< Filibbiyawa 4 >
1 Saboda haka’yan’uwana, ku da nake ƙauna, nake kuma marmarin ganinku, ku da kuke farin cikina da kuma rawanina, ku dāge ga Ubangiji, ya ku ƙaunatattuna!
Saboda haka, kaunatattu 'yan'uwana da nake marmari, farin ciki na da rawani na, a wannan hanya ku tsaya daram cikin Ubangiji, kaunatattun abokai.
2 Ina roƙon Yuwodiya ina kuma roƙon Sintike, su yi zaman lafiya da juna saboda su na Ubangiji ne.
Ina rokon Afodiya, ina rokon Sintiki, ku zama da ra'ayi daya cikin Ubangiji.
3 I, ina kuma roƙonka, abokin famata, ka taimaki matan nan waɗanda suka yi fama aikin bishara tare da ni, haka ma Kilemen da kuma sauran abokan aikina, waɗanda sunayensu suna cikin littafin rai.
Babu shakka, ina sake rokon ku, abokan tarayyar takunkumina na gaske: ku taimaka wa matayen nan. Domin mun yi wahala tare a cikin yada bishara tare da Kilimas da sauran abokan aiki na, wanda sunayensu na rubuce cikin littafin rai.
4 Ku yi farin ciki a cikin Ubangiji kullum. Ina sāke gaya muku ku yi farin ciki!
Yi farin ciki cikin Ubangiji kullayomi. Ina sake cewa, yi farin ciki.
5 Bari kowa yă kasance da sauƙinkai. Ubangiji ya yi kusan zuwa.
Bari dukan mutane su ga jimirin ku. Ubangiji ya yi kusa.
6 Kada ku damu game da kome sai dai a cikin abu duka, ku gabatar da roƙe-roƙenku ga Allah ta wurin addu’a da roƙo, tare da godiya.
Kada ku damu da kowanne abu, maimakon haka, cikin komai tare da addu'a, da rokeroke, da godiya, bari rokeroken ku su sanu ga Allah.
7 Salamar Allah, wadda ta wuce dukan fahimta, za tă tsai da zukatanku da tunaninku cikin Kiristi Yesu.
Salamar Allah, da ta zarce dukan ganewa za ta tsare zuciyarku da tunaninku cikin Almasihu Yesu.
8 A ƙarshe,’yan’uwa, duk abin da yake na gaskiya, duk abin da yake na girmamawa, duk abin da yake daidai, duk abin da yake da tsarki, duk abin da yake kyakkyawa, duk abin da yake na sha’awa, in ma wani abu mafifici ne, ko ya cancanci yabo, ku yi tunani a kan irin abubuwan nan.
A karshe, 'yan'uwa, duk abin da ke mai gaskiya, duk abin da ya isa ban girma, duk abin da ke mai adalci, duk abin da ke mai tsabta, duk abin da ke karbabbe, duk abin da ke kawo kauna, duk abin da ke da kyakkyawan ambato, idan akwai yabo, yi tunani a kan wadannan abubuwan.
9 Duk abin da kuka koya ko kuka karɓa ko kuka ji daga wurina, ko kuka gani a cikina, ku yi aiki da shi. Allah na salama kuma zai kasance tare da ku.
Wadannan abubuwan da kuka koya kuka karba kuka ji kuka gani a rayuwa ta, ku aikata wadannan abubuwan. Allah mai salama zai kasance tare da ku.
10 Na yi farin ciki sosai ga Ubangiji don yanzu kun sāke nuna kun kula da ni. Ko da yake dā ma kun kula da ni sai dai ba ku sami dama ku nuna mini ba.
Na yi farin ciki sosai cikin Ubangiji domin yanzu a karshe kun sabunta kulawar ku game da ni. Kun kula da ni da gaske kwanakin baya, amma ba ku samu zarafin taimako ba.
11 Ba na faɗin haka domin ina cikin bukata, gama na koya yadda zan gamsu a cikin kowane hali.
Ba don bukata ta bane nake fada wannan. Domin na koyi dangana a kowanne irin yanayi.
12 Na san mene ne zaman rashi, na kuma san mene ne zaman samu. Zan iya zama cikin kowane hali, ko cikin ƙoshi ko cikin yunwa, ko cikin yalwa ko kuma cikin fatara.
Na san yadda zan zauna cikin bukata, na kuma san yadda zan samu a yalwace. A kowace hanya cikin kowanne abu na koyi asirin yadda zan ci da yawa da yadda zan zauna da yunwa, yadda zan zama a yalwace kuma in zama cikin bukata.
13 Ina iya yin kome ta wurin wannan wanda yake ba ni ƙarfi.
Zan iya yin komai ta wurinsa shi da yake karfafa ni.
14 Duk da haka kun kyauta da kuka yi tarayya da ni cikin wahalolina.
Duk da haka, kun yi zumunta da ni cikin kunci na.
15 Ban da haka, kamar yadda ku Filibbiyawa kuka sani, a farkon kwanakin da kuka ji bishara, sa’ad da na tashi daga Makidoniya, babu wata ikkilisiyar da tă yi tarayya da ni a fannin bayarwa da karɓa, sai ku kaɗai;
Kun kuma sani, ku Filibiyawa, cewa da farkon bishara, lokacin da na bar Makidoniya, babu ikilisiya da ta tallafe ni cikin batun bayarwa da karba sai ku kadai.
16 gama ko sa’ad da nake a Tessalonika ma, kun aiko mini da taimako sau da sau sa’ad da nake cikin bukata.
Ko lokacin da nake Tassalonika, kun aika da gudumawar biyan bukatu na fiye da sau daya.
17 Ba cewa ina neman kyauta ba ne, sai dai ina neman abin da za a ƙara a kan ribarku.
Ba domin ina neman kyauta ba ne. A maimakon haka, ina neman amfani da zai kawo karuwa cikin ajiyar ku.
18 An biya ni duka, biyan da ya wuce misali. Bukatata ta biya, da yake na karɓi kyautarku da kuka aiko ta hannun Afaforiditus. Baiwa mai ƙanshi, hadaya abar karɓa, mai faranta wa Allah rai.
Na karbi dukan abubuwan, ina da shi a yalwace. An kosar da ni. Na karba ta hanun Abafroditus abubuwa daga wurinku. Shesheki na dadin kamshi mai dandanno, karbabbiyar hadaya mai gamsarwa ga Allah.
19 Allahna kuma zai biya dukan bukatunku bisa ga ɗaukakar wadatarsa cikin Kiristi Yesu.
Allah na zai cika dukan bukatunku bisa ga yalwarsa da ke cikin daukaka cikin Almasihu Yesu.
20 Ɗaukaka ta tabbata ga Allahnmu da Ubanmu har abada abadin. Amin. (aiōn )
Yanzu bari daukaka ta tabbata ga Allah da Ubanmu har abada abadin. Amin. (aiōn )
21 Ku gai da dukan tsarkaka cikin Kiristi Yesu.’Yan’uwan da suke tare da ni suna gaishe ku.
Gai da kowanne mai bi cikin Almasihu Yesu. Dukan 'yan'uwa da ke tare da ni suna gaisuwa.
22 Dukan tsarkaka suna gaishe ku, musamman waɗanda suke na gidan Kaisar.
Dukan masu bi a nan suna gaisuwa, musamman wadanda suke gidan Kaisar.
23 Alherin Ubangiji Yesu Kiristi yă kasance da ruhunku. Amin.
Bari alherin Ubangijin Yesu Almasihu ya zauna tare da ruhunku. Amin