< Ƙidaya 9 >

1 Ubangiji ya yi magana da Musa a Hamadar Sinai, a watan farko na shekara ta biyu bayan fitarsu daga ƙasar Masar. Ya ce,
וידבר יהוה אל משה במדבר סיני בשנה השנית לצאתם מארץ מצרים בחדש הראשון--לאמר
2 “Ka sa Isra’ilawa su yi Bikin Ƙetarewa a ƙayyadadden lokaci.
ויעשו בני ישראל את הפסח במועדו
3 A yi wannan bikin ƙayyadadden lokaci da yamma, a rana ta goma sha huɗu ga wannan wata, a yi shi bisa ga dokokinsa da ƙa’idodinsa.”
בארבעה עשר יום בחדש הזה בין הערבים תעשו אתו--במעדו ככל חקתיו וככל משפטיו תעשו אתו
4 Saboda haka sai Musa ya gaya wa Isra’ilawa su yi Bikin Ƙetarewa,
וידבר משה אל בני ישראל לעשת הפסח
5 suka kuwa yi haka a Hamadar Sinai da yamma, a rana ta sha huɗu ga watan farko. Isra’ilawa suka yi dukan abubuwa yadda Ubangiji ya umarci Musa.
ויעשו את הפסח בראשון בארבעה עשר יום לחדש בין הערבים--במדבר סיני ככל אשר צוה יהוה את משה--כן עשו בני ישראל
6 Amma waɗansunsu ba su iya yin Bikin Ƙetarewa a ranar ba gama sun ƙazantu ta wurin taɓa gawa. Saboda haka suka zo wurin Musa da Haruna a wannan rana
ויהי אנשים אשר היו טמאים לנפש אדם ולא יכלו לעשת הפסח ביום ההוא ויקרבו לפני משה ולפני אהרן--ביום ההוא
7 suka ce wa Musa, “Mun ƙazantu saboda mun taɓa gawa, don me aka hana mu mu ba da hadaya ga Ubangiji tare da sauran Isra’ilawa a ƙayyadadden lokaci?”
ויאמרו האנשים ההמה אליו אנחנו טמאים לנפש אדם למה נגרע לבלתי הקריב את קרבן יהוה במעדו בתוך בני ישראל
8 Musa ya amsa musu ya ce, “Ku dakata sai na sami umarni daga wurin Ubangiji game da ku.”
ויאמר אלהם משה עמדו ואשמעה מה יצוה יהוה לכם
9 Sai Ubangiji ya ce wa Musa,
וידבר יהוה אל משה לאמר
10 “Gaya wa Isra’ilawa cewa, ‘Sa’ad da waninku ko zuriyarku ya ƙazantu ta wurin taɓa gawa, ko kuwa ya yi tafiya mai nisa, duk da haka zai kiyaye Bikin Ƙetarewa ta Ubangiji.
דבר אל בני ישראל לאמר איש איש כי יהיה טמא לנפש או בדרך רחקה לכם או לדרתיכם ועשה פסח ליהוה
11 Za su yi bikin da yamma, a rana ta sha huɗu ga wata na biyu. Za su ci naman tunkiya, tare da burodi marar yisti, da ganyaye masu ɗaci.
בחדש השני בארבעה עשר יום בין הערבים--יעשו אתו על מצות ומררים יאכלהו
12 Kada su bar kome daga cikinsa yă kai safe, ko a karye ƙashinsa. Sa’ad da suke Bikin Ƙetarewa, dole su kiyaye dukan ƙa’idodinsa.
לא ישאירו ממנו עד בקר ועצם לא ישברו בו ככל חקת הפסח יעשו אתו
13 Amma in mutumin da yake da tsarki bai kuma yi tafiya ba, ya kuwa ƙi yă yi Bikin Ƙetarewar, dole a ware wannan mutum daga mutanensa, domin bai miƙa hadaya ga Ubangiji a ƙayyadadden lokaci ba. Wannan mutum zai ɗauki alhakin zunubinsa.
והאיש אשר הוא טהור ובדרך לא היה וחדל לעשות הפסח--ונכרתה הנפש ההוא מעמיה כי קרבן יהוה לא הקריב במעדו--חטאו ישא האיש ההוא
14 “‘Baƙon da yake zaune a cikinku wanda yake so yă yi Bikin Ƙetarewar Ubangiji, dole yă yi shi bisa ga dokokinsa da ƙa’idodinsa. Dole ku kasance da ƙa’ida ɗaya ga baƙo da kuma ɗan ƙasa.’”
וכי יגור אתכם גר ועשה פסח ליהוה--כחקת הפסח וכמשפטו כן יעשה חקה אחת יהיה לכם ולגר ולאזרח הארץ
15 A ranar da aka kafa Tenti na Alkawari, sai girgije ya rufe shi. Daga yamma har safe, girgijen da yake bisa tabanakul ya yi kama da wuta.
וביום הקים את המשכן כסה הענן את המשכן לאהל העדת ובערב יהיה על המשכן כמראה אש--עד בקר
16 Haka ya ci gaba da kasancewa; girgijen ya rufe shi, da dare kuma sai ya yi kamar wuta.
כן יהיה תמיד הענן יכסנו ומראה אש לילה
17 Duk sa’ad da aka ɗaga girgijen daga Tentin, sai Isra’ilawa su kama hanya; duk inda girgijen ya tsaya, a nan Isra’ilawa za su yi sansani.
ולפי העלות הענן מעל האהל--ואחרי כן יסעו בני ישראל ובמקום אשר ישכן שם הענן--שם יחנו בני ישראל
18 Da umarnin Ubangiji, Isra’ilawa suke tashi. Da umarninsa kuma suke sauka. Muddin girgijen yana tsaye a bisa tabanakul, sukan yi ta zamansu a sansanoni.
על פי יהוה יסעו בני ישראל ועל פי יהוה יחנו כל ימי אשר ישכן הענן על המשכן--יחנו
19 Sa’ad da girgijen ya ci gaba da kasancewa a bisan tabanakul na dogon lokaci, Isra’ilawa sukan bi umarnin Ubangiji, ba kuwa za su tashi ba.
ובהאריך הענן על המשכן ימים רבים--ושמרו בני ישראל את משמרת יהוה ולא יסעו
20 Wani lokaci girgijen yakan yi’yan kwanaki ne kawai a bisa tabanakul; da umarnin Ubangiji sukan kafa sansani da umarninsa kuma su tashi.
ויש אשר יהיה הענן ימים מספר--על המשכן על פי יהוה יחנו ועל פי יהוה יסעו
21 Wani lokaci girgijen yakan zauna daga yamma har safiya ne kawai, sa’ad da kuma aka ɗaga shi da safe, sai su kama hanya. Ko da rana, ko da dare, duk sa’ad da aka ɗaga girgijen, sai su ma su tashi.
ויש אשר יהיה הענן מערב עד בקר ונעלה הענן בבקר ונסעו או יומם ולילה ונעלה הענן ונסעו
22 Ko girgijen ya yi kwana biyu a bisa tabanakul, ko wata guda, ko shekara, Isra’ilawa za su zauna a sansani ba kuwa za su tashi ba; amma sa’ad da aka ɗaga shi, sai su kuma su tashi.
או ימים או חדש או ימים בהאריך הענן על המשכן לשכן עליו יחנו בני ישראל ולא יסעו ובהעלתו יסעו
23 Da umarnin Ubangiji sukan kafa sansani, da umarninsa kuma sukan tashi. Sukan bi umarnin Ubangiji, bisa ga umarninsa ta wurin Musa.
על פי יהוה יחנו ועל פי יהוה יסעו את משמרת יהוה שמרו על פי יהוה ביד משה

< Ƙidaya 9 >