< Karin Magana 11 >
1 Ubangiji yana ƙyamar ma’aunan zamba, amma ma’aunin da suke daidai ne abin farin cikinsa.
Dishonest scales are an abomination to the LORD, but an accurate weight is His delight.
2 Sa’ad da girman kai ya zo, sai shan kunya ta zo, amma hikima kan zo tare da ƙasƙantar da kai.
When pride comes, disgrace follows, but with humility comes wisdom.
3 Mutuncin masu aikata gaskiya takan bi da su, amma marasa aminci sukan hallaka ta wurin cin amanar da suke yi.
The integrity of the upright guides them, but the perversity of the faithless destroys them.
4 Dukiya ba ta da amfani a ranar fushi, amma adalci kan yi ceto daga mutuwa.
Riches are worthless in the day of wrath, but righteousness brings deliverance from death.
5 Adalcin marasa laifi kan miƙe hanyarsu, amma akan ƙasƙantar da mugaye ta wurin muguntarsu.
The righteousness of the blameless directs their path, but the wicked fall by their own wickedness.
6 Adalcin masu aikata gaskiya kan cece su, amma rashin aminci tarko ne ga mugayen sha’awace-sha’awace.
The righteousness of the upright delivers them, but the faithless are trapped by their own desires.
7 Sa’ad da mugu ya mutu, sa zuciyarsa kan hallaka; dukan abin da ya sa zuciya daga ikonsa ba ya amfana kome.
When the wicked man dies, his hope perishes, and the hope of his strength vanishes.
8 Akan kuɓutar da mai adalci daga wahala, sai ta dawo wa mugu a maimako.
The righteous man is delivered from trouble; in his place the wicked man goes in.
9 Da bakinsa marar sanin Allah kan hallaka maƙwabcinsa, amma ta wurin sani mai adalci kan kuɓuta.
With his mouth the ungodly man destroys his neighbor, but through knowledge the righteous are rescued.
10 Sa’ad da adali ya yi nasara, birnin kan yi farin ciki; sa’ad da mugu ya hallaka, akwai sowa ta farin ciki.
When the righteous thrive, the city rejoices, and when the wicked perish, there are shouts of joy.
11 Ta wurin albarkar mai aikata gaskiya birni kan ƙasaita, amma ta wurin bakin mugu akan hallaka birnin.
By the blessing of the upright a city is built up, but by the mouth of the wicked it is torn down.
12 Mutum da ba shi da azanci kan ki maƙwabci, amma mutum mai fahimi kan ƙame harshensa.
Whoever shows contempt for his neighbor lacks judgment, but a man of understanding remains silent.
13 Gulma yakan lalace yarda, amma mutum mai aminci kan kiyaye asiri.
A gossip reveals a secret, but a trustworthy person keeps a confidence.
14 Saboda rashin jagora al’umma takan fāɗi, amma masu ba da shawara da yawa kan tabbatar da nasara.
For lack of guidance, a nation falls, but with many counselors comes deliverance.
15 Duk wanda ya ɗauki lamunin wani tabbatacce zai sha wahala, amma duk wanda ya ƙi ya sa hannu a ɗaukar lamuni ba ruwansa.
He who puts up security for a stranger will surely suffer, but the one who hates indebtedness is secure.
16 Mace mai hankali na samu bangirma, amma azzalumai za su sami dukiya.
A gracious woman attains honor, but ruthless men gain only wealth.
17 Mutumin kirki kan ribance kansa, amma mugu kan kawo wa kansa wahala.
A kind man benefits himself, but a cruel man brings trouble on himself.
18 Mugun mutum kan sami albashin ƙarya amma shi da ya shuka adalci zai girbe lada tabbatacce.
The wicked man earns an empty wage, but he who sows righteousness reaps a true reward.
19 Mutum mai adalci da gaske yakan sami rai, amma shi da ya duƙufa ga aikata mugunta kan tarar da mutuwarsa.
Genuine righteousness leads to life, but the pursuit of evil brings death.
20 Ubangiji yana ƙyamar mutane masu muguwar zuciya amma yana jin daɗin waɗanda hanyoyinsu ba su da laifi.
The perverse in heart are an abomination to the LORD, but the blameless in their walk are His delight.
21 Ka tabbata da wannan. Mugaye ba za su tafi babu hukunci ba, amma waɗanda suke masu adalci za su tafi babu hukunci.
Be assured that the wicked will not go unpunished, but the offspring of the righteous will escape.
22 Kamar zinariya a hancin alade haka kyan mace wadda ba ta da hankali.
Like a gold ring in a pig’s snout is a beautiful woman who lacks discretion.
23 Sha’awar adalai kan ƙare kawai a aikata alheri, amma sa zuciyar mugaye kan ƙarasa kawai a fushi.
The desire of the righteous leads only to good, but the hope of the wicked brings wrath.
24 Wani mutum kan bayar hannu sake, duk da haka yakan sami fiye; wani yakan riƙe abin da ba nasa ba, amma sai ya ƙarasa cikin talauci.
One gives freely, yet gains even more; another withholds what is right, only to become poor.
25 Mutum mai kyauta zai azurta; shi da yakan taimake waɗansu, za a taimake shi.
A generous soul will prosper, and he who refreshes others will himself be refreshed.
26 Mutane kan la’anci mai ɓoye hatsi yana jira ya yi tsada, amma albarka kan zauna a kan wanda yake niyya ya sayar.
The people will curse the hoarder of grain, but blessing will crown the one who sells it.
27 Duk mai nema alheri kan sami alheri, amma mugu kan zo wa wanda yake nemansa.
He who searches out good finds favor, but evil will come to him who seeks it.
28 Duk wanda ya dogara ga arzikinsa zai fāɗi, amma adali zai yi nasara kamar koren ganye.
He who trusts in his riches will fall, but the righteous will thrive like foliage.
29 Duk wanda ya kawo wahala wa iyalinsa zai gāji iska kawai, kuma wawa zai zama bawan masu hikima.
He who brings trouble on his house will inherit the wind, and the fool will be servant to the wise of heart.
30 ’Ya’yan itacen adali itacen rai ne, kuma duk mai samun rayuka mai hikima ne.
The fruit of the righteous is a tree of life, and he who wins souls is wise.
31 In masu adalci sun sami abin da ya dace da su a duniya, yaya zai zama ga marasa sanin Allah da kuma masu zunubi!
If the righteous receive their due on earth, how much more the ungodly and the sinner!