< Karin Magana 12 >
1 Duk mai ƙaunar horo yana ƙaunar sani, amma duk mai ƙin gyara wawa ne.
Whoever loves discipline loves knowledge, but he who hates correction is stupid.
2 Mutumin kirki kan sami tagomashi daga Ubangiji, amma Ubangiji yakan hukunta mai son yin wayo.
The good man obtains favor from the LORD, but the LORD condemns a man who devises evil.
3 Ba yadda mutum zai kahu ta wurin aikata mugunta, amma ba za a tumɓuke adali ba.
A man cannot be established through wickedness, but the righteous cannot be uprooted.
4 Mace mai halin kirki rawanin mijinta ne, amma mace marar kunya tana kama da ciwo a ƙasusuwansa.
A wife of noble character is her husband’s crown, but she who causes shame is like decay in his bones.
5 Shirye-shiryen masu adalci daidai ne, amma shawarar mugaye ruɗu ne.
The plans of the righteous are just, but the counsel of the wicked leads to deceit.
6 Kalmomin mugu sukan kwanta suna jira su yi kisankai, amma jawabin masu aikata gaskiya kan kuɓutar da su.
The words of the wicked lie in wait for blood, but the speech of the upright rescues them.
7 Akan tumɓuke mugaye ba a ƙara ganinsu, amma gidan masu adalci kan tsaya daram.
The wicked are overthrown and perish, but the house of the righteous will stand.
8 Akan yabi mutum bisa ga hikimarsa, amma mutane marasa azanci akan rena su.
A man is praised according to his wisdom, but a twisted mind is despised.
9 Gara ka zama kai ba kome ba ne amma kana da bawa da ka mai da kanka kai wani ne alhali kuwa ba ka da abinci.
Better to be lightly esteemed yet have a servant, than to be self-important but lack food.
10 Mai adalci kan kula da bukatun dabbobinsa, amma halaye mafi kyau na mugaye su ne ƙeta.
A righteous man regards the life of his animal, but the tender mercies of the wicked are only cruelty.
11 Duk wanda ya nome gonarsa zai sami abinci a yalwace, amma shi da yake naushin iska marar azanci ne.
The one who works his land will have plenty of food, but whoever chases fantasies lacks judgment.
12 Mugaye suna sha’awar ganimar mugayen mutane, amma saiwar masu adalci kan haɓaka.
The wicked desire the plunder of evil men, but the root of the righteous flourishes.
13 Mugun mutum kan fāɗa a tarkon maganarsa ta zunubi, amma adali kan kuɓuta daga wahala.
An evil man is trapped by his rebellious speech, but a righteous man escapes from trouble.
14 Daga abubuwan da suke fitowa daga leɓunansa mutum kan cika da abubuwa masu kyau tabbatacce yadda aikin hannuwansa suke ba shi lada.
By fruitful speech a man is filled with good things, and the work of his hands returns to him.
15 Hanyar wawa daidai take a gare shi, amma mai hikima kan saurari shawara.
The way of a fool is right in his own eyes, but a wise man listens to counsel.
16 Wawa kan nuna fushinsa nan take, amma mai la’akari kan ƙyale zargi.
A fool’s anger is known at once, but a prudent man overlooks an insult.
17 Mashaidin gaskiya kan ba da shaidar gaskiya, amma mashaidin ƙarya yana baza ƙarairayi ne.
He who speaks the truth declares what is right, but a false witness speaks deceit.
18 Maganganun rashin tunani sukan soki mutum kamar takobi, amma harshen mai hikima kan kawo warkarwa.
Speaking rashly is like a piercing sword, but the tongue of the wise brings healing.
19 Leɓunan gaskiya kan dawwama har abada, amma harshen ƙarya yakan dawwama na ɗan lokaci ne kawai.
Truthful lips endure forever, but a lying tongue lasts only a moment.
20 Akwai ruɗu a zukatan waɗanda suke ƙulla mugunta, amma waɗanda suke aikata alheri za su yi farin ciki.
Deceit is in the hearts of those who devise evil, but the counselors of peace have joy.
21 Ba wani lahanin da zai sami masu adalci, amma mugaye suna da nasu cike da wahala.
No harm befalls the righteous, but the wicked are filled with trouble.
22 Ubangiji yana ƙyamar leɓunan masu ƙarya, amma yana jin daɗin mutanen da suke masu gaskiya.
Lying lips are detestable to the LORD, but those who deal faithfully are His delight.
23 Mai la’akari kan kiyaye saninsa wa kansa, amma zuciyar wawa kan yi ta tallar wawanci.
A shrewd man keeps his knowledge to himself, but a foolish heart proclaims its folly.
24 Hannuwan masu aiki tuƙuru za su yi mulki, amma ragwanci kan ƙarasa a aikin bauta.
The hand of the diligent will rule, but laziness ends in forced labor.
25 Zuciya mai damuwa takan naƙasar da mutum, amma maganar alheri kan faranta masa rai.
Anxiety weighs down the heart of a man, but a good word cheers it up.
26 Adali yakan yi hankali a abokantaka, amma hanyar mugaye kan kai su ga kaucewa.
A righteous man is cautious in friendship, but the ways of the wicked lead them astray.
27 Rago ba ya gashin abin da ya kama daga farauta, amma mai aiki tuƙuru yakan ɗauki mallakarsa da muhimmanci.
A lazy man does not roast his game, but a diligent man prizes his possession.
28 A hanyar adalci akwai rai; a wannan hanya akwai rashin mutuwa.
There is life in the path of righteousness, but another path leads to death.