙin hanyar mugaye amma yana ƙaunar waɗanda suke neman adalci.
תועבת יהוה דרך רשע ומרדף צדקה יאהב
10 Horo mai tsanani yana jiran duk wanda ya bar hanya; wanda ya ƙi gyara zai mutu.
מוסר רע לעזב ארח שונא תוכחת ימות
11 Mutuwa da Hallaka suna nan a fili a gaban Ubangiji, balle fa zukatan mutane! (Sheol h7585)
שאול ואבדון נגד יהוה אף כי-לבות בני-אדם (Sheol h7585)
12 Mai yin ba’a yakan ƙi gyara; ba zai nemi shawara mai hikima ba.
לא יאהב-לץ הוכח לו אל-חכמים לא ילך
13 Zuciya mai farin ciki kan sa fuska tă yi haske, amma ciwon zuciya kan ragargaza rai.
לב שמח ייטב פנים ובעצבת-לב רוח נכאה
14 Zuciya mai la’akari kan nemi sani, amma bakin wawa wauta ce ke ciyar da shi.
לב נבון יבקש-דעת ופני (ופי) כסילים ירעה אולת
15 Dukan kwanakin mutumin da ake danniya fama yake yi, amma zuciya mai farin ciki yana yin biki kullum.
כל-ימי עני רעים וטוב-לב משתה תמיד
16 Gara a kasance da kaɗan da tsoron Ubangiji da a kasance da arziki mai yawa game da wahala.
טוב-מעט ביראת יהוה-- מאוצר רב ומהומה בו
17 Gara a ci abincin kayan ganye inda akwai ƙauna da a ci kiwotaccen saniya inda ƙiyayya take.
טוב ארחת ירק ואהבה-שם-- משור אבוס ושנאה-בו
18 Mutum mai zafin rai kan kawo faɗa, amma mutum mai haƙuri kan kwantar da faɗa.
איש חמה יגרה מדון וארך אפים ישקיט ריב
19 An tare hanyar rago da ƙayayyuwa, amma hanyar mai aikata gaskiya buɗaɗɗiyar hanya ce.
דרך עצל כמשכת חדק וארח ישרים סללה
20 Ɗa mai hikima kan kawo farin ciki wa mahaifinsa, amma wawa yakan rena mahaifiyarsa.
בן חכם ישמח-אב וכסיל אדם בוזה אמו
21 Wauta kan sa mutum marar azanci ya yi farin ciki, amma mai basira kan kiyaye abin da yake yi daidai.
אולת שמחה לחסר-לב ואיש תבונה יישר-לכת
22 Shirye-shirye sukan lalace saboda rashin neman shawara, amma tare da mashawarta masu yawa za su yi nasara.
הפר מחשבות באין סוד וברב יועצים תקום
23 Mutum yakan yi farin ciki a ba da amsar da take daidai, kuma ina misali a yi magana a lokacin da ya dace!
שמחה לאיש במענה-פיו ודבר בעתו מה-טוב
24 Hanyar rai na yin jagora ya haura wa masu hikima don ta kiyaye shi daga gangarawa zuwa kabari. (Sheol h7585)
ארח חיים למעלה למשכיל-- למען סור משאול מטה (Sheol h7585)
25 Ubangiji yakan rushe gidan mai girman kai amma yakan kiyaye iyakokin gwauruwa daidai.
בית גאים יסח יהוה ויצב גבול אלמנה
26 Ubangiji yana ƙyamar tunanin mugaye, amma waɗanda suke da tunani masu tsabta yakan ji daɗinsu.
תועבת יהוה מחשבות רע וטהרים אמרי-נעם
27 Mutum mai haɗama kan kawo wahala ga iyalinsa, amma wanda yake ƙin cin hanci zai rayu.
עכר ביתו בוצע בצע ושונא מתנת יחיה
28 Zuciyar mai adalci takan auna amsoshinta, amma bakin mugu yakan fitar da mugunta.
לב צדיק יהגה לענות ופי רשעים יביע רעות
29 Ubangiji yana nesa da mugaye amma yakan ji addu’ar adalai.
רחוק יהוה מרשעים ותפלת צדיקים ישמע
30 Fuska mai fara’a takan kawo farin ciki ga zuciya, kuma labari mai daɗi na kawo lafiya ga ƙasusuwa.
מאור-עינים ישמח-לב שמועה טובה תדשן-עצם
31 Duk wanda ya mai da hankali sa’ad da ake tsawata masa ba zai kasance dabam a cikin masu hikima ba.
אזן--שמעת תוכחת חיים בקרב חכמים תלין
32 Duk waɗanda suka ƙi horon sun rena kansu ke nan, amma duk waɗanda sun yarda da gyara sukan ƙara basira.
פורע מוסר מואס נפשו ושומע תוכחת קונה לב
33 Tsoron Ubangiji yakan koya wa mutum hikima, kuma sauƙinkai kan zo kafin girmamawa.
יראת יהוה מוסר חכמה ולפני כבוד ענוה

< Karin Magana 15 >