< Ƙidaya 8 >

1 Ubangiji ya ce wa Musa,
וידבר יהוה אל משה לאמר
2 “Yi magana da Haruna, ka ce masa, ‘Sa’ad da za ka shisshirya fitilun nan bakwai, ka shirya su yadda za su fuskanci gaba domin haskensu yă haskaka ta gaba.’”
דבר אל אהרן ואמרת אליו בהעלתך את הנרת אל מול פני המנורה יאירו שבעת הנרות
3 Haka kuwa Haruna ya yi; ya shisshirya fitilun yadda za su fuskanci gaba a kan wurin ajiye fitilan, kamar dai yadda Ubangiji ya umarci Musa.
ויעש כן אהרן--אל מול פני המנורה העלה נרתיה כאשר צוה יהוה את משה
4 Ga yadda aka yi wurin ajiye fitilan. An ƙera shi da zinariya daga gindinsa har zuwa sama inda ya buɗu. Aka ƙera wurin ajiye fitilan yadda Ubangiji ya nuna wa Musa.
וזה מעשה המנרה מקשה זהב עד ירכה עד פרחה מקשה הוא כמראה אשר הראה יהוה את משה--כן עשה את המנרה
5 Ubangiji ya ce wa Musa,
וידבר יהוה אל משה לאמר
6 “Keɓe Lawiyawa daga sauran Isra’ilawa, ka tsarkake su.
קח את הלוים מתוך בני ישראל וטהרת אתם
7 Ga yadda za ka tsarkake su, ka yayyafa musu ruwan tsarkakewa; ka sa su aske jikunansu duka su kuma wanke tufafinsu, ta haka za su tsarkake kansu.
וכה תעשה להם לטהרם הזה עליהם מי חטאת והעבירו תער על כל בשרם וכבסו בגדיהם והטהרו
8 Ka sa su ɗauki ɗan bijimi tare da lallausan garin hadaya, kwaɓaɓɓe da mai; sa’an nan, kai kuma ka ɗauki ɗan bijimi na biyu na hadaya don zunubi.
ולקחו פר בן בקר ומנחתו סלת בלולה בשמן ופר שני בן בקר תקח לחטאת
9 Ka kawo Lawiyawa a gaban Tentin Sujada, ka kuma kira taron Isra’ilawa duka.
והקרבת את הלוים לפני אהל מועד והקהלת--את כל עדת בני ישראל
10 Za ka kawo Lawiyawa a gaban Ubangiji, Isra’ilawa kuma za su ɗibiya musu hannuwansu.
והקרבת את הלוים לפני יהוה וסמכו בני ישראל את ידיהם על הלוים
11 Haruna zai miƙa Lawiyawa a gaban Ubangiji a matsayin hadaya ta kaɗawa daga Isra’ilawa, saboda a shirya su domin aikin Ubangiji.
והניף אהרן את הלוים תנופה לפני יהוה מאת בני ישראל והיו לעבד את עבדת יהוה
12 “Bayan Lawiyawa sun ɗibiya hannuwansu a kan bijiman, sai ka yi amfani da ɗaya a matsayin hadaya don zunubi ga Ubangiji, ɗayan kuma domin hadaya ta ƙonawa, don yin kafara saboda Lawiyawa.
והלוים יסמכו את ידיהם על ראש הפרים ועשה את האחד חטאת ואת האחד עלה ליהוה לכפר על הלוים
13 Ka kuma sa Lawiyawa su tsaya a gaban Haruna da’ya’yansa, sai ka miƙa su kamar hadaya ta kaɗawa ga Ubangiji.
והעמדת את הלוים לפני אהרן ולפני בניו והנפת אתם תנופה ליהוה
14 Da haka za ka keɓe Lawiyawa daga sauran Isra’ilawa, Lawiyawa za su zama nawa.
והבדלת את הלוים מתוך בני ישראל והיו לי הלוים
15 “Bayan ka tsarkake Lawiyawa, ka kuma miƙa su kamar hadaya ta kaɗawa, sai su zo su yi aikinsu a Tentin Sujada.
ואחרי כן יבאו הלוים לעבד את אהל מועד וטהרת אתם והנפת אתם תנופה
16 Gama dukansu an ba ni su daga cikin Isra’ilawa a maimakon dukan waɗanda suka fara buɗe mahaifa, wato, dukan’ya’yan farin Isra’ilawa. Na karɓi Lawiyawa su zama nawa.
כי נתנים נתנים המה לי מתוך בני ישראל תחת פטרת כל רחם בכור כל מבני ישראל--לקחתי אתם לי
17 Kowane ɗan farin haihuwa, ko mutum, ko dabba a Isra’ila, nawa ne. Sa’ad da na kashe’ya’yan fari a Masar, na keɓe’ya’yan fari na Isra’ilawa wa kaina.
כי לי כל בכור בבני ישראל באדם ובבהמה ביום הכתי כל בכור בארץ מצרים הקדשתי אתם לי
18 Na kuma ɗauki Lawiyawa a maimakon dukan’ya’yan fari maza a Isra’ila.
ואקח את הלוים תחת כל בכור בבני ישראל
19 Cikin dukan Isra’ilawa, na ba da Lawiyawa kyauta ga Haruna da’ya’yansa, su yi hidima a Tentin Sujada a madadin Isra’ilawa, su kuma yi kafara dominsu saboda kada annoba ta bugi Isra’ilawa sa’ad da suka je kusa da wuri mai tsarki.”
ואתנה את הלוים נתנים לאהרן ולבניו מתוך בני ישראל לעבד את עבדת בני ישראל באהל מועד ולכפר על בני ישראל ולא יהיה בבני ישראל נגף בגשת בני ישראל אל הקדש
20 Musa, Haruna da kuma dukan taron Isra’ilawa, suka yi da Lawiyawa yadda Ubangiji ya umarci Musa.
ויעש משה ואהרן וכל עדת בני ישראל ללוים ככל אשר צוה יהוה את משה ללוים--כן עשו להם בני ישראל
21 Lawiyawa suka tsarkake kansu, suka kuma wanke tufafinsu. Sai Haruna ya miƙa su kamar hadaya ta kaɗawa a gaban Ubangiji, ya kuma yi kafara saboda su don yă tsarkake su.
ויתחטאו הלוים ויכבסו בגדיהם וינף אהרן אתם תנופה לפני יהוה ויכפר עליהם אהרן לטהרם
22 Bayan haka, sai Lawiyawa suka zo don su yi aikinsu a Tentin Sujada, a ƙarƙashin Haruna da’ya’yansa. Suka yi da Lawiyawa kamar dai yadda Ubangiji ya umarci Musa.
ואחרי כן באו הלוים לעבד את עבדתם באהל מועד לפני אהרן ולפני בניו כאשר צוה יהוה את משה על הלוים כן עשו להם
23 Ubangiji ya ce wa Musa,
וידבר יהוה אל משה לאמר
24 “Wannan ya shafi Lawiyawa ne, wato, mazan da suka kai shekara ashirin da biyar, ko fiye, za su zo su yi aiki a Tentin Sujada,
זאת אשר ללוים מבן חמש ועשרים שנה ומעלה יבוא לצבא צבא בעבדת אהל מועד
25 amma in suka kai shekaru hamsin da haihuwa, dole su huta daga wannan aiki na yau da kullum, su kuma daina aiki.
ומבן חמשים שנה ישוב מצבא העבדה ולא יעבד עוד
26 Za su iya taimakon’yan’uwansu cikin tafiyar da ayyuka a Tentin Sujada, amma su kansu ba za su yi aikin ba. Haka fa za ka ba wa Lawiyawa aikinsu.”
ושרת את אחיו באהל מועד לשמר משמרת ועבדה לא יעבד ככה תעשה ללוים במשמרתם

< Ƙidaya 8 >