< Karin Magana 10 >

1 Karin maganar Solomon. Ɗa mai hikima yakan kawo wa mahaifinsa farin ciki, amma wawan ɗa kan sa wa mahaifiyarsa baƙin ciki.
משלי שלמה בן חכם ישמח אב ובן כסיל תוגת אמו׃
2 Dukiyar da aka samu a hanyar da ba tă dace ba, ba ta da albarka, amma adalci kan ceci mutum daga mutuwa.
לא יועילו אוצרות רשע וצדקה תציל ממות׃
3 Ubangiji ba ya barin mai adalci da yunwa amma yakan lalace burin mugu.
לא ירעיב יהוה נפש צדיק והות רשעים יהדף׃
4 Ragwanci kan sa mutum yă zama matalauci, amma aiki tuƙuru kan ba da dukiya.
ראש עשה כף רמיה ויד חרוצים תעשיר׃
5 Shi da ya tattara hatsi da rani ɗa ne mai hikima, amma shi da yakan yi barci a lokacin girbi ɗa ne wanda ya zama abin kunya.
אגר בקיץ בן משכיל נרדם בקציר בן מביש׃
6 Albarka kan zauna a kan mai adalci kamar rawani, amma rikici kan sha bakin mugu.
ברכות לראש צדיק ופי רשעים יכסה חמס׃
7 Tunawa da mai adalci albarka ne amma sunan mugu zai ruɓe.
זכר צדיק לברכה ושם רשעים ירקב׃
8 Mai hikima a zuciya yakan yarda da umarni amma surutun wawa kan kai ga lalaci.
חכם לב יקח מצות ואויל שפתים ילבט׃
9 Mai mutunci yana tafiya lafiya, amma shi da yake tafiya a karkatattun hanyoyi za a kama shi.
הולך בתם ילך בטח ומעקש דרכיו יודע׃
10 Shi da ya ƙyifta ido da mugunta kan jawo baƙin ciki surutun wawa kuma kan zo da lalaci.
קרץ עין יתן עצבת ואויל שפתים ילבט׃
11 Bakin adali maɓulɓulan rai ne, amma kalmar mugun takan ɓoye makircinsa.
מקור חיים פי צדיק ופי רשעים יכסה חמס׃
12 Ƙiyayya kan haddasa wahala, amma ƙauna kan rufe dukan laifofi.
שנאה תעורר מדנים ועל כל פשעים תכסה אהבה׃
13 Ana samun hikima a leɓunan masu fahimi, amma bulala domin bayan marasa azanci ne.
בשפתי נבון תמצא חכמה ושבט לגו חסר לב׃
14 Mai hikima kan yi ajiyar sani, amma bakin wawa kan gayyaci lalaci.
חכמים יצפנו דעת ופי אויל מחתה קרבה׃
15 Dukiyar masu arziki yakan zama mafakar birninsu, amma talauci shi ne lalacin matalauci.
הון עשיר קרית עזו מחתת דלים רישם׃
16 Hakkin adalai kan kawo musu rai, amma albashin mugaye kan kawo musu hukunci.
פעלת צדיק לחיים תבואת רשע לחטאת׃
17 Duk wanda ya mai da hankali ga horo kan nuna hanyar rai, amma duk wanda ya ƙyale gyara kan sa waɗansu su kauce.
ארח לחיים שומר מוסר ועוזב תוכחת מתעה׃
18 Duk wanda ya ɓoye ƙiyayyarsa yana da ƙarya a leɓunansa, duk kuma wanda yake baza ƙarairayi wawa ne.
מכסה שנאה שפתי שקר ומוצא דבה הוא כסיל׃
19 Sa’ad da magana ta yi yawa, ba a rasa zunubi a ciki, amma shi da ya ƙame harshensa mai hikima ne.
ברב דברים לא יחדל פשע וחשך שפתיו משכיל׃
20 Harshen adali azurfa ce zalla, amma zuciyar mugu ba ta da wani amfani.
כסף נבחר לשון צדיק לב רשעים כמעט׃
21 Leɓunan adalai kan amfane yawanci, amma wawa kan mutu saboda rashin azanci.
שפתי צדיק ירעו רבים ואוילים בחסר לב ימותו׃
22 Albarkar Ubangiji kan kawo wadata, ba ya kuma ƙara wahala a kai.
ברכת יהוה היא תעשיר ולא יוסף עצב עמה׃
23 Wawa yakan ji daɗi halin mugunta, amma mutum mai fahimi kan ji daɗin hikima.
כשחוק לכסיל עשות זמה וחכמה לאיש תבונה׃
24 Abin da mugu ke tsoro shi ne zai same shi; abin da adali ke bukata yakan sami biyan bukata.
מגורת רשע היא תבואנו ותאות צדיקים יתן׃
25 Sa’ad da hadiri ya taso, yakan watsar da mugaye, amma adalai za su tsaya daram har abada.
כעבור סופה ואין רשע וצדיק יסוד עולם׃
26 Kamar yadda ruwan tsami yake ga haƙora hayaƙi kuma ga idanu, haka malalaci yake ga wanda ya aike shi.
כחמץ לשנים וכעשן לעינים כן העצל לשלחיו׃
27 Tsoron Ubangiji kan ƙara tsawon rai, amma akan gajartar da shekarun mugaye.
יראת יהוה תוסיף ימים ושנות רשעים תקצרנה׃
28 Abin da adali yake sa rai yakan kai ga farin ciki, amma sa zuciyar mugu ba ya haifar da kome.
תוחלת צדיקים שמחה ותקות רשעים תאבד׃
29 Hanyar Ubangiji mafaka ce ga adalai amma lalaci ne ga waɗanda suke aikata mugunta.
מעוז לתם דרך יהוה ומחתה לפעלי און׃
30 Ba za a taɓa tumɓuke masu adalci ba, amma mugaye ba za su ci gaba da kasance a ƙasar ba.
צדיק לעולם בל ימוט ורשעים לא ישכנו ארץ׃
31 Bakin adalai kan fitar da hikima, amma za a dakatar da mugun harshe.
פי צדיק ינוב חכמה ולשון תהפכות תכרת׃
32 Leɓunan adalai sun san abin da ya dace, amma bakunan mugaye sun san abin da yake mugu ne kawai.
שפתי צדיק ידעון רצון ופי רשעים תהפכות׃

< Karin Magana 10 >