< Filibbiyawa 2 >

1 In kuna da wata ƙarfafawa daga tarayya da Kiristi, in da wata ta’aziyya daga ƙaunarsa, in da wani zumunci da Ruhu, in da juyayi da tausayi,
If there is therefore any exhortation in Christ, if any consolation of love, if any fellowship of the Spirit, if any tender mercies and compassion,
2 to, sai ku sa farin cikina yă zama cikakke ta wurin kasance da hali ɗaya, kuna ƙauna ɗaya, kuna zama ɗaya cikin ruhu da kuma manufa.
make my joy full, by being like-minded, having the same love, being of one accord, of one mind;
3 Kada ku yi kome da sonkai ko girman kai, sai dai cikin tawali’u, ku ɗauki waɗansu sun fi ku.
doing nothing through rivalry or through conceit, but in humility, each counting others better than himself;
4 Bai kamata kowannenku yă kula da sha’anin kansa kawai ba, sai dai yă kula da sha’anin waɗansu ma.
each of you not just looking to his own things, but each of you also to the things of others.
5 A cikin dangantakarku da juna, ya kamata halayenku su zama kamar na Kiristi Yesu.
Have this in your attitude, which was also in Christ Jesus,
6 Wanda, ko da yake cikin ainihin surar Allah yake, bai mai da daidaitakansa nan da Allah wani abin riƙewa kam-kam ba,
who, existing in the form of God, did not consider equality with God a thing to be grasped,
7 amma ya mai da kansa ba kome ba, yana ɗaukan ainihin surar bawa, aka yi shi cikin siffar mutum.
but emptied himself, taking the form of a servant, being made in the likeness of men.
8 Aka kuma same shi a kamannin mutum, ya ƙasƙantar da kansa ya kuma zama mai biyayya wadda ta kai shi har mutuwa, mutuwar ma ta gicciye!
And being found in human form, he humbled himself, becoming obedient to death, yes, the death of the cross.
9 Saboda haka Allah ya ɗaukaka shi zuwa mafificin wuri ya kuma ba shi sunan da ya fi dukan sunaye,
Therefore God also highly exalted him, and gave to him the name which is above every name;
10 don a sunan Yesu kowace gwiwa za tă durƙusa, a sama da a ƙasa da kuma a ƙarƙashin ƙasa,
that at the name of Jesus every knee should bow, of those in heaven, those on earth, and those under the earth,
11 kowane harshe kuma yă furta cewa Yesu Kiristi Ubangiji ne, don ɗaukakar Allah Uba.
and that every tongue should confess that Jesus Christ is Lord, to the glory of God the Father.
12 Saboda haka, ya abokaina ƙaunatattu, kamar yadda kullum kuke biyayya ba kawai sa’ad da ina nan ba, amma yanzu da ba na nan tare da ku, ku ci gaba da yin ayyukan cetonku da tsoro da kuma rawan jiki,
So then, my beloved, even as you have always obeyed, not only in my presence, but now much more in my absence, work out your own salvation with awe and reverence.
13 gama Allah ne yake aiki a cikinku, don ku nufa ku kuma aikata bisa ga nufinsa mai kyau.
For it is God who works in you both to will and to work, for his good pleasure.
14 Ku yi kome ba tare da gunaguni ko gardama ba,
Do everything without complaining or arguing,
15 don ku zama marasa abin zargi, sahihai’ya’yan Allah, waɗanda ba su da laifi, a zamanin mutane karkatattu, kangararru, waɗanda kuke haskakawa a cikinsu kamar fitilu a duniya
that you may become blameless and pure, children of God without blemish in the midst of a crooked and perverse generation, among whom you are seen as lights in the world,
16 kuna kuwa cin gaba da riƙe maganar rai domin in yi taƙama a ranar Kiristi cewa ban yi gudu ko fama a banza ba.
holding up the word of life; that I may have something to boast in the day of Christ, that I did not run in vain nor labor in vain.
17 Amma ko da ana tsiyaye jinina kamar hadaya ta sha a kan hadaya da kuma hidimar da take fitowa daga bangaskiyarku, ina murna ina kuma farin ciki da ku duka.
Yes, and if I am poured out on the sacrifice and service of your faith, I rejoice, and rejoice with you all.
18 Haka ma ya kamata ku yi murna ku kuma yi farin ciki tare da ni.
In the same way, you also rejoice, and rejoice with me.
19 Ina sa rai a cikin Ubangiji Yesu cewa zan aika da Timoti zuwa gare ku ba da daɗewa ba, don ni ma in ji daɗi sa’ad da na ji labarinku.
But I hope in the Lord Jesus to send Timothy to you soon, that I also may be cheered up when I know how you are doing.
20 Ba ni da wani kamar sa, wanda yake da ainihin sha’awa a zaman lafiyarku.
For I have no one else like-minded, who will truly care about you.
21 Gama kowa yana lura da al’amuran kansa ne kawai, ba na Kiristi Yesu ba.
For they all seek their own, not the things of Jesus Christ.
22 Amma, ai, kun san darajar Timoti yadda muka yi bautar bishara tare, kamar ɗa da mahaifinsa.
But you know the proof of him, that, as a child serves a father, so he served with me in furtherance of the Good News.
23 Saboda haka, ina sa rai, in aike shi da zarar na ga yadda abubuwa suke a nan.
Therefore I hope to send him at once, as soon as I see how it will go with me.
24 Ni kuma ina da tabbaci a cikin Ubangiji cewa zan zo ba da daɗewa ba.
But I trust in the Lord that I myself also will come shortly.
25 Amma ina gani ya dace in aika da Afaforiditus, ɗan’uwana, abokin aikina da kuma abokin famana, wanda kuma yake ɗan saƙonku, wanda kuka aika domin yă biya mini bukatuna.
But I counted it necessary to send to you Epaphroditus, my brother, fellow worker, fellow soldier, and your apostle and servant of my need;
26 Gama yana marmarin ganinku duka ya kuma damu domin kun ji cewa ya yi rashin lafiya.
since he longed for you all, and was very troubled, because you had heard that he was sick.
27 Ba shakka ya yi rashin lafiya, har ya kusa mutuwa. Amma Allah ya nuna masa jinƙai, ba shi kaɗai ba amma har da ni ma, don yă rage mini baƙin ciki kan baƙin ciki.
For indeed he was sick, nearly to death, but God had mercy on him; and not on him only, but on me also, that I might not have sorrow on sorrow.
28 Saboda haka na yi niyya ƙwarai in aike shi wurinku, don sa’ad da kuka sāke ganinsa za ku yi murna, ni kuma in rage damuwa.
I have sent him all the more eagerly, therefore, so that when you see him again you may rejoice, and that I may be less anxious.
29 Ku marabce shi cikin Ubangiji da farin ciki mai yawa, ku kuma girmama mutane irinsa,
Receive him therefore in the Lord with all joy, and hold such in honor,
30 domin ya kusa yă mutu saboda aikin Kiristi, ya yi kasai da ransa don yă cikasa taimakon da ba ku iya yi mini ba.
because for the work of Christ he came near to death, risking his life to supply that which was lacking in your service toward me.

< Filibbiyawa 2 >