< Ƙidaya 34 >
1 Ubangiji ya ce wa Musa,
Then the LORD said to Moses,
2 “Ka umarci Isra’ilawa, ka ce musu, ‘Sa’ad da kuka shiga Kan’ana, ƙasar da aka ba ku gādo za tă kasance da waɗannan iyakoki.
“Command the Israelites and say to them: When you enter the land of Canaan, it will be allotted to you as an inheritance with these boundaries:
3 “‘Gefenku na kudu zai haɗa da wani sashin Hamadan Zin ta iyakar Edom. A gabas, iyakarku ta kudu za tă fara daga ƙarshen Tekun Gishiri,
Your southern border will extend from the Wilderness of Zin along the border of Edom. On the east, your southern border will run from the end of the Salt Sea,
4 tă ƙetare Mashigin Kunama a kudu, tă ci gaba zuwa Zin, sa’an nan tă nufi kudu da Kadesh Barneya. Sa’an nan za tă zarce zuwa Hazar Addar, tă nausa zuwa Azmon,
cross south of the Ascent of Akrabbim, continue to Zin, and go south of Kadesh-barnea. Then it will go on to Hazar-addar and proceed to Azmon,
5 inda za tă juya tă haɗu da Rafin Masar, tă kuma ƙarasa a Bahar Rum.
where it will turn from Azmon, join the Brook of Egypt, and end at the Sea.
6 “‘Iyakarku a yammanci, za tă kasance bakin Bahar Rum. Wannan ce za tă zama iyakarku a yamma.
Your western border will be the coastline of the Great Sea; this will be your boundary on the west.
7 “‘Iyakarku a arewanci kuwa za tă tashi daga Bahar Rum zuwa Dutsen Hor,
Your northern border will run from the Great Sea directly to Mount Hor,
8 za tă kuma tashi daga Dutsen Hor, zuwa Lebo Hamat. Sa’an nan tă miƙe zuwa Zedad,
and from Mount Hor to Lebo-hamath, then extend to Zedad,
9 tă ci gaba zuwa Zifron, sa’an nan tă ƙarasa a Hazar-Enan. Wannan ce za tă zama iyakarku a arewa.
continue to Ziphron, and end at Hazar-enan. This will be your boundary on the north.
10 “‘Iyakarku a gabashi, za tă tashi daga Hazar-Enan zuwa Shefam.
And your eastern border will run straight from Hazar-enan to Shepham,
11 Iyakar za tă gangara daga Shefam zuwa Ribla a gefen gabashin Ayin, sa’an nan tă ci gaba a gangaren gabashin Tekun Kinneret.
then go down from Shepham to Riblah on the east side of Ain and continue along the slopes east of the Sea of Chinnereth.
12 Sa’an nan tă gangara ta Urdun, tă ƙarasa a Tekun Gishiri. “‘Wannan za tă zama ƙasarku, tare da iyakokinta a kowane gefe.’”
Then the border will go down along the Jordan and end at the Salt Sea. This will be your land, defined by its borders on all sides.”
13 Sai Musa ya umarci Isra’ilawa ya ce, “Ku raba wannan ƙasa da za ku gāda ta hanyar jefa ƙuri’a. Ubangiji ya umarta cewa a ba da ita ga kabilu tara da rabi,
So Moses commanded the Israelites, “Apportion this land by lot as an inheritance. The LORD has commanded that it be given to the nine and a half tribes.
14 saboda iyalan kabilar Ruben, kabilar Gad da rabin kabilar Manasse sun riga sun sami gādonsu.
For the tribes of the Reubenites and Gadites, along with the half-tribe of Manasseh, have already received their inheritance.
15 Waɗannan kabilu biyu da rabi, sun sami gādonsu a wancan hayin Urdun a gabashin Yeriko wajen fitowar rana.”
These two and a half tribes have received their inheritance across the Jordan from Jericho, toward the sunrise.”
16 Ubangiji ya ce wa Musa,
Then the LORD said to Moses,
17 “Waɗannan su ne sunayen mutanen da za su raba muku ƙasar gādo. Eleyazar firist, da Yoshuwa ɗan Nun.
“These are the names of the men who are to assign the land as an inheritance for you: Eleazar the priest and Joshua son of Nun.
18 Ka kuma naɗa shugaba guda ɗaya daga kowace kabila domin yă taimaka a rabon ƙasar.
Appoint one leader from each tribe to distribute the land.
19 “Ga sunayensu. “Kaleb ɗan Yefunne, daga kabilar Yahuda;
These are their names: Caleb son of Jephunneh from the tribe of Judah;
20 Shemuyel ɗan Ammihud, daga kabilar Simeyon
Shemuel son of Ammihud from the tribe of Simeon;
21 Elidad ɗan Kislon, daga kabilar Benyamin;
Elidad son of Chislon from the tribe of Benjamin;
22 Bukki ɗan Yogli, shugaba daga kabilar Dan;
Bukki son of Jogli, a leader from the tribe of Dan;
23 Hanniyel ɗan Efod, shugaba daga kabilar Manasse ɗan Yusuf;
Hanniel son of Ephod, a leader from the tribe of Manasseh son of Joseph;
24 Kemuwel ɗan Shiftan, shugaba daga kabilar Efraim ɗan Yusuf;
Kemuel son of Shiphtan, a leader from the tribe of Ephraim;
25 Elizafan ɗan Farnak, shugaba daga kabilar Zebulun;
Eli-zaphan son of Parnach, a leader from the tribe of Zebulun;
26 Faltiyel ɗan Azzan, shugaba daga kabilar Issakar;
Paltiel son of Azzan, a leader from the tribe of Issachar;
27 Ahihud ɗan Shelomi, shugaba daga kabilar Asher;
Ahihud son of Shelomi, a leader from the tribe of Asher;
28 Fedahel ɗan Ammihud, shugaba daga kabilar Naftali.”
and Pedahel son of Ammihud, a leader from the tribe of Naphtali.”
29 Waɗannan su ne mutanen da Ubangiji ya umarta su raba gādo ga Isra’ilawa a ƙasar Kan’ana.
These are the ones whom the LORD commanded to apportion the inheritance to the Israelites in the land of Canaan.