< Karin Magana 13 >

1 Ɗa mai hikima yakan mai da hankali ga umarnin mahaifinsa, amma mai ba’a ba ya sauraran kwaɓi.
בן חכם מוסר אב ולץ לא-שמע גערה
2 Daga abin da ya fito leɓunan mutum ne mutum kan ji daɗin abubuwa masu kyau, amma marar aminci yakan ƙosa ya tā-da-na-zaune-tsaye.
מפרי פי-איש יאכל טוב ונפש בגדים חמס
3 Duk mai lura da leɓunansa yakan lura da ransa, amma duk mai magana da haushi zai kai ga lalaci.
נצר פיו שמר נפשו פשק שפתיו מחתה-לו
4 Rago ya ƙosa ya sami wani abu ainun amma ba ya samun kome, amma sha’awar mai aiki tuƙuru yakan ƙoshi sosai.
מתאוה ואין נפשו עצל ונפש חרצים תדשן
5 Adali yana ƙin abin da yake ƙarya, amma mugu kan jawo kunya da ƙasƙanci.
דבר-שקר ישנא צדיק ורשע יבאיש ויחפיר
6 Adalci yakan lura da mutum mai mutunci, amma mugunta takan sha kan mai zunubi.
צדקה תצר תם-דרך ורשעה תסלף חטאת
7 Wani mutum yakan ɗauki kansa mai arziki ne, alhali ba shi da kome, wani ya ɗauki kansa shi matalauci ne, alhali shi mawadaci ne ƙwarai.
יש מתעשר ואין כל מתרושש והון רב
8 Arzikin mutum zai iya kuɓutar da ransa, amma matalauci ba ya jin barazana.
כפר נפש-איש עשרו ורש לא-שמע גערה
9 Hasken masu adalci kan haskaka ƙwarai, amma fitilar mugaye mutuwa take.
אור-צדיקים ישמח ונר רשעים ידעך
10 Girmankai kan jawo faɗa ne kawai, amma hikima tana samuwa a waɗanda suke jin shawara.
רק-בזדון יתן מצה ואת-נועצים חכמה
11 Kuɗin da aka same su a rashin gaskiya yakan ɓace da sauri, amma duk wanda ya tara kuɗi kaɗan-kaɗan za su yi ta ƙaruwa.
הון מהבל ימעט וקבץ על-יד ירבה
12 Sa zuciyar da aka ɗaga zuwa gaba kan sa zuciya tă yi ciwo, amma marmarin da aka ƙosar yana kamar itacen rai.
תוחלת ממשכה מחלה-לב ועץ חיים תאוה באה
13 Duk wanda ya rena umarni zai ɗanɗana ƙodarsa, amma duk wanda ya yi biyayya da umarni zai sami lada.
בז לדבר יחבל לו וירא מצוה הוא ישלם
14 Koyarwar mai hikima maɓulɓulan rai ne, mai juyar da mutum daga tarkon mutuwa.
תורת חכם מקור חיים-- לסור ממקשי מות
15 Fahimta mai kyau kan sami tagomashi, amma hanyar marar aminci tana da wuya.
שכל-טוב יתן-חן ודרך בגדים איתן
16 Kowane mai azanci yakan nuna sani, amma wawa yakan yi tallen wawancinsa.
כל-ערום יעשה בדעת וכסיל יפרש אולת
17 Mugun ɗan saƙo kan shiga wahala, amma jakadan da mai aminci yakan kawo warkarwa.
מלאך רשע יפל ברע וציר אמונים מרפא
18 Duk wanda ya ƙyale horo yakan kai ga talauci da kuma kunya, amma duk wanda ya karɓi gyara yakan sami girma.
ריש וקלון פורע מוסר ושמר תוכחת יכבד
19 Marmarin da aka cika yana da daɗi ga rai, amma wawa yana ƙyamar juyewa daga mugunta.
תאוה נהיה תערב לנפש ותועבת כסילים סור מרע
20 Shi da yake tafiya tare da masu hikima yakan ƙaru da hikima, amma abokin wawaye zai yi fama da lahani.
הלוך (הולך) את-חכמים וחכם (יחכם) ורעה כסילים ירוע
21 Rashin sa’a kan fafare mai zunubi, amma wadata ce ladar adali.
חטאים תרדף רעה ואת-צדיקים ישלם-טוב
22 Mutumin kirki kan bar gādo wa’ya’ya’ya’yansa, amma arzikin mai zunubi ajiye ne da aka yi wa mai adalci.
טוב--ינחיל בני-בנים וצפון לצדיק חיל חוטא
23 Gonar matalauci za tă iya ba da abinci a yalwace, amma rashin adalci kan share shi tas.
רב-אכל ניר ראשים ויש נספה בלא משפט
24 Duk wanda ba ya horon ɗansa ba ƙaunarsa yake yi ba, amma duk mai ƙaunarsa yakan kula ya hore shi.
חושך שבטו שונא בנו ואהבו שחרו מוסר
25 Masu adalci sukan ci isashen abinci, amma cikin mugaye na fama da yunwa.
צדיק--אכל לשבע נפשו ובטן רשעים תחסר

< Karin Magana 13 >