< Filibbiyawa 3 >

1 A ƙarshe,’yan’uwana, ku yi farin ciki a cikin Ubangiji! Ba abin damuwa ba ne a gare ni in sāke rubuta muku irin waɗannan abubuwa, domin lafiyarku ne.
Dalej mówiąc, bracia moi! radujcie się w Panu. Jedneż rzeczy wam pisać mnie nie mierzi, a wam jest bezpiecznie.
2 Ku yi hankali da waɗancan karnuka, waɗancan mutane masu aikata mugunta, waɗancan masu yankan jiki.
Upatrujcie psy, upatrujcie złych robotników, upatrujcie rozerwanie.
3 Gama mu ne masu kaciya, mu da muke yi sujada ta wurin Ruhun Allah, mu da muke taƙama a cikin Kiristi Yesu, mu da ba mu dogara da ayyukan da ake gani ba,
Albowiem my jesteśmy obrzezaniem, którzy duchem służymy Bogu i chlubimy się w Chrystusie Jezusie, a w ciele nie ufamy.
4 ko da yake ni kaina ina da dalilan dogara da haka. In kuwa akwai wani wanda yake tsammani yana da dalilan dogara ga jiki, ni fa na fi shi,
Aczci i ja w ciele mam ufanie; jeźli kto inszy zda się mieć ufanie w ciele, bardziej ja,
5 an yi mini kaciya a rana ta takwas, asalina Isra’ila ne, na kabilar Benyamin, mutumin Ibraniyawa ɗan Ibraniyawa; bisa ga doka kuwa ni Bafarisiye ne;
Obrzezany będąc ósmego dnia, z narodu Izraelskiego, z pokolenia Benjaminowego, Żyd z Żydów, według zakonu Faryzeusz;
6 wajen himma kuwa, ni mai tsananta wa ikkilisiya ne, wajen aikin adalci bisa ga hanyar doka, ni marar laifi ne.
Według gorliwości prześladowca kościoła, według sprawiedliwości onej, która jest z zakonu, będąc bez przygany.
7 Amma abin da dā ya zama mini riba yanzu, na ɗauka hasara ce saboda Kiristi.
Ale to, co mi było zyskiem, tom poczytał dla Chrystusa za szkodę.
8 Me kuma ya fi, na ɗauki dukan abubuwa hasara ne in aka kwatanta da mafificiyar girman sanin Kiristi Yesu Ubangijina, wanda saboda shi ne na yi hasarar kome. Na mai da su kayan wofi, domin in sami Kiristi
Owszem i wszystko poczytam sobie za szkodę dla zacności znajomości Chrystusa Jezusa, Pana mojego, dla któregom wszystko utracił i mam to sobie za gnój, abym Chrystusa zyskał,
9 a kuma same ni a cikinsa, ba da wani adalcin kaina wanda yake zuwa daga bin doka ba, sai dai adalcin da yake samuwa ta wurin bangaskiya a cikin Kiristi, adalcin da yake fitowa daga Allah da kuma yake zuwa ta wurin bangaskiya.
I był znaleziony w nim, nie mając sprawiedliwości mojej, tej która jest z zakonu, ale tę, która jest przez wiarę Chrystusową, to jest sprawiedliwość z Boga, która jest przez wiarę;
10 Ina so in san Kiristi da ikon tashinsa daga matattu da kuma zumuncin tarayya cikin shan wahalarsa, in kuma zama kamar sa a cikin mutuwarsa,
Żebym go poznał i moc zmartwychwstania jego, i społeczność ucierpienia jego, przykształtowany będąc śmierci jego,
11 yadda kuma ko ta yaya, in kai ga tashin nan daga matattu.
Owabym jakimkolwiek sposobem doszedł do powstania z martwych.
12 Ba cewa na riga na sami dukan wannan ba ne, ko kuma an riga an mai da ni cikakke ba, sai dai ina nacewa don in kai ga samun abin da Kiristi Yesu ya riƙe ni saboda shi.
Nie iżbym już uchwycił, albo już doskonałym był; ale ścigam, ażbym też uchwycił to, na com też od Chrystusa Jezusa uchwycony.
13 ’Yan’uwa, ban ɗauki kaina a kan cewa na riga na sami abin ba. Sai dai abu guda nake yi. Ina mantawa da abin da yake baya, ina kuma nacewa zuwa ga samun abin da yake gaba,
Bracia! jać o sobie nie rozumiem, żebym już uchwycił.
14 ina nacewa gaba zuwa ga manufar, don in sami ladar da Allah ya yi mini na kiran nan zuwa sama a cikin Kiristi Yesu.
Ale jedno czynię, że tego, co za mną jest, zapamiętywając, a do tego się, co przede mną jest, spiesząc, bieżę do kresu ku zakładowi powołania onego Bożego, które jest z góry w Chrystusie Jezusie.
15 Dukanmu da muka balaga ya kamata mu yi wannan irin ganin abubuwa. In kuwa saboda wani dalili tunaninku ya yi dabam, Allah zai bayyana muku wannan ma.
Ile tedy nas doskonałych, toż rozumiejmy; a jeźli co inaczej rozumiecie, i toć wam Bóg objawi.
16 Sai dai a duk inda muka kai, mu ci gaba da haka.
Wszakże w tem, czegośmy doszli, według jednegoż sznuru postępujmy i jednoż rozumiejmy.
17 Ku haɗa kai da waɗansu cikin bin gurbina, ku kuma lura da waɗanda suke rayuwa bisa ga ƙa’idar da muka ba ku.
Bądźcież wespół naśladowcami moimi, bracia! a upatrujcie tych, którzy tak chodzą, jako nas za wzór macie.
18 Gama kamar yadda na sha gaya muku yanzu kuma ina sāke gaya muku har ma da hawaye, waɗansu da yawa suna rayuwa kamar abokan gāban gicciyen Kiristi.
Albowiem wiele ich chodzi, o którychem wam często powiadał, a teraz i z płaczem mówię, iż są nieprzyjaciołmi krzyża Chrystusowego;
19 Ƙaddararsu hallaka ce, allahnsu cikinsu ne, rashin kunyarsu shi ne abin fahariyarsu. Hankalinsu yana kan kayan duniya.
Których koniec jest zatracenie, których Bóg jest brzuch, a chwała w hańbie ich, którzy się o rzeczy ziemskie starają.
20 Amma mu’yan mulkin sama ne. Muna kuma jira zuwan Mai Ceto daga can, Ubangiji Yesu Kiristi,
Aleć nasza rzeczpospolita jest w niebiesiech, skąd też zbawiciela oczekujemy, Pana Jezusa Chrystusa.
21 shi ne mai ikon kawo dukan abubuwa ƙarƙashin mulkinsa. Ta wurin ikon nan nasa zai sāke jikin nan namu na ƙasƙanci, yă mai da shi kamar jikin nan nasa na ɗaukaka.
Który przemieni ciało nasze podłe, aby się podobne stało chwalebnemu ciału jego, według skutecznej mocy, którą też wszystkie rzeczy sobie podbić może.

< Filibbiyawa 3 >