< Filemon 1 >
1 Bulus, ɗan kurkuku saboda Kiristi Yesu, da kuma Timoti ɗan’uwanmu, Zuwa ga Filemon ƙaunataccen abokinmu da kuma abokin aikinmu,
Paul, a prisoner of Christ Jesus, and Timothy the brother, to Philemon our beloved and co-workman,
2 zuwa kuma ga Affiya’yar’uwarmu, zuwa kuma ga Arkiffus abokin famarmu, da zuwa kuma ga ikkilisiyar da take taruwa a gidanka.
and to the beloved Apphia, and Archippus our fellow soldier, and to the congregation at thy house:
3 Alheri da salama daga Allah Ubanmu da kuma Ubangiji Yesu Kiristi, su kasance tare da ku.
Grace to you and peace from God our Father and the Lord Jesus Christ.
4 Kullum nakan gode wa Allahna sa’ad da nake tuna da kai cikin addu’o’ina,
I thank my God, making recollection of thee always in my prayers,
5 domin ina jin labari bangaskiyarka cikin Ubangiji Yesu da kuma ƙaunarka da kake yi saboda dukan tsarkaka.
hearing of thy love and faith, which thou have toward the Lord Jesus and for all the sanctified,
6 Ina addu’a ka zama mai ƙwazo cikin shaida bangaskiyarka, domin ka sami cikakken fahimta ta kowane abin da yake nagarin da muke da shi cikin Kiristi.
so that the fellowship of thy faith may become potent (in the knowledge of every good thing in us) for Christ Jesus.
7 Ƙaunarka ta sa ni farin ciki ƙwarai ta kuma ƙarfafa ni, domin kai, ɗan’uwa, ka wartsake zukatan tsarkaka.
For we have much joy and encouragement in thy love, because the bowels of the sanctified have been refreshed by thee, brother.
8 Saboda haka, ko da yake cikin Kiristi ina iya yin ƙarfin hali in umarce ka ka yi abin da ya kamata,
Therefore, though I have much boldness in Christ to command thee that which is befitting,
9 duk da haka ina roƙonka saboda ƙauna, na fi so in roƙe ka, ni Bulus tsoho, a yanzu kuma ga ni ɗan sarƙa saboda Kiristi Yesu.
because of love I rather beseech, being such as aged Paul, and now also a prisoner of Jesus Christ.
10 Ina roƙonka saboda ɗana Onesimus, wanda ya zama ɗana yayinda nake cikin sarƙoƙi.
I beseech thee for my child Onesimus, whom I begot in my bonds.
11 Dā kam, ba shi da amfani a gare ka, amma yanzu ya zama da amfani a gare ka da kuma gare ni.
A man formerly unprofitable to thee, but now is profitable to thee and to me, whom I sent back.
12 Ina aike shi yă koma gare ka, shi da yake zuciyata.
And thou should welcome him, that is, my bowels.
13 Na so in riƙe shi a wurina a madadinka domin yă taimake ni yayinda nake cikin sarƙoƙi saboda bishara.
Whom I wanted to keep back for myself, so that in thy behalf he might serve me in the bonds of the good news.
14 Sai dai ban so in yi kome ban da yardarka ba, domin kowane alherin da za ka yi, yă fito daga zuciyarka, ba na tilas ba.
But I wanted to do nothing without thy mind, so that thy goodness might not be as from obligation, but from volition.
15 Wataƙila abin da ya sa aka raba ka da shi na ɗan lokaci ƙanƙani shi ne don ka same shi da amfani (aiōnios )
For perhaps because of this he departed for an hour, so that thou might receive him back forever, (aiōnios )
16 ba kamar bawa kuma ba, sai dai fiye da bawa, a matsayin ƙaunataccen ɗan’uwa. Shi ƙaunatacce ne sosai a gare ni amma a gare ka ya ma fi zama ƙaunatacce, kamar mutum da kuma kamar ɗan’uwa a cikin Ubangiji.
no longer as a bondman, but above a bondman, a beloved brother, especially to me, but how much more to thee, both in flesh and in the Lord.
17 Saboda haka in ka ɗauke ni a kan ni abokin tarayya ne, sai ka marabce shi kamar yadda za ka marabce ni.
If then thou have me a partner, accept him as myself.
18 In ya yi maka wani laifi ko kuma yana riƙe maka wani bashi, sai ka mai da shi a kaina.
But if he has wronged thee, or owes anything, charge this to me.
19 Ni, Bulus, nake rubuta wannan da hannuna. Zan biya ka, kada ma a yi zancen ranka da kake riƙe mini bashi.
I Paul write with my hand, I will repay, so that I may not say to thee that thou owe me in return even thyself.
20 Ina fata, ɗan’uwa, zan sami amfani daga gare ka cikin Ubangiji; ka wartsake zuciyata cikin Kiristi.
Yes, brother, let me have a favor of thee in the Lord. Refresh my bowels in the Lord.
21 Da tabbacin biyayyarka, ina rubuta maka, da sanin za ka yi fiye da abin da na ce.
Being confident in thine obedience I wrote to thee, knowing that thou will do above what I say.
22 Abu guda ya rage, ka shirya mini masauƙi, domin ina bege za a mayar da ni gare ku albarkacin addu’o’inku.
But simultaneously also prepare a lodging for me, for I hope that by your prayers I will be granted to you.
23 Efafaras, abokin tarayyata a kurkuku cikin Kiristi Yesu, yana gaishe ka.
Epaphras, my fellow prisoner in Christ Jesus, salutes thee,
24 Haka kuma Markus, Aristarkus, Demas da kuma Luka, abokan aikina.
and Mark, Aristarchus, Demas, Luke, my co-workmen.
25 Alherin Ubangiji Yesu Kiristi yă kasance da ruhunku.
The grace of our Lord Jesus Christ is with your spirit. Truly.