< Karin Magana 14 >
1 Mace mai hikima kan gina gidanta, amma da hannunta wawiya takan rushe shi ƙasa.
sapiens mulier aedificavit domum suam insipiens instructam quoque destruet manibus
2 Wanda tafiyarsa ta aikata gaskiya ce kan ji tsoron Ubangiji, amma wanda hanyoyinsa ba a kan gaskiya ba ne yakan rena shi.
ambulans recto itinere et timens Deum despicitur ab eo qui infami graditur via
3 Maganar wawa kan kawo sanda a bayansa, amma leɓunan masu hikima kan tsare su.
in ore stulti virga superbiae labia sapientium custodiunt eos
4 Inda ba shanu, wurin sa wa dabbobi abinci zai kasance ba kome, amma daga ƙarfin saniya ce yalwar girbi kan fito.
ubi non sunt boves praesepe vacuum est ubi autem plurimae segetes ibi manifesta fortitudo bovis
5 Mashaidi na gaskiya ba ya ruɗu, amma mashaidin ƙarya kan baza ƙarairayi.
testis fidelis non mentietur profert mendacium testis dolosus
6 Mai ba’a kan nemi hikima amma ba ya samun kome, amma sani kan zo a sawwaƙe ga mai basira.
quaerit derisor sapientiam et non inveniet doctrina prudentium facilis
7 Ka guji wawa, gama ba za ka sami sani a leɓunansa ba.
vade contra virum stultum et nescito labia prudentiae
8 Hikima masu la’akari shi ne su yi tunani a kan hanyoyinsu, amma wautar wawaye ruɗu ne.
sapientia callidi est intellegere viam suam et inprudentia stultorum errans
9 Wawaye kan yi ba’a a gyaran zunubi, amma fatan alheri yana samuwa a cikin masu aikata gaskiya.
stultis inludet peccatum inter iustos morabitur gratia
10 Kowace zuciya ta san ɓacin ranta, kuma babu wani dabam da zai yi rabon jin daɗinsa.
cor quod novit amaritudinem animae suae in gaudio eius non miscebitur extraneus
11 Za a rushe gidan mugu, amma tentin mai aikata gaskiya zai haɓaka.
domus impiorum delebitur tabernacula iustorum germinabunt
12 Akwai hanyar da ta yi kamar tana daidai ga mutum, amma a ƙarshe takan kai ga mutuwa.
est via quae videtur homini iusta novissima autem eius deducunt ad mortem
13 Ko cikin dariya zuciya takan yi ciwo, kuma farin ciki kan iya ƙarasa a baƙin ciki.
risus dolore miscebitur et extrema gaudii luctus occupat
14 Marasa bangaskiya za su sami sakamako cikakke saboda hanyoyinsu, kuma mutumin kirki zai sami lada saboda nasa.
viis suis replebitur stultus et super eum erit vir bonus
15 Marar azanci kan gaskata kome, amma mai la’akari kan yi tunani game da matakinsa.
innocens credit omni verbo astutus considerat gressus suos
16 Mai hikima kan ji tsoron Ubangiji ya kuma guji mugunta, amma wawa yana da girman kai yakan yi kome da garaje.
sapiens timet et declinat malum stultus transilit et confidit
17 Mutum mai saurin fushi yakan yi ayyukan wauta, akan kuma ƙi mai son nuna wayo.
inpatiens operabitur stultitiam et vir versutus odiosus est
18 Marar azanci kan gāji wauta, amma mai la’akari kan sami rawanin sani.
possidebunt parvuli stultitiam et astuti expectabunt scientiam
19 Masu mugunta za su rusuna a gaban masu kirki, mugaye kuma za su yi haka a ƙofofin adalai.
iacebunt mali ante bonos et impii ante portas iustorum
20 Maƙwabta sukan gudu daga matalauta, amma masu arziki suna da abokai da yawa.
etiam proximo suo pauper odiosus erit amici vero divitum multi
21 Duk wanda ya rena maƙwabci ya yi zunubi, amma mai albarka ne wanda yake alheri ga mabukata.
qui despicit proximum suum peccat qui autem miseretur pauperi beatus erit
22 Ba waɗanda suke ƙulla mugunta sukan kauce ba? Amma waɗanda suke ƙulla abin da yake mai kyau sukan sami ƙauna da aminci.
errant qui operantur malum misericordia et veritas praeparant bona
23 Duk aiki tuƙuru yakan kawo riba, amma zama kana surutu kan kai ga talauci kawai.
in omni opere erit abundantia ubi autem verba sunt plurima frequenter egestas
24 Dukiyar masu hikima ita ce rawaninsu, amma wautar wawaye kan haifar da wauta ne kawai.
corona sapientium divitiae eorum fatuitas stultorum inprudentia
25 Mashaidin gaskiya kan ceci rayuka, amma mashaidin ƙarya mai ruɗu ne.
liberat animas testis fidelis et profert mendacia versipellis
26 Duk mai tsoron Ubangiji yana da zaunannen mafaka, kuma ga’ya’yansa zai zama mafaka.
in timore Domini fiducia fortitudinis et filiis eius erit spes
27 Tsoron Ubangiji shi ne maɓulɓular rai yakan juye mutum daga tarkon mutuwa.
timor Domini fons vitae ut declinet a ruina mortis
28 Yawan mutane shi ne ɗaukakar sarki, amma in ba tare da mabiya ba sarki ba kome ba ne.
in multitudine populi dignitas regis et in paucitate plebis ignominia principis
29 Mutum mai haƙuri yana da fahimi mai yawa, amma mai saurin fushi yakan nuna wautarsa a fili.
qui patiens est multa gubernatur prudentia qui autem inpatiens exaltat stultitiam suam
30 Zuciya mai salama kan ba jiki rai, amma kishi kan sa ƙasusuwa su yi ciwo.
vita carnium sanitas cordis putredo ossuum invidia
31 Duk wanda ya zalunci matalauci ya zagi Mahaliccinsu ke nan, amma duk wanda ya yi alheri ga mabukata yana girmama Allah ne.
qui calumniatur egentem exprobrat factori eius honorat autem eum qui miseretur pauperis
32 Sa’ad bala’i ya auku, mugaye kan fāɗi, amma ko a mutuwa masu adalci suna da mafaka.
in malitia sua expelletur impius sperat autem iustus in morte sua
33 Hikima tana a zuciyar mai azanci, kuma ko a cikin wawaye takan sa a santa.
in corde prudentis requiescit sapientia et indoctos quoque erudiet
34 Adalci yakan ɗaukaka al’umma, amma zunubi kan kawo kunya ga kowane mutane.
iustitia elevat gentem miseros facit populos peccatum
35 Sarki yakan yi murna a kan bawa mai hikima, amma bawa marar kunya kan jawo fushinsa.
acceptus est regi minister intellegens iracundiam eius inutilis sustinebit